← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 89

Sashe 77

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'u ta faÉ—a lokaci É—aya ni da ita muna kallon juna. Kafin kuma kowa ya kauda kanshi gefe amma ni na gani sai da ta yi wannan shegen mirmishin na ta, a raina na ce wannan mirmishin yau na faÉ—uwa ba na nasararki ba ce Ma'u.

Da haka taron ya tashi Ma'u ba ta yi gigin zama ba saboda ba ta ga fuska ta bi mijinta zuwa gida nima Yallaɓai na bi muka koma gida. Ya Murja ce ta kusa sakani dariya da ta na ce ma Ya Aina ta yarda da Ma'u ta ci amanarta da ka gaya mata mgana ta je ta kai shi gaba, sai dai ta ga haka ya faru ne ta ke faɗin Ma'u ta na da daman halin an ce ka ce musamman daman a kaina ta yi ta cewa na yi mata kaza na yi mata kaza. Ban yi magana ba amma dai na yi dariya, saboda da ko da  na yi mgana sai a ce ni ce mai fitina yanzu ai sun ga gaskiya Baaba dai duk baki ya mutu. Kuma ita ta so haka ta san gaskiya amma sai idanuwanta suka rufe daga  ƙarshe sai ta ji kunya gaban surukai.

Ranar a gida muka yini ni da Yallaɓai bai fita ba. Muna tare ya na ɗan jana da hira har na saki jikina kaɗan. Tun daga ranar ban ƙara komawa ɗorayi ba, ballantana Gwammaja da na ji ma gidan ya fita daga kaina kwata kwata. Nene dai bayan lokaci ina kiran ta mu gaisa. Anty Bahijja kuma ban ƙara ganin ta ba, Gimbiyar ma haka tana can gidan Nene tun da an sake ba ta bedrest na sati biyar kuma ba a son zirga zirga. Harkan gabana kawai na ke yi tun da suka sha ni na warke shi kenan na koma tsoron duniya an fi sati biyu ban dawo dai-dai ba, har Tariq sai da ya kirani a waya ya na ba ni haƙuri haka ma Farida. Kawu Abba ko har gida ya dawo ya yi ta ba ni haƙuri na ce komai ya wuce. Mganar Marwa ko ya ce ba fashi manya ma suna shirin shiga cikin maganar tun da ba ya so shekara ta ƙare ba a yi auren ba.

Maganar gaskiya na fi wata ban iya mantawa da abin da ya faru ba. Ni gabaɗaya ma kowa sai ya koma ba ni tsoro. Ba dangin nawa ba na Yallaɓai ba har Amina sai daga baya ta ji labari ta yi ta ashar ta na zage zage. Sai ga Ma'u ta na min mgana a chart na ban hakuri na yi block ɗinta har ta test massages ta ke turomin, amma na share ta. Ai an gama har abada ba zan ƙara yarda da ita ba. Nesa nesa kallon kura a tsakanina da ita shi ne zaman lafiyata

Yallaɓai kuwa shi a ƙoƙarinsa na manta komai na sake rumgumar Yayarsa da Matarsa kamar baya. Ni ko na faɗa masa har abada. Za dai kawai a yi sha'ani, ni matar tashi ma ta fi ba ni mamaki yadda na sakankance da ita ta cutar da ni, itama ta turomin test mai tsawo na ban haƙuri ko karantawa ban yi ba na goge saboda ni gabaɗaya sun fita daga zuciyata ba na jin ko nan da shekara ɗaya ne zan iya sake sakin jiki da su. Ina ganin har abada ni da su.

*Janafty*
*TKG02020AA*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX

*BAYAN WATANNI UKU*

Watanni uku sun zo sun shuɗe kamar ƙiftawan ido. A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah da haka muke ta cinye kwanakin mu ba tare da mun farga ba.  A cikin watanni ukun da suka gabata, ba ƙoƙarin da ban yi domin na manta da abin da ya faru tsakanina da Gimbiya da su Anty Bahijja ba amma na kasa.  Duk lokacin da na tuna sai na ji gabaɗaya rayuwata ta yi ƙunci. Sai na ji zuciyata ta chunƙushe ga shi dai har a zuciyata na yafe musu amma kuma na kasa mantawa da abin da suka yi min. Barin ma in na ga ɗaya daga cikin su sai abin ya zo min shar a cikin raina.

Bayan faruwan lamarin na daɗe ba na zuwa ko'ina ina gidana. Har sai da Nene ta kirani a waya ta na faɗin saboda Anty Bahijja itama na yi mata ya ji, dalilin haka ne ya sa na je Gwamnaja na gaishe da Nene Allah kuma ya taimake ni Gimbiya ba ta nan ta je ganin likita har kuma na baro gidan ba su dawo ba, Nene sai da ta ba ni tausayi yadda ta riƙa bani haƙuri kamar ita ta yi min laifi. Saboda ita na ji a raina wataƙila in muka haɗu da Anty Bahijja na iya gaisheta. Amma ba saboda darajan ta ba sai domin ta ci darajan Nene da Yallabai su ne kawai za su saka in muka haɗu na iya buɗe baki na gaisheta. Amma a cikin idanuwana ba na kallon ta da ƙima da girman da can baya na saba ganinta dashi.

  Ilai ko mun haɗu da ita a gidan Nasara lokacin da ta haihu ranar suna. Sai ga ni ga Anty Bahijja da Anty Maimuna. Daƙyar na iya daurema zuciyata na gaishe su. Suka amsa suma cikin irin yanayin da na gaishe su. Kuma har na bar gidan sunan nan bamu ƙara mgana ba, ni ina tare da su Hauwa su kuma suna ciki tare da su Suwaiba. Gimbiya ba ta zo ba, ta na can Gwammaja ba ta fita tun da ta na ƙarƙashin dokan likita ne a bakin mijinta na ke jin kwanakin cikinta ya ɗan dawo baya, saboda raunin da ya samu amma ya tarkato ta ya kawo min ita har sau biyu gida na da sunan ta ƙara ba ni haƙuri amma bayan gaisuwa ban sake yarda wata mgana ta haɗamu ba sai ma na bar mata falon ita da yara da mijin gabaɗaya.

A zuwan ta na farko bai yi magana ba sai da suka ƙara dawowa shi ɗin ma daddare ne ya ɗaukota ya sake kawo min ita da cewarsa ta ƙara sake ba ni haƙuri
"Yallaɓai ka daina sa ta wahala ni fa na riga na ce na yafe tun a wancan lokacin"
Haka na faÉ—a masa amma sai ya dake da cewa in na ce na yafe me ya sa ba zan saki jiki da ita mu dawo kamar da ba.

"Yallaɓai da kamar wuya mu dawo kamar baya. Kawai ka bar ni tun da na ce komai ya wuce a bar shi a komai ya wucen mana."

Ya ƙara nacewa da cewa wai ai shima ya na yi min laifi nima ina yi masa mu yi faɗa sosai daga baya kuma mu manta komai mu zo mu shirya me ya sa yanzu ba zan manta ba.

"Kai Mijina ne. Kuma Ubangiji ne kaɗai ya san falalan da ke cikin aure. Wataƙila laifukan junanmu Allah ne ke umartan mala'iku suna shafe su daga cikin zukatan mu saboda martaba da daraja irin ta aure. Ita kuma matarka ce ita ɗin ba dole na ba ce, gaba ne ba zan yi da ita ba in muka haɗu za mu gaisa amma ka yi haƙuri ba zan ƙara sakin jikin da na yi a baya ba. Hausawa suka ce ruwa cikin cokali ya isa mai hankali wanka."

Amsar da na bashi kenan a lokacin na samu ya shafa min lafiya da kawo matarsa tare da min magiya na saki jiki a koma kamar baya sai ka ce ba ni da tunani ko ban san ciwon kaina ba. Ma'u ma mun haɗe sau biyu da ita bayan abin da ya faru, na farko mun haɗu a Ɗorayi da Baaba Aminu ya zo Gwaggo ta kikkiramu ta ce mu zo mu gaishe shi. Ban fara yi mata magana ba ita ce ta gaishe ni na amsa kuma bayan nan har na koma gida magana ba ta ƙara haɗamu ba, amma su Ya Aina kam har sun manta sun sake sakin mata ni dai kan an gama sha ni kuma na warke. In aka yi maka laifi ka nuna an yi maka haka ma Annabi(SWA) Ya ce. In kuma a ka ba ka haƙuri to ka haƙura amma kar ka manta domin rashin mantawar shi ne zai ba ma mutum daman kar ya ƙara sakankacewa a sake cutar da shi.

  Sai haɗuwa ta biyu a gidan Ya Balki da Firdausin ta ta yi sauka Qur'ani muka je walima a gidan ma ita ta fara min mgana muka gaisa shima kuma har muka rabu ba wanda ya ƙara tanka ɗan'uwansa ni fa da gaske na ke yi da na ce na yanke alaqa da ita. Kuma na ji daɗin yadda har Alhajinmu wannan karon bai tsamamin bq. Amma a raina na ce itama ba zan yi gaba da ita ba amma zumunci kamar ba ya ne dole ya ja baya a tsakaninmu. Dalilin haka ne ya sa har munafukan ƙawarta shema na daina ganin ta na ma na zarya a gida in wani abu ya faru. Ido ai da kunya ita kanta Ma'u ba ta san kunya ba ne shi ya sa ta iya gagicewa ta na shiga cikin jama'a bayan duk tsiyar da ta tafka.
Chapter 77 · 0% Book details