← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 89

Sashe 67

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka na faɗa ina haki, sai na juya baya ina ganin Yallaɓai ya koma mota ya yi riverse kenan ni zai biyo ni kuma ina azalzal ma mai adaidata da cewa ya yi sauri kawai hango kaina na ke yi a gaban Ma'u yadda zan makure ta sai ta kusa mutuwa ji na ke yi kamar zan iya yin bindiga ni kaɗai tsabar halin da na ke ciki na bakin ciki da ɓacin rai, kafin na fara kai su ƙara sai na ci uban Ma'u saboda in hukuma ta shiga ciki da farko ba zan samu damar cin uban ta dakyau ba gwara na fara nuna mata ina nan a Sadiyar da ta sani ban sauya ba kuma wallahi ni da zumunci da Ma'u har abada. Bahijja da sauran masu ta ya ta a kaina Yallaɓai zai shiga tsakanina da su, da ita kanta matarsa munafuka mai maida alheri da alheri sai an tuhuman min ita a gidan uban wa ta ga Inna Mariya ta kawo min asiri? Wallahi ko sama da ƙasa ne za ta haɗe ba zan bar maganar nan ba. Wato maganin nan da Inna Mariya ta kawo min ranar shi ne ta ke magana akai kenan lalle kar ka raina mutum duk wannan abubuwan da suka faru Ma'u ce sila ita ta ba ma Anty Bahijja daman cin zarafina. Shin wai da aka je asibiti an ce ne magani Gimbiyar ta sha? Ba ɗaya fa kawai ta tsane ne shi ya sa ta ke neman hanyar ci min mutumci, ban da haka ai ta san Gimbiyar na ta matsalan raunin mahaifa ko acan Abuja ma ta yi ɓari kuma ni da bakin Anty Bahijja na ji lokacin rasuwar mijin Gimbiyar ta na faɗin ai an nema mata maganin gargajiya na matsalan ciwon maran da ta ke fama da shi ke sa ta yi ɓari in ta samu ciki, amma yanzu sun manta Ma'u ta zo ta ɓata ni su kuma daman kamar su na jira sun far min da cin mutumci to komai ya zo ƙarshe daga wannan ba za a ƙara ba.

Muna tafe duk irin gudun da mai adaidaitan nan ya ke yi ni ba na gani, ji na ke yi kamar na karɓi tuƙin ƙila na isa in da na ke so a kan lokaci domin ji na ke yi kamar na yi tsuntsuwa na ganni a gaban Ma'u. Sai faman kiran wayata da ke cikin jaka ake yi amma ban bi ta kai ba, alokacin ni kaina ban san a yanayin da na ke ciki ba amma zan iya cewa tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin irin ɓacin ran da na ke ji a yanzu ba. Ban taɓa jin nauyin ƙirji da na zuciya irin na wannan ranar ba, ban taɓa tsintar kaina a yayin fusata da fushi mai tsanani irin na yau ba. Abu ɗaya ke ƙara tafasa min zuciya in na tuna yau duk cin mutumcin da Anty Bahijja ta yi min ba kowa ya ba ta dama ba sai Ma'u. Ma'u fa ƴar'uwata ce da za ta iya tsaya min da jikinta da aljihunta in ta ga wani zai cutar da ni wani ko zai ci zarafina, amma sai gashi yau ita da kanta ta ba da damar da aka taru aka ci zarafina a ka zagi dangin mahaifiyata da ta ke ƙasa ba ta san ma abin da ke faruwa ba.

Ban san ina hawaye ba sai da na ji ɗigan su a saman hannuwana. Ban san ina kuka ba sai da na ji zuciyata na wani irin zafi, zafin kuma sosai kamar sheɗata za ta ɗauke min sai da na fara numfashi sama sama saboda halin da na ke ciki. Ina tuna labarin da ta je ta ba ma Anty Bahijja wani tsohon labari ne da mu muna yara ƙanana ma aka yi, da girman mu labari muka ji daga baya. Yayar Mama Inna Mandiya Allah ya jiƙanta mijinta ya auro wata bafullatana an yi auren ba daɗewa ta fara rashin lafiya aka yi ta yawon mgani anan ne aka ce wai asiri aka yi mata. Daga nan magana ta shiga gari aka yi ta cewa Inna Mandiya ce ta yi mata asiri ta kwanta jinya. Ƙwatsam kuma sai ta rasu bayan kuma mutuwarta ba daɗewa itama Inna Mandiya ta fara rashin lafiya na aljanu a yadda Mama ta faɗa ma na ana tunanin Gamo ta yi shi ne da wannan rashin lafiyan ta koma ga Allah. Magana ta za ga gari cewa ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙewa sama da shekaru amma mutane ba su bar maganar ba, an daɗe ana kiran gidan su Mama da gidan yan asiri, daga baya da mutane suka ga ji suka daina ni kaina na manta da labarin abin da ya faru sama da shekaru ashirin amma da ya ke ita Ma'u munafuka ce ta na tune da labarin shi ne ta zaunar da Anty Bahijja ta faɗa mata domin ni ta tozarta ni.

Ban san ma na buÉ—e muryata ina kuka ba sai da mai Adaidaitan da na ke ciki ya juyo ya na faÉ—in" Hajiya lafiya?
Na kalle shi amma na ƙasa mgana sai danne laɓena na ƙasa na ke yi kar na fashe da kuka tsabar yadda na ke ji na a rikice kamar na fita daga hayyacina. Wannan abin da aka yi min shi ne abu mafi munin da ya taɓa ɓata min rai tun aurena da Yusuf duk da an yi wasu a baya amma bai kai wanda ni za a tozarta ni sannan a yi min mummunan ƙazafi ba.

"Ko rasuwa aka yi miki Hajiya? Sai haƙuri Allah ya jiƙan musulmi."

Shi ya yi kiɗan shi ya yi rawan shi amma ni kallo bai ishe ni ba, ni kaɗai na san yanayin da na ke ciki. Ma'u daman suna farko farkon Rijiyar zaki ne gidanta na bakin titi da kin shiga layi kaɗan haka, gani na yi ma in na tsaya sai ya shiga dani zan ɓata lokaci ya sa na sauka a bakin titi na buɗe jakata na ɗauko masa 1k na bashi ya na mgana ban ji sa ba domin tuni na yi gaba. Hango kaina kawai na ke yi a gaban Ma'u na maƙureta ina dukanta ko zan ji kaɗan daga abin da ke taso min a ƙasan zuciyata ya ragu. Gudu gudu sauri sauri ina tafe a hanya na ga wani ƙaton dutse na ɗauka na riƙe a hannuna ina zuwa bakin get ɗin ban jira komai na saka dutsen nan na riƙa buga kofar da shi ina jin megadin gidan na tambayan waye na yi banza da shi, ya na buɗe get ɗin ta ƙaramar ƙofa bakin sa ya buɗe da shirin mgana na tura shi baya da ƙarfi na shigo gidan.

Da idanuwana na ke kallon haraban gidan Allah ya ba ni sa'a na hango Ma'u tsaye a jikin mota da shirinta tsab na fita ta dukar da kai ta na duba wayarta. Ban jira komai ba da sassarfa na fara takawa zuwa gare ta megadi ya biyo ni ya na faÉ—in" Baiwar Allah lafiya?
Bai sanni ba domin rabo na da gidan Ma'u tun haihuwan Alhaji ƙarami..

Hayaniyar Megadi ya sa hankalin Ma'u ya dawo kan mu yadda ta ke kallona na san ta yi mamakin ganina ne. Na dumfare ta da sauri dai dai ina fuskarta ƙofar shiga falonta. A kuma lokacin mijinta Alhaji Mustapha ya fito ya na saɓa babban riga da alama tare za su fita da Ma'u. Kafin ya ƙariso ni na riga shi ƙarisawa gaban Ma'u na saki jakar hannuna da mayafina lokacin da bakin ta ke motsi na ji ta ambaci sunana.

"Sadiy.."

Ban bari ta ƙarisa ba, saboda lokacin da na ganta ga ta a gabana sai na ji ɓacin ran da na yi kafin na zo gidanta ya ninka sama da sau saba'in ba tare da jira ba kawai na ɗaga hannuna da karfi na kwashe ta da wani mahaukacin mari ta bangaren damanta wanda sai da ta gicjiya gefe cikin razana da firgici. Adai dai lokacin da mijinta ya ƙariso ya na faɗin.

"Sadiya ke ce ta fe? Ah Subhanallah."

Sai maganarsa ta ƙare da kiran sunan Allah ganin na yi sauke ma matarsa marin diɓan mahaukaciya. Ganin ya na ƙokarin karisowa ya sa ta na ɗagowa cikin mamaki dafe da kunci na ƙara dagewa na sauke mata wani marin a bangaren dama da sai da wayar hannunta ta suɓuce a ƙasa ta ba da sautin ƙara kafin kuma ta yi wani motsi na saka hannuwana duka biyu na ɗago kafaɗunta na yo gaba da ita sai kuma da karfi na mai da ta baya gam! Na buga kanta da jikin motan da ta ke tsaye a gefenta, na ƙara ɗagota na ƙara maida ta gam sannan na saka duka hannuwana na shaƙe mata wuya kamar zan kasheta idanuwanta sun firfito waje ta na rike hannuwana domin ceton ranta amma a lokacin ni ba na ji ba na gani burina kawai na yi ma Ma'u dukan mutuwan da gaba ko sunana aka ambata sai ta razana.

Alhaji Mustapha ya yo kaina cikin tashin hankali.
"Ke ke Sadiya me ye haka?
Ya ke faɗa ya na neman ɓambare hannayena daga wuyan Ma'u amma ina ya kasa domin sai na ji wani karfi na shiga ta, hankaɗe shi na yi gefe ya ta ga taga taga kamar zai faɗi. Sakin mata wuya na yi na jawo mayafin da ke jikinta na matse mata wuya da shi, na ƙara jawo ta ta dawo na sake maida ta ta ƙara buguwa da jikin mota gam! Ban tsaya ba na saka duka hannuwana dama da hauni na riƙa yarfa mata maruka kamar Allah ya aiko ni . Sai ga Alhaji Mustapha ya yo kaina shi da megadin shi suna neman raba ni da Ma'u.

"Ke mahaukaciya ce! Yar'uwan ki ce fa?

Ya faɗa lokacin da suka ƙwaci Ma'u daga hannuna ta na bayan shi duƙe ta na maida numfashi, Megadi na gefe ya na salati shi kuma Alhaji Mustpha ni ya ke kallo ganin yadda na ke huci kamar zakin da ya daɗe a dawa bai samu abinci ba.
Chapter 67 · 0% Book details