← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 89

Sashe 38

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muka yi shuru ni da ita, shi kuma sai ya zagayo ya zauna kusa da ni har kafaɗan shi na gogan nawa, a hankali na ƙara matsawa sai na ga ya ƙara matsoni, ina kuma ɗaga kaina sai na ga ta na kallon mu shi ya sa na barsa ban ƙara matsawa ba.

"Na yi kewar ki sosai Sadiya ta."

Haka ya yi min raɗa a kunne ya faɗa mini, ko kallon shi ban yi ba domin sai na ga kamar rawan jikin Yallaɓai ya ƙaru ne saboda a gaban matar shi ne, ni zai faɗa ma burauba a gaban matarsa. Kallo ma ni bai ishe ni ba sai ma na juya masa ƙeya ina ce ma Gimbiya ta sha ruwa mana.

"Zan sha "

Ta sake faÉ—a a hankali tana wasa da yatsun hannun Baby.

"Anty Gimbiya ina ta kuka ina so na je wajen ku ke da Abba."

Baby ta faɗa cikin shagwaɓa ita kuma sai ta shafa kanta ta na faɗin" Ban sani ba da kin kirani da gudu zan zo na tafi da ke My Baby."
Sai Baby ta fara murna, ni ko gani zaune ina yaƙe ban yi mgana ba.

"To ko Baby za ta ture gwamatin Jidda ne kawai sai ki tafi da ita ta ta ya ki kwana."

Sai ta yi mirmishi ta na kallon shi kafin ta ce" Sai abin da ka ce Daddy"
"Duk É—aya ne ko Baby ko Jidda Daugther. Gwara Jidda ma ba za ta yi rigima ba amma Baby ba za ta yarda ki ta fi da Jidda ita ki bar ta ba."
"Sai na tafi da su gabaÉ—aya mana Daddy."
Ta faɗa cikin shagwaɓa ta na yi masa wani kallo. Kawai sai na ga ya yi wani mirmishi, mirnishin da na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai sake yi ma wata mace irin shi ba sai gashi a gaba na a gaban yara Yallaɓai ke hira da wata mace ta na masa shagwaɓa ya na jin daɗi.

"Daughter.."

Ya faÉ—a ya na yar dariya sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujera ya na faÉ—in" Ke ma kin cika rigima. Su biyu ai sun yi miki yawa. Ita Madam sai a bar ta ita kaÉ—ai ko su je kawai ni kaÉ—ai na ishe ki ko Sadiya ta?
Ya ƙarishe zencensa ya na kallona, ban ko kalle shi ba amma a cikin raina ina jinjina karfin halin irin na Yallaɓai wato ma har ya raba mini yayan nawa amma ni ban da darajan da zai faɗa min, ni fa a baya ne na ke da bakin cikawa a kan Yallaɓai amma a yanzu na shaida munafuki ne na gidi ma, ni fa yanzu ba duka ma mganganunsa ne abin yarda a wajena ba, na tabbata tunda ya ƙara aure zai kulla alaqa da ƙarya da munafunci.

"Ya baƙun ta?

Na katse shurun namu da mganata. Cikin wani karya murya ta ce" Baƙunta ya fara bin jiki."
Ta faɗa ta na ƴar dariya, ni kuma sai na yi mirmishi ba tare da na sake yin magana ba amma da za a tona zuciyata baƙinƙirin ta ke, kiran sunan Allah kawai na ke yi domin saura kiris na fallasa a sirin zuciyata. Mun zauna shuru har na tsawom mintina ashirin ita dai sai hira ta ke yi da su Jidda Yallaɓai kuma ya na ta faman latsa waya ni kuma ina zaune abin tausayi E mana abar tausayi ni da gidana amma na kasa sakewa, sai satan kallon Gimbiya na ke yi sai da na ƙara lura dakyau na ga har da kwalliya ma ta yi, to wai ta manta yau mijin ma ya fita ɗakin ta ne? Sai da na lura sosai sai na ga jefi jefi suna kallon juna ita da Yallaɓai suna sakar ma juna mirmishi, ji na yi kamar na tashi na bar musu falon amma na ƙara dai haƙuri na zauna, ina so na duba lokaci amma wayata na baro ta a ɗaki kuma gashi ba na so na tambayi Yallaɓai kawai sai na yi shuru kamar in yi tagumi in fashe da kuka haka na ji, ban yi hakan ba amma acikin zuciyata Allah ya saka min kawai na ke faɗa domin Yallaɓai ya gama cutata.

Kiran sa a ka yi a waya sai ya tashi ya koma falon shi, ba daÉ—ewa ya dawo yadda ya bar mu haka ya dawo ya tadda mu, ita dai ta na ta hira da Baby mai shegen surutu in ta fara ba ta son ta tsayawa gwara Jidda ta fita Aji shi ya sa na ke son ta ba ta cika surutu haka barkatai ba. sai balla mata harara na ke yi ta gefe amma yarinyar nan ba ta ji ba sai zuba ta ke yi kamar Æ´aÆ´an kanya.

"Kun yi shuru abin ku."

Ya faɗa yana mai sake zama gefena sai a lokacin na saci kallon Yallaɓai kwata kwata bai yi min kyau ba a raina ma faɗi na ke yi Yallaɓai an yi girman banza ka rufe arba'in kana wani cin zanzaro. A baya ne in yi ta masa nacin saka ƙananun kaya ya yi ta kuma cewa shi ba ya son sakawa amma sai ga shi yanzu ya saka har da zanzaro saboda ya burge wata tir! Tsaki na ja a hankali amma kuma sautin ya fita tun da shi ya ji har kuma sai ya kalleni na basar na haɗe rai kamar ba ni ba shi ya sa bai samu damar yi min wata mgana ba.

"Jidda kama hannun Baby ku je falona ku kunna Tv ku yi kallo kafin na gama mgana da Ummomin na ku."

Haka ya faɗa ya na kallon Jidda sai ta amsa masa da to. Amma Baby har da ƙin tashi ta makale ma Gimbiya. Shi ya tsaya ya na lallashinta shi da Gimbiyar ni ko tsawa na daka mata kafin na ce" Za ki tashi ko sai na zo nan na tattaka ki ?
Na faÉ—a ina mata wani kallo ai kafin ma na yi wani matsi ta sauko daga jikin Gimbiyar ta na neman yi min kuka.

"Kina ɓare min baki yanzu jikin ki zai gaya miki."

Na faɗa ina kallonta jin haka yasa ta koma bayan Jidda ta raɓe, shi kuma Yallabai ni ya kallah kafin ya ce" Haba! Sai ki da ke ta?
"Ta yi kukan sai ka gani."
Na bashi amsa a takaice sai na ga kawai ya tsaya ya na kallona ni kuma na É—aure fuska ina kallon jidda kafin na ce" Kama ta ku je mana."
Sai ta riƙe hannun Baby suka wuce wacce ta yi narai narai kamar za ta yi kuka ga shi ba hali kuka Gimbiya na ɗaga mata hannu da alamun ta na nan ba tafiya za ta yi ba.

Sai da suka shige da mintina sannan Yallaɓai ya gyara zama gyara murya ya yi irin na juyo na kalle shi sai ma na ƙara yamma da fuskata.
"Wannan hijabin fa? Ki cire shi ki sha iska mana."
Ya faÉ—a ya na kama gefen Hijabin kamar da gayya ya yi maganar ni zai ma mutumci gaban matarsa. Daman hijabin da na yi salla dashi ne ban cire ba, kawai sai na fizge hijabin daga hannun shi kafin na ce.

"Ka bar min kayana. Tun da kuma ba zafi ake yi ba."

Na faɗa ina jin kamar na rufe shi da duka ni fa na kosa ya gama maganarsa na shige ciki zuciyata ta kusa daina ɗaukan munafuncin Yallaɓai kar ta kai mu ga in ya faɗa na maida masa mara daɗi.

"Halima."

Ya kira sunana amsawa kawai na yi ban kalle shi ba saboda ni dai yanzu in Yallaɓai ya kirani da Halima ban wani rawan jiki saboda na san na yaudara ne shi ya sa na daina ma rawan jiki.

"Daughter."

"Na'am. Daddy".

Ta amsa cikin sanyin sauti. Ina zaune ne amma ji na ke yi kamar ina yawo a sararin samaniya saboda hazo hazo na fara gani saboda wulaƙancin Yallaɓai, ni ya kira sunana sunan da ko ubana da ya yankamin rago ba ya kirana da wannan sunan ya na sakayawa saboda girmamawa haka sauran ahalina Sadiya suke kirana amma shi yau sabida cin mutumci ni ya kira ni da Halima ita kuma tunda sunan Nene gare ta ba zai iya kiran ta da sunanta na yanka ma sai ya sakaya kamar yadda ya saba. Wani iska na furzar daga bakina da ya sa sai da suka kalleni gabaɗayan su.

"Lafiya?

Ya faɗa ya na kallona, wani irin kallon sama da ƙasa na yi masa kawai na ɗauke kaina shima kuma ya ga yanayin kallon shi ya sa bai ƙara nema na da wata mgana ba ya kama kan shi.

"Na san kun san dalilin da ya sa na tara ku anan ko?

Daga ni har ita shuru muka yi masa, ni ko a raina na ce to kasan mun sani uban miye kuma za ka taramu? Amma dai ban yi magana ba sai ma na maida kaina ƙasa kawai ina wasa da gefen Hijabina.

"Duk da kun sani amna tunatarwa tana daÉ—i. A matsayina na wanda kuke zaune domin shi akwai wasu mganganu da ya kamata na sake tunatar daku game da su."

Uhm! A cikin raina na ja sheɗata na fesar ta baki, saboda yau wai ni ce zaune da wata matar a matsayin matar Yallaɓai bayan ni. Na kasa gasgatawa amma yanzu gasgatawa ya zama dole tunda ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya ya ke faruwa.

"Sadiya ga abokiyar zama nan na kawo miki. Aurena da Daugther Allah ne ya kaddaro shi, ke ma Daugther ga Yayanan na yi miki. Abun fatana na farko shine haÉ—in kan ku, ku sani wata ba ta fi wata a wajena ba dukkan ku mata ne da aure ya samar min da ku, ina fatan za ku haÉ—e kan ku ku zauna da juna lafiya domin samun zaman lafiya ta nima."

"In sha Allahu."

Ta faÉ—a cikin sanyin murya, ni ko ban ce komai ba sai daga baya da na ga ya yi shuru kenan ni ya je jira na ce wani abu.

"Allah ya ba mu zaman lafiya."

Suka amsa a tare da shi da Amin.
Chapter 38 · 0% Book details