Sashe 58
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina mirmishi na ce" Ko? To ko gobe a sake yo miki wani ne?
Kanta na ƙasa ta ce" In ba zai zama takura ba ina so."
"Wani takura. Bakomai zan yo miki in kuma akwai wani abun da kike so ne ki faÉ—a min ko shi sai ya faÉ—a min sai na dafo miki."
"To na gode."
Ta faÉ—a ta na mirmishi.
Daga shi har Maman Farko suna jin mu amma ba su yi magana ba suna ta dai mirmishi sallama muka yi musu Baby Yallaɓai sai da ya ɗauketa daga zuwa dubiya ta haye gadon asibiti ta na sharan barci. Bayan mun koma gida Yallaɓai sai wani nan nan ya ke yi da ni a raina na ce Namiji. Namiji sai shi wai saboda ina ma matarsa kirki shi ne na zama fara yanzu a idon shi haka ya riƙa nanike min da daddare ya saka mu ɓarnan ruwa haka ma bayan salla asuba shi dai kawai na lura ya na cikin farinciki har wani suna ya sauya min ya na maƙale murya da kirana Abar ƙauna a raina na ce daga baya kenan an yi sadaka da bazawara.
Kamar yadda na yi alƙwari na sake yi mata faten Yallaɓai ya kai mata ta kirani ta na ta min godiya na ce bakomai ranar ban je asibitin ba sai washegari na iske Naja'atu da wasu ƙawayen Gimbiya har da abokan aikinta haka na ji Najan na faɗa ma Maman farko na dai shiga mun gaisa na fito domin na ga ana ta nuna ni, ko ba a yi mgana ba na san sai na fita za a ce ita ce kishiyar ta ki? Ranar ma mun sake haɗewa da Anty Bahijja ina kuma asibitin sai ga Ma'u ta zo tun ina mamakim munafunci Ma'u har na zo na daina amma ta ba ni mamaki da na ganta sanin ni dai ban faɗa ma kowa ba sai Ya Aina ita ma Marwa ce da muka yi waya na faɗa mata sai ta sanar da ita shi ne ta kira ta ji, har ta ce ko za ta yi ma su Ya Balki mgana ne su zo asibitin su duba ta na ce su yi zaman su ai ta ji sauƙi haba abin sai ya yi yawa gani ni ina ta zarya sai kuma na gayyato dangina.
Na san za ta sani tun da ta na tare da Anty Bahijja amma zuwan na ta ne ya fi ba ni mamaki kuma ita kanta ta É—an yi wani iri da ta ganni.
Mun gaisa da ita sama sama ina mai mamakinta Anty Bahijja ta yi mata jagora zuwa ciki ba daɗewa sai ga su sun fito har da ma wasu ƙawayen Gimbiyar da ita Naja'atun a gabansu Anty Bahijja ta kalleni ta na faɗin.
"Sadiya ashe ba ki faÉ—a ma kowa a gidanku Gimbiya ba ta da lafiya ba?
Sai na kalleta amma ban yi magana ba saboda na ga renin wayan ne ya yi yawa. To Gimbiyar uwata ce da zan yi she ɗan ciwonta a dangi ko Yallaɓai ne ai sai na ga daman na faɗa ballantana ita.
"Sai da na kira Ma'u ina ta mata tsiyan ba ta zo ba shi ne ta ke min rantsuwan ba ta sani ba. Kai tsaye na ce to laifin Sadiya ne wannan ita ce ba ta sanar da ku ba."
Ma'u na yi ma wani kallo kafin na sauke kallona kan Anty Bahijja kafin na ce" Ban faÉ—a ba amma tun da ita ta sani gashi har ta zo na wakiltata ta sanar da su."
Daga haka na juya fuskata ina kallon wani bangaren raina kawai na ji yana tafasa ji na ke yi kamar na je na shake Ma'u.
"Ai ko zan faÉ—a ma su Ya Murja. Don dai dubiya mene a ciki? In sha Allahu na san za su zo"
Ni dai ƙala ban ƙara ce musu ba har suka gama mganan da ƙawayen Gimbiyar za su tafi kamar Anty Bahijja ta kwanta musu haka ta raka su ta na yi musu godiya ni fa matar nan har mamakinta na ke yi, ba ta da yadda za ta yi dani ne da tuni ta saka an koreni Gimbiya ta mamaye komai sai dai kuma ta Allah ba ta ta ba na riga na zame mata ciwon ido.
Ma'u da za ta tafi har da ba da kuÉ—i ina zaune ina ganin ikon Allah da ta yi min sallama ina ji amma ban amsa mata ba na haÉ—e rai suka fice ita da Anty Bahijja na raka su da harara kafin na ja tsaki.
Ranar kafin na bar asibitin nan sai da raina ya ɓaci Anty Bahijja daga ganin sauran fate da na yi ma Gimbiya jiya ta ce a bata ta shanye ta fara faɗa ba fa komai ne za ta riƙa sha ko ci ba kar ta manta ta na da juna biyu kuma ta na ƙarkashin kulawan likito ci ne.
"Ke Bahijja to ai fanten ne ta ke samu ya zauna mata. Kuma Sadiya ce ke yo mata ta na aikowa dashi wani zubin ma da kanta ta ke kawowa."
"Koma wace ce dai bai kamata a barta ta sha ba. Abu tun jiya duk ya yi sanyi sai kuma a bar ta tasha? Ai sai ya jawo mata wani illar Allah na tuba"
Sai ta É—anÉ—ana faten da sauri ta furzar ta na faÉ—in" TabÉ—ijan wannan kaifin tsamin kawai ya isa ya zubar da ciki."
Ina tsaye a É—akin ina kallonta kuma ina jin ta amma matar nan ba ta fasa yada min mgana ba.
"Anty Bahijja ni na ke son tsamin fa.'
Gimbiya ta faɗa a hankali ita Maman farko shuru ta yi ba ta ƙara mgana ba.
"Kuma Likitoci sun ce ba wata matsala ko Mama?
Naja'atu ta faɗa ta na mai kallon Maman farko da ta yi kamar ba ta ji ba saboda abin ya ba ta haushi. Amma Anty Bahijja ƙiri ƙiri ta hana Gimbiya shan faten nan ta ce ba za ta sha ba.
"To wanne zan sha?
"Ba dai fate ba. Zan saka Suhailat ta yo miki ba shikenan ba"
Har Gimbiya sai da ta kalleta amma ba ta yi mgana ba. Nima ban ce komai ba na tattara kololina na saka a kwando na yi musu sallama shi ne Anty Bahijjan ta ke ce min" Ba raina ƙokarin ki na yi ba. An gode amma ya yi tsami da yawa ne kin gane?
"Kar ki damu. Ki cigaba da yi mata mara tsamin wanda ba zai zubar da ciki ba."
Ina gama faÉ—in haka na fice ina yi ma Maman farko sai anjuma ta amsa min da cewa na gaida gida.
Muna tafe acikin adaidaita ina jin ƙuna a raina na kuma ce tunda shi alheri ya koma sharri shike nan kuma an gama daman ni saboda Allah na yi da kuma Yallaɓai amma tunda lamarin ya zo da cin mutumci an gama mgana. Tun daga ranar ban ƙara dafa wani abu da sunan Gimbiya ba amma kuma ban fasa kai ma Maman farko. Gimbiyar da kanta ta kirani a waya ta na bani haƙuri na ce kar ta damu bakomai.
Kawai ranar da Gimbiya ta cika sati a asibiti sai ga kiran Yallaɓai a waya wai don Allah na taimaka na yi ma Gimbiya faten wake kai tsaye ba kwana kwana na ce.
"Gaskiya ba zan yi ba Yallaɓai. Amma ka kira Anty Bahijja ta yi mata daga gidan ta."
"Saboda mene?
Ya tambaya cikin mamaki kai tsaye na ce" Saboda ba na son ƙananun mganganu ka kuma sanni ba ni da haƙuri kamar zawo na ke yi in raina ya ɓaci"
"Me ya faru?
"Komai ma ya faru. Na yo fate Anty Bahijja ta hana Gimbiya sha ta ce ya yi tsami da yawa wannan zai iya zubar mata ciki ma."
"Ita Anty Bahijjan ta ce?
"Ya wuce wai."
Na faÉ—a ina kaÉ—a kafa kamar ya na ganina.
"To ina ruwanki da ita? Ai ba don ita kike yi ba."
"Don Allah na ke yi amma ba shi zai saka na zauna ana ci mun mutumci ba. Daga alheri sai ya koma tsiya kuma?
Na ƙarishe faɗa a fusace shi kuma ganin na fusata ya sa ya sassauta murya ya na faɗin" Na ji to ki yi hakuri kin ji ko?
"Na yi haƙuri amma girkin ne ba zan yi ba."
"To ni ne na ce ko Daughter? Bai kamata ki damu da mganar Anty Bahijja kin san halinta."
"Dole fa na damu. In wani abu ya zo ya faru ba fata ake yi ba mganganu suka tashi fa? Kasan ba zan zauna a ci zarafi ba in kuma na yi magana a ce na cika ƙorafi daga na ce an yi min kaza sai na ce an yi min kaza."
Da gayya na daba masa mgana kuma na san ya san dashi na ke yo ina dalili daga abin arziki ban da ma ina da zuciyar Imani ni har wata kishiya ne zan zauna ina ma girki ina zuwa kai mata asibiti duk wannan sadaukarwan da na yi ba ta gani ba ta na neman ci min mutumci to ba ta isa ba mganin ayi ma to kar ma a fara shi.
"Ki yi hakuri na ce ko?
"Na faɗa maka na haƙura."
"To za ki yi É—in?
"A'a."
"Me ya sa?
"Ai na faÉ—a maka dalilina."
Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Duk na ji kuma zam mata mgana amma dai yanzu ki yi hakuri saboda ni saboda Daugther ki yi mata don Allah."
Sai na yi shuru ban yi magana ba amma ina ta ƙunƙuni.
"Abar ƙaunata ki yi don Allah. Ni na yarda dake shi ya sa a komai nawa na ke sakawa a ciki. Da gaske na ke ke ɗin amintattaciya ta ce Sadiya."
Nan ma na yi masa shuru har dai ya gaji ya ce" Kin ji ko?
"Na ji."
"Za ki yi É—in?
"Uhm."
Ina jin sautin mirmishin shi kafin ya ce" Yauwa Abar ƙaunata. Allah ya yi albarka."
"Amin."
Na amsa da Amin aciki ciki shi kuma har da yo min kiss ta cikin waya kafin ya ce" Sai na dawo."