Sashe 36
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na yi mamakin yadda daga tura saƙo ko mintina goma ba a yi ba sai ga amsar shi kamar wayar ta na hannun shi ne.
"To sai yaushe?
Haka kawai ya ce, sai kawai na ga kamar so ya ke yi ya yi wasa da hankalina. Nan take na saka wayata a filght mode na dankwafar da wayar ina girgiza kafa, har da su kaɗa harshe takaici ya isheni ni kaɗai. Ina cikin wannan halin Amina ta shigo sai na ɗan saki, kamar ta san in na zauna ni kaɗai tunani zai iya yi mun kutse zaman ta a kusa da ni ya sa sai na maida hankalina kanta muna ta ɗan taɓa hira a kan dai yan gidanmu ne.
"Ya Sadiya Ma'u ta ba ni mamaki. Ni fa in kika ce munafuka ce in yi ta mamakinta."
Mirmishin takaici na yi kafin na ce" Uhm ai wanda bai san halinta ba zai taɓa yarda munafuka ba ce. Ta iya kissa fuska biyu gare ta shi ya sa."
Amina ta jinjina kai kafin ta ce" Na gani kuwa. Ai da Ya Aina ta mata mgana sai ta fara kuka ta na cewa ita ba da wata manufa ta je Gwammaja ba. "
Ina dariya na ce" To ko da wata manufar ne za ta nuna ne? Makira ce fa Ma'u ina faɗa muku ba ku yarda. Uhm! Shi ya sa ni ban taɓa son Ma'u ba halayyanta ba su da kyau sam"
Sai Amina ta ja numfashi kafin ta ce" Uhm ai na gani yanzu. Ni dai fatana kar ta je ta rika bin Amaryan Yallaɓai ta rikita muku zama tunda ta shige ma yayar ta sa."
"Za ta iya aikata komai domin ta ga ni na yi ƙasa. Amma kuma komai za ta yi na fi karfinta ni Allah na ce ita kuma tunda makirci ta saka ma gaba sai dai ya ƙare a kanta."
"Amin wallahi kuwa ah."
Amina ta faɗa har ta na riƙe baki ita fa Ma'u ce ke ba ta mamaki, ni ko na ce ta ma daina mamaki Ma'u ta wuce tunanin su wallahi nan na ke faɗa mata wasu sirrukan nawa ita ke faɗa ma Anty Bahijja in muka haɗu ta rika zagina ta yada min mgana na ƙarishe da cewa" Ina da ta cewa ne Amina? Ƴar'uwata ce ta ba da ni fa, shi ya sa na ke addu'an Allah ya shiga tsakanina da Ma'u duk mugun nufin ta ya koma kanta."
"Amin in sha Allahu."
Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na cigaba da faɗin" Ita fa abin da ya faru na rashin auran Ya Hamza ne ta riƙe a ranta shi ya sa ta ke jin haushin ki Ya Sadiya."
"Sai dai ko ta mutu amma Ya Hamza ya yi mata nisa. Kuma wallahi tallahi ba na nadaman abin da na yi har nan da gaban Abada Amina"
Na faɗa ina mai jadadda mganata sannan na ƙara da cewa" Ba ki lura ƙawarta Shema na ta ya ta ba. Ita kuma shegiya ta ki auru ai duk wanda ya ce tunkunyar wani ba za ta tafasa ba ina mai tabbatar miki da na shi ko ɗumi ba za ta yi ba. Kuma ko alaqarsu da Ma'u hali ne ya zo ɗaya amma in kin lura Ma'u ta fita wayau ita kuma har da kwaɗayi gani ta ke yi Ma'un na ba ta duniya ita kuma saboda mijinta na da kuɗi sai ta riƙa yi ma Shema'un abu kamar ita ce uwarta."
Na ƙarishe faɗa ina mai kallon Amina wacce ta jinjina kai kafin ta ce" Kwarai kuwa. Kamar raƙumi da alaqarsa haka Ma'u ke jan Shema."
Ƙwafa na yi kafin na ce" Gungun munafukai ai sai munafuncin su ya ci su in sha Allahu." Nan muka cigaba da hira har muka gangaro kan Ya Murja na ce ai ita wannan na daɗe da sanin yadda ta ɗauki Ma'u ba haka ta ɗauke mu ba, sannan kuma da ƙwaɗayin itama, wani cewa halina ne ba ta so duk mgana ce amma jiya ta ɗan samu muhallin afuwa acikin zuciyata a karon farko da ta gano Ma'u ba ta kyauta ba.
Sannan Ya Abubakar ma sai a hankali. Shima raƙumin ne sai abin da ya ga an karkata acan ya ke. Har neman fitan hayyacinsa ya ke yi in dai akan lamarin Ma'u ne.
Amina ta bushe da dariya kafin ta ce" Tsohuwar zuma ce Ya Sadiya "
Nima ina taya ta dariyan na ce" Shi ya sa wani lokacin na ke yi masa uzuri."
Mun daÉ—e muna hira har aka kira sallar isha'i sannan ta fita ta ce min za ta je falo ta yi kallo nima na ce in na idar da sallah zan fito.
Una ko idarwa na fito na iske suna kallon wani indian Movie a Bolloywood Kuchi kuchi hota hae. Ina son film ɗin tuni na zauna muna kallo har da Saude da Jidda Baby ta kwanta ita da Sultana ɗiyar Amina ƙarama, muna cikin kallon Amina ta je ta ɗumamo mana Tuwo muna ci muna ƙona hannu sannan muna kallo bayan mun gama muka kora da lemu da ruwa, mune har 11pm har sai da aka gama film ɗin nan sannan muka tashi har Jidda ba ta yi barci ba sai da a ka gama sannan muka kora su ɗaki, ni na tsaya na rage hasken duka ɗakunan na duba ko'ina sannan na je na kwanta na iske Amina ta yi shirin barci ta na kwance suna waya da mijinta sai na ba su waje na shiga Tiolet na kama ruwa na yi brush, ko da na fito sun gama wayar sai nima na yi shirin kwanciya na saka kayan barci muka kwanta, mun ɗan fara hira ba daɗe barci ya ɗaukeni ban ƙara sanin kaina ba sai huɗun asuba sannan na tashi na ɗauro alwala na yi nafilfilu, sai da a ka fara kiran sallar farko sanman na fita na ta da su Jidda. Dakyar na idar da sallar asuba saboda barci na cin idona na haye gado ba ni na tashi ba sai tara na safe.
Na iske gida ƙal an gyara ko'ina ya na tashin kamshi har sun karyawa Amina ta shirya sai tafiya Ɗorayi ita da Saude. Ina zama a saman kujera a falon su Jidda na ce" Ke Amina da sassafen nan? Kamar ana koran ki?
Amina na gyara É—aurin É—ankwalinta ta ce" Yau fa zan koma kaduna Ya Sadiya gwara na je na gaida su Alhaji na É—an zauna zuwa azahar haka."
"To tare da Dattin za ku koma?
Sai ta gyaɗa min kai, ya na iya duk da ba na son tafiyarta haka nan na yi shuru ina laifi an yi min kwana uku. Ni da yara sai rakiya har bakin get muna ɗaga musu Hannu Saude dai gobe ma za ta dawo. Sai ga shi mun dawo cikin gida mun yi tsuru ni da su. Zama kawai na yi a falo ina nazarin rayuwa. Yanzu yau kwanan Yallaɓai biyu ya na cikin garin nan amma ba ya tare da mu sai na ji kwalla sun kawo min amma na yi saurin mayarwa. Tea na ce Jidda ta haɗo min na ci da Dankalin da Amina ta soya da safe. Su daman sum yi wankansu ni ce bayan na gama na tashi na yo wanka yau ma ɗin sabuwat atamfa ta na saka, ban zauna a ɗaki ba fito wajen su Jidda saboda su ɗeɓe min kewa. Baby ta ɗauke mana hankali da rawan drama ɗin da suka yi a makaranta ni da Jidda muna ta dariya.
Haka muka yinin mu kaɗai a gida sai can bayan La'asar Musbahu ya zo ya ce min Yallaɓai ne ya ce ya zo ya duba mu ina mirmiahi na ce" To me zai same mu? Ai dole ma mu saba tunda haka tafiyar za ta miƙa."
Ban tambaye shi ba da bakinsa ya ke faɗa min Yallaɓai bai fito Office ba kwana biyu a raina na ce ya fito ya na can ya na cin amarcin sa, ya ɗan daɗe tunda har sai da ya tsaya ya ci abincin da na yi. Da zai tafi Baby sai ta fara rigiman wai ita sai ya kaita wajen Abba da Anty Gimbiya tun jiya ta fara min riginan Ina Abba na ce mata ya na gidan Anty Gimbiya ta ce sai ta je na ce ba yanzu ba, to jiyan ban biye mata ba sai yau ne bayan Tafiyan Musbahu yarinyar nan ta kafa min kuka da rigiman ita sai an kaita wajen Abba da Anty Gimbiya.
Yarinyar nan har da zan shiga salla sai da na yi ma ta jan ido akan ta tashi a saman cafet ɗin ta je ta yi salla amma ba ta ji ba. Har na idar da sallah na fito ta na wajen ta na min kukan banza ba tare da na yi mata mgana ba na koma ɗaki na ɗauko bulalar injin ce wacce na ke dukansu ne, ƙarama ce ma wannan ɗayar babban Yallaɓai ya dauke ta wai ba ta dukan mutane ba ne kamar zan doke dabbobi.
Ta na kwancen nan ta na rigima sai dai ta ji saukan bulala tuni ta fara ihu tun tana kiran Abba sai ta koma Umma ki yi hakuri Ya Jidda Ya jidda. Ta na kuka ta na majina karshenta dai Jiddan ta ƙwace ta, ta na ba ni hakuri.
"Don Allah Umma ki yi haƙuri."