← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 89

Sashe 69

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Babu wani hukuma. Ni nan zan tsaya miki sai na ji dalilin wannan kazafin da cin mutumci. Ki daina kuka ki bar min komai a hannuna kawai."

"Ni dai a'a ka bari na kai su ƙara."

"Na ce a'a ba za ki bi umarnina ba ne Sadiya?

Ya yayyaƙomin kamar zai dake ni ai sai na yi shuru

"Ko ba ki yarda da ni ba ne? Ko domin Anty Bahijja na yayata sai na zauna na zura ido a ci zarafin ki? Ba zan bar wannan mganar ba sai na ji dalilin wannan tozarcin. Na rantse da wanda raina ke hannun shi sai na tada ma duk wanda ya yi silan a taruwa a ci miki zarafi ki hankali shima"

Ya faɗa a fusace har ya na dukan sitayari duk fusata ta sai da na koma na yi shuru saboda na ga Yallaɓai ya harzuka. Daman ya kan daɗe ran shi bai ɓaci ba in kuma ran shi ya ɓaci to ba shi da kyau.
Sai na koma gefe ina maida numfashi ina jera ajiyar zuciya.

"Na maida ke gida ko gidan Alhaji?

"Mu je gidan Ya Aina."

Na faÉ—a ba tare da wani tunani ba sai ya yi shuru bai yi mgana ba ana ta kuma cigaba da kiran wayarsa

"Nene ina tare da Sadiya. Zan taho gidan yanzu in sha Allahu."

Na ji ya na faÉ—a sai na É—aga kai na kalle shi, ya na waya ne kuma Nenen da ya ambata ya sa na gane da ita ya ke waya.

"Nene gidan Yayarta zan kai ta. Yanzu zan dawo gida, ki kuma sanar da Bahijja ba Sadiya ta tozarta ba ni ta tozarta na kuma gode mata."

Sai na zo."

Ya faɗa kafin ya kashe wayar haka muka yi tafiyar nan shuru ni ina ta sauke ajiyar zuciya shi kuma ya na ta tsula gudu ba daɗewa muka iso gidan Ya Aina ya sauke ni kuma bai ce min komai ba ya juya motar a fusace ya bar layin ni kuma na taka na shiga gidan Ya Aina da sallama cikin muryata da ke shaƙe saboda kukan da shaƙa kamar an yi min mutuwa.

*Janafty*
*TKG018*

*Littafin TURKEN GIDA, 1k ne akan manhajar Telegram.*
09069067488

Na shiga gidan Ya Aina ko gani ba na yi saboda tashin hankali da damuwa. Tafe na ke ina jefa ƙafuwana ba tare da na san in da za su faɗa ba. Ya Aina na hanga a ɗan karamin madafinta dake tsakar gida sai ƙannen Marwa na gefen ɗakinta a kan tarbarma suna cin abinci. Ko sallama ma ban yi ba ni dai kawai na shigo kuma na dumfari ɗakin Ya Aina so na ke yi na samu waje ni kaɗai na fashe da kuka na yi kuka mai ƙara mai sauti ko zan ci ɗan sauƙi sauƙi abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata.

"Laa Mama ga Umma Sadiya."

Na ji wani cikin yaran ya faɗa amma ba zan iya gane ko waye a cikin su ba. Ni dai ƙafafuwana na taka suka shigar da ni falon Ya Aina sannan lokaci ɗaya na zube a saman cafet ɗin ɗakin tare da fashewa da kuka mai sautin da har a tsakar gida ana jiyo kukana.

Da gudu Ya Aina ta shigo ina jin salatinta.
"Innalillahi me zan gani Sadiya?
Ta faÉ—a lokaci É—aya ta na zama kusa da ni ta saka hannu ta É—ago ni ta na mai kiran sunana.

"Sadiya"

"Ke Sadiya me ya faru?

Ta ke faɗa cikin tashin hankali da damuwa. Ban buɗe idanuwana ba amma na ɗora kaina a saman cinyarta ina cigaba da rera kukana, sai na ji kamar jikina ya na wani irin yam tsikar jikina sun tashi yam! Zuciyata na ji ta buɗe ina so na yi kuka mai yawan da na daɗe ban yi irin shi ba. Sannan ji na a saman cinyar Ya Aina ya ƙara raunana raunina da ya sa na ji kamar tsawon shekaru ban samu kafaɗan da zai tallafeni ba, shi ya sa na daɗe ban yi kukan da na ke jin yau ya na tahowa daga ƙasan zuciyata ba.

"Kai ku koma ku cigaba da cin abincin ku."

Na ji ta na faɗa, sai na ɗan buɗe idanuwana da suka kumbura saboda kuka sai na gansu sun yi jere a bakin kofa suna kallon mu. Maganarta ya sa suka fara fita ɗaya bayan ɗaya amma fuskokinsu dañkare da mamakin ganina ina kuka.

  Sai da suka fice sannan Ya Aina ta ƙara maida hankalinta a kaina.
"Sadiya me ke faruwa ne? 
Nan ma na yi mata shuru ina ta kuka hawaye da majina na zuba lokaci É—aya.

"Ko wani abu ya faru tsakanin ki da Baban su Jidda ne?

Sai na ƙara ma kukana Volume amma na kasa mgana.

"Sadiya ki bar kukan nan ki yi min bayani. Duk kin É—aga min hankali."

Ina shassheƙa na ce" Ki bar ni na yi kuka Ya Aina.. ki bar ni na yi kukan da zuciyata za ta samu natsuwa."
Na ƙarishe faɗa ina mai ƙara fashewa da kuka sai ta ƙyaleni ina ta kukana amma ta saka hannunta guda ɗaya a bayana ta na bubbugawa alaman lallashi mun fi karfin sama da mintina ashirin sannan kukan ya fara ɗaukewa sai shessheƙa da kuma jan majina.

"Sadiya me ke faruwa?

Ta faÉ—a ta na kallona dai-dai lokacin da na tashi daga saman cinyarta ina faman goge hawayena da É—ankwalina da ya zame daga saman kaina.

"Ya Aina Ma'u ta ba da gudummuwa an tozartani yau a dangin su Yusuf"

"Ma'u kuma?

Ya Aina ta maimaita sunan ta cikin mamaki. Kawai sai na ji sabon kuka ya taso min ina kukan ina labarta ma Ya Aina abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe.

"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un"

"Anty Bahijja ta ci min mutumci ta kirani dangin bokaye  da asiri. Ta ce aurena da Yusuf ba ta ga amfanin shi ba, Ya Aina wai ni suke zargi da ƙoƙarin zubar da cikin Amaryan Yallaɓai? Duk ta dalilin Ma'u. Domin ita ce ta ba su damar duk abin da suka yi min Ya Aina."

Na ƙarishe faɗa ina gunjin kuka da ƙarfi saboda sai na ji kamar a alokacin ma abin ya ke faruwa.

"Innalillahi. Ita Ma'un ce ta aikata haka? Amma ta ba ni mamaki matuƙa ban taɓa tunanin haka daga gare ta ba."

"Ba in ina cewa munafuka ba ce sai a riƙa ganin laifina ba? Yanzu dai kun yarda ko? to Ma'u ta daɗe ta na ci duduniyata a dangin Yallaɓai ta daɗe ta na son rana irin ta yau ta faru sai yau burinta ya cika."

Na faÉ—a ina goge idanuwana da hannuna kamar wata yarinya.

Ya Aina ta kasa mgana saboda lamerin ne ya zo mata cikin ba za tan da ba ta taɓa tunani ko tsammani ba. Salati kawai ta ke yi ta na ɗaukowa ta na direwa.

"Ma'u ce ta je ta faɗa ma Anty Bahijja dangin mahaifiyata yan asiri ne, sannan ita kuma Amaryan Yallaɓai ta ƙara da cewa ta na gidan ma Inna Mariya ta kawo min asiri. Sannan kuma ta ce wai yadda na gama shanye Yallaɓai haka na ke so na tusa ma Kawu Marwa domin shima a shanye shi da asiri tun da mu ƴan na gada ne ba na haya ba."

"Na shiga uku ni Aina. A ina suka ji labarim Marwan? Ko shi Abban ne ya faÉ—a?

"Ma'u ce ta fasa maganar. Ita kuma Ya Murja ce ta faɗa mata. Ba ina faɗa muku munafuka ce kuna ganin kamar ban da haƙuri ba? Uhm ni kaɗai na san wace ce Ma'u da kaidin ta."

Na faÉ—a ina mai É—aura É—ankwali na rufe kaina kukan ya tsaya amma zafin da ke cikin zuciyata ya kasa raguwa.

"Ma'u. Lalle ko Ma'u ta ba ni matuƙar mamaki."

Ta fada ta na mai yin tagumi cikin É—imuwa.

"Shi ya sa na ce an zo ƙarshe wallahi tallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da su Ya Aina. Ba zan bar wannan kazafin da suka yi min ya tafi a banza ba."

Sai ta kalleni kafin ta ce" Shi Babansu Jidda me ya ce?
"Me kuwa? Ya ce shima zai É—au mataki amma ba shi zai hana ni É—au nawa matakin ba."

"Alhajinmu ya sa ni?

"Ke kaÉ—ai kika san abin da ya faru."

Na bata amsa ina kallonta sai kawai ta miƙe tana faɗin" Ya zama dole ya sani domin magana ce da ta shafi zumunci. Kuma ni kaina ba zan so a bar maganar ba gwara a ɗau mataki tun da ya shafi zuru'armu ya kuma shafi auran ki da mutumcin ki, ya zama wajibi a shiga wannan mganar domin a yi min lamarin tufkan hanci."

"Wa za ki kira?

Na tambayeta ganin ta na É—aukan wayarta.

"Hamza zan kira. Shi sai ya kira Alhajinmu."

Sai na yi shuru saboda na san Ya Hamza zai ba ni dukkan goyon baya har sai ya ga an ƙwatamin haƙƙina. Da dai Ya Abubakar ne daman ba zan saka ran ya goyi bayana ya bar Ma'u ba amma kuma ya sani wannan karon ba gudu ba ja da baya ni da Ma'u har abada sannan sai hukuma ta shata mana layi a tsakaninmu.

A gabana Ya Aina ta zauna ta labartama Ya Hamza duk abin da ya faru ta ƙarishe da cewa" Sadiya ta zo min ciki kuka na fitan hayyaci. Hamza Ma'u ba ta kyauta ba, kuma tun da ta taɓa auren Sadiya bai kamata a yi shuru ba. Ka kira Alhaji ka faɗa mishi sai a san yadda za a shiga mganar. Domin Sadiya ta ce ba za ta yarda ba sai ta kai ta ƙara hukuma."

"Ta yi min dai-dai. "
Chapter 69 · 0% Book details