Sashe 81
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mun je gidan Munnira da sati É—aya Gimbiya ta je Rano ta yi sati Hajiyar Tafida kafa ta motsa ranar da za ta dawo gabaÉ—aya muka tafi ni da Yallabai da yara muka gaisheta sannan muka É—auko Gimbiya muka dawo gida Kano.
Rayuwa ta yi nisa kwanaki na ta gangarawa. Tuni Gimbiya har ya fara zuwa awo sannan suna ta siyayyan kayan haihuwa ta bakin mijinta. Yadda Yallaɓai ke rawan jiki kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba, sai dai na yi masa uziri bayan tsawon shekaru bakwai ba a yi haihuwa a gidan shi ba abin mamaki ba ne domin ya nuna zumuɗi, bq shi ba hatta yan'uwan shi da nata suna ta ɗoki kowa fatan shi Gimbiya ta buɗe ido lafiya.
Nima har acikin raina ina mata fatan haka. Kuma daman gashi Yallabai kuÉ—i ya ke samu kwangiloli ne ya yi ta yin su akai akai buÉ—i ko ta ko'ina tun cikin ta na wata takwas komai na haihuwa sun gama tanadar shi har ragunan da zai yanka firÉ—a firÉ—a suna can Rano. Hauwa ta ke faÉ—a min ita kuma kannenta ke kiranta suna kawo mata wani rahoton
Ni dai na koma gefe na zama yar kallo abin jaje na yi abin murna ma na yi amma ni kaina na san duk abin da ke cikin Gimbiya in ya fito duniya zai ga gata. Duk da shi uban gayyar da kan shi ya ce min namiji ne aka gani a scan ɗin ta. Ban ji haushi ba domin nima ya nuna ma ƴaƴana gata da so shi da ƴan'uwan shi, shi ya sa na danne kishina ban taɓa nuna masa wani abu kan ɓare ɓaren da ya ke yi a kan cikin Gimbiya ba.
*Janafty*
*TKG02020B*
Tun da cikin Gimbiya ya kai watan fitowarsa duniya Yallaɓai ya tattara gabaɗaya hankalin shi a kanta. Da a ce ya ga fuska zai ce ne na bashi dama ya koma can da zama har sai ta haihu tun da ga shi anguwan zoma. Sai dai bai samu wannan fuskar ba, ko da ya ke mene ne maraba da abin da ya ke yi. In ya na gidanta ba koda yaushe ya ke leƙomu ba sai dai ya kira waya in ko ya na gidana kwana kawai ke kawo shi tun safe zai fita ya je gidan Gimbiya daga nan sai ya wuce wajen aiki da daddare ma can ya ke raba dare sai sha ɗaya ya ke dawowa wata rana ma har sha biyun dare ya na kaiwa.
Jiri ƙiri Yallaɓai ya san gaskiya kuma ya ke ta ke ta. E mana rashin aldaci ya ke nuna min kuma ai ya sani ba wai bai sani ba ni tun da ai kowa ya aikata mai kyau ya na sane. In ma mara kyau ɗin ne duk ya na sane. Ban dai taɓa magana ba saboda yanzu ina cewa uffan sai cibi ya zama ƙari tsab zai ce ni lokacin da na yi cikin bai kulani da ni ba ne? Ko ƴan'uwansa su ji labari su je hassada ne, shi ya sa ban taɓa ɗaga baki na yi masa mgana ba, kuma har a cikin zuciyata ina yi mata fatan ta sauka lafiya. Shi da kan shi ya zo ya na faɗa min ya yi ma Nene magana ta kira Hajiyar Tafida a samu wacce za ta zo ta zauna da Gimbiyar har ta haihu. Na ce hakan ya kamata kwana biyu tsakani kuma ya zo ya na faɗa min autar su Hajiyar ita ce Baaba Asma'u ta zo za ta zauna da ita har ta sauka lafiya. Amma zuwanta bai hana shi sintiri a gidan ba sai dai ya rage ba kamar lokacin da ba kowa ba.
Cikin Gimbiya ya fita watan haihuwan shi har ya shiga wattani goma. In za a ƙirga ma ainihin wattanin cikin kafin ya koma baya kimanin watanni sha ɗaya kenan. Duk Yallaɓai ya tashi hankalinshi sun je asibiti an ce haihuwan ba ta taso ba, a cikin satin nan ma naguda ta ta so mata gadan gadan kamar za ta haihun suna zuwa asibiti kuma komai ya tsaya nan suka kwana shuru aka dubata suka ce ba haihuwa ba ne dole suka koma gida da cewa nan da sati ɗaya in ba ta haihu da kanta ba za su yi mata C.S ne domin ceto abin da ke cikinta lafiya.
Sati ɗaya bai cika ba wata ranar jumma'a da daddare 20 ga watan october 2016 misalin ƙarfe biyu da rabi na dare. Gimbiya ta fara zubar jini. Hankali tashe Baaba Asma'u ta kira wayar Yallaɓai ranar ya na gida na ne, barcin sa ma ya yi nauyi ni ce na tashi da vibration ya ishe ni. Ina ganin Baaba Asma'u na san mganar Gimbiya ce ni na ɗauki kiran ba ta bari na yi mgana ba cikin tashin hankali ta ce masa Gimbiyar na zubar da jini ni kaina na ruɗe saboda zubar jini ga mai naguda haɗari ne babba ban san lokacin da na ɗaka ma Yallabai uban duka a gadon baya ba ya tashi a firgice. Ina faɗa masa abin da ke faruwa ya sake firgicewa da haka zai fita daga shi sai gajeren wando da vest sai da na ce ya dawo na rarumo masa jallabiyansa ya saka na damƙa masa key ɗin motar shi, kamar zan bi shi sai kuma na fasa bai kamata na bar yara su kaɗai a gida kuma ga dare ba amma hankali ya tashi ko bayan tafiyar shi ban iya komawa barci ba ina zaune ina ta addu'an Allah ya sauwake ta lafiya duk da ba na salla ina hutu ban kwanta ba carbi na ɗauka ina ta hailala da yi ma Allah kirari ban san barci ya kwashe ni ba sai misalin ƙarfe biyar saura na asuba kiran wayar Yallaɓai ya tashe ni da cewa an yi ma Gimbiya C.S. An samu nasaran ciro ɗa Namaji har a cikin zuciyata na yi farinciki na yi ta taya Yallaɓai murna muka rabu da shi da cewa shima ba daɗewa yanzu zai taho gida.
Da asuban na faɗa ma su Jidda sun yi ƙani suna ta tsallen murna musamman ma Baby, Jidda dai sai dai ta yi mirmishi shine ƙololiyar nuna farincikinta Baby ce uwar tsalle tsalle ta na murna. Ta so ma ba za ta je Tahfez ba sai da na yi mata jan ido sannan ta bi Jidda suka tafi. Ni kuma na gyara gidan na yi ma Yallaɓai abun karyawa tun da ya ce min zai dawo gida, ina buɗe datan wayata na ga an yi saƙonni da yawa a group ɗin gidan su Yallaɓai ina shiga na ga Anty Bahijja ce ta sanar da an samu ƙaruwa a gidan Tafida Gimbiya ta haihu an samu Sadauki. Sai tagging ɗin sa ake yi ana masa murna ni ma na shiga na yi tagging ɗin sa na ce.
"Alhamdulillah. Ina ta ya ka murna Yallaɓai. Allah ya raya ita kuma Maijego Allah ya ba ta lafiyar shayarwa."
Mimisco ce kaɗai ta amsa da Amin sai Suwaiba da ta zolaye ni da cewa saura ke sai kawai na tura mata emojin mirmishi daga nan na kashe data na ijiye wayar. Yallaɓai sai wajen goma saura ya dawo gidan duk ya gaji ga barci a idanuwansa na tarbe shi cikin murna ya rumgumeni ya na ce min ya gaji sannan kuma ya na jin barci sai na ja shi tiolet na taimaka masa ya yi wanka ya so ya fara kwanciya sai na matsa masa a kan ya fara ƙaryawa sannan ya kwanta to muna saman dining ɗin ne ya ke ba ni labarin yadda komai ya faru. Ashe suna zuwa ne lokitoci suka ce a yi gaggawan saka hannu a yi mata C.S saboda cibiya ce ta sarƙe wuyan yaron. Nan ta ke ya saka hannu aka shiga da ita tiyata sai asuba suka fito da ita,  ta na can ɗakin hutu yanzu haka Baaba Asma'u ya baro tare da ita sai Nene da Anty Bahijja.
"Ta farfaÉ—o kuwa?
"E sai da ta farfaÉ—o sannan na taho ai."
Sai na ce to alhamdulillah tun da ta farfaɗo na ce masa ina so na je asibitin sai ya ce na bari ya huta in ya tashi sai mu tafi tare. Haka ko a ka yi shi na jira sai bayan azahar ya tashi daga barci ya sake yin wanka ni kuma lokacin na dafa kuskus mai karas da kabeji shi muka ci kafin mu tafi sannan kuma na ɗiba a kola wanda muka tafi da shi asibitin. A asibitin da ta ke zuwa dai anan ne ta haihu asibitin nan cike har da ƴan Rano sun zo mota guda su Anty Bahijja da su Anty Maimuna suna a gefen gado. Na gaishe su sama sama kamar yadda ke tsakaninmu tun faruwan abin da ya faru sannan na gaisa da Maijego an kuma ba ni yaro na ɗauka kamar Yallaɓai ya yi haki shi ya sa sai ya ɗauko fuskar Baby ban damu da mutanen da ke ɗakin ba na kalli Yallaɓai ina faɗin.
"Yallaɓai kama su ke yi da Baby fa? Fuskarsa fuskar Baby kuma ai fuskar ta na ka ne ko?