← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 89

Sashe 16

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina daga kwance na ga fitowarsa sai na yunƙura na miƙe zaune ina faɗin" Ina kwana."
Sau É—aya ya kalleni sai kawai ya yi gaba ya na faÉ—in" Lafiya lau.'
Bari na je waje na ji ana buga get."
Ya na gama faɗin haka ya buɗe kofa ya fice na rasa shi da kallon mamakim to wai har na fara masa baƙi a ido ne da ya sa Yallaɓai daga jiya zuwa yau ba ya son haɗa ido da ni? Zaune na ke ina mamakin shi, ni ko shigowar mota ma ban ji ba sai dai na ji kamar mgana daga falo sai na miƙe na kawo gabda ƙofa zan buɗe sai ya rigani turowa ya shigo sai muka haɗe ya kalleni na kalle shi.

"Nene. Nene ce ta zo."

Cikin mamaki na ce" Nene fa?
Saboda ni dai tun da muka dawo gidan nan sau ɗaya ta taɓa zuwa shima rashin lafiya Baby ta yi shi ne ta zo duba ta. A wancan gidan kuwa har muka tashi ba ta taɓa zuwa ba.

"E. Ta ce ta na son mgana da ke."

Haka ya faÉ—a min kafin ya wuce.
"Magana da ni?
Na maimaita a cikin raina.
"To wata mgana ce?
"Ta wuce ta auran Yusuf da Gimbiya"
Kamar wahayi haka na ji zuciyata na saƙa min magana.
Uhm kawai nace a saman leɓena sannan na bi bayan shi domin na ɗauko hijabina ina shiga na ganshi ya saka riga zai fita ya raɓa ta gefena ya fice ni kuma na shigo ciki na ɗauko hijabin sallah na saka nima na bi bayan shi amma ni sai da na fara biyawa ta kitchen na dauko mata ruwa da lemu lokacin safe ne domin tara ma ba ta yi ba, bayan tafiyar yara makaranta ne ba daɗewa na kwanta a falon da Yallaɓai ya fito ya ganni kwance.

*Janafty*
*TKG*

05.

Da sallama na shiga falon hannuna ɗauke da farantin da na ɗora ruwa da lemu tare da ƙananun kofunan glass a saman shi.
Gabaɗayansu a tare suka amsa sallamata ashe Musbahu ne ya kawo ta ya na zaune gefen Yallaɓai a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ɗaya. Ita kuma Nene ta zauna akan mai zaman mutum huɗu ne.

Sai da na ja center table ɗin da ke wajen na ɗora ruwan a kai sannan na durƙusa a gaban Nene ina gaisheta ta amsa cikin fara'a lokaci ɗaya ta na ba ni umarni na koma kan kujera na zauna sai na koma na zauna kan kujera mai zaman mutum biyu da ke gefen in da Nene ta ke zaune.

"Anty Sadiya ina kwana."

Musbahu ya gaisheni yana kallona na amsa ina faɗin kwana biyu idon sa kenan ya na yar dariya ya ce" Yallaɓan na ki ne har yau bai cire min ranar hutu ba shi ya sa bakya ganina"
Mirmishi na yi amma ban yi magana ba, yadda Yallaɓai bai kalleni ba nima ban damu da na kalle shi ba domin tunda na shigo falon kansa na ƙasa ya yi shuru kamar wani mara gaskiya. Ko da ya ke ai mara gaskiyan ne tunda menene maraban dambe da faɗa?

"Ina takwarata da Maimunatu? An tafi makaranta ko?

Kaina na ƙasa na amsa ma da Nene da cewa" E Nene.'
Sai ta rausayar dakai kafin ta ce" Allah ya ba da sa'a. Allah ya sa a samu karatu mai albarka."
Muka amsa da Amin gabaÉ—ayanmu.
Shuru na wani lokaci domin shi Musabahu wayarsa yake ta latsawa ganin haka ya sa na gyara zama ina faÉ—in" Nene a kawo abun karyawa?

Da sauri ta ce" A'a Alhamdulillah. Sai da na karya a gida na fito sai dai in Musbahu ga shi nan."
Ta faɗa ta na kallon shi, sai da ya ɗan yi shuru kafin ya ce" Tea kawai matar Yallaɓai."
Sai na miƙe ina faɗin bari na je na haɗo masa, har na fice daga falon ba wanda ya ce mini komai, daman already akwai ruwan lipton a cikin fulas, sai kawai na soya masa ƙwai guda uku ina cikin soyan ma ya leƙo ya ce gashi a falon su Jidda sai na ce to ina gama soya kwan na kai masa nan tare da mug da fulas ɗin ruwan zafi sannan na kwaso masa kayan tea ɗin har da buredi.

"Sannu da aiki Anty Sadiya."

"Yauwa."

Na amsa masa ina ɗan mirmishi hannuna na wanke sannan na koma falon wajen Nene na koma na zauna kenan Nene ta kalli Yallaɓai da ke zaune jugum kamar wani marayan da ya zo neman abin sakawa a bakin salati.

"Tafida."

Ta kira sunan shi sai ya dago ya na kallonta lokaci É—aya kafin ya ce" Na'am Nene."
"Ba mu waje. Zan yi mgana da Sadiya daga ni sai ita."
Da ni da shi gabaɗaya mun kalli juna sannan muka juya muna kallon Nene sai ta gyara zama kafin ta gyaɗa kanta lokaci ɗaya ta na ƙara jadadda mganarta.

"E haka na ce. Ka ba mu wuri mu yi mgana Tafida."

"To Nene."

Haka ya faɗa sannan ya miƙe a hankali kamar wanda ƙwai ya fashe ma a ciki haka ya fice daga falon lokaci ɗaya ya na mai rufe mana ƙofar falon a sannu kar ta yi ƙara. Da ga ni har Nene da kallo muka bi shi ni kuma da ita kowa a cikin ranshi ya na da nashi tunani, ni dai ko tausayinshi ban ji ba domin a ganina wannan shi ake kira daga baya kenan an yi sadaka da bazawara.

Shuru na ɗan wani lokaci kaina na ƙasa ina wasa da gefen hijabina na ji Nene ta kira sunana.

"Sadiya."

Sai da na É—ago na kalleta kafin na ce" Na'am Nene."
"Na zo ne mu yi wata mgana da ke. Kuma kar ki yi tunanin ko mijinki ne ya turo ne"
Na kalleta sai ta gyaÉ—amin kai kafin ta cigaba da faÉ—in" Ko É—aya bai ma san zan zo ba. Bai kuma san da abin da na zo da shi ba, ni ce kawai na yi tunanin na ga lalle ya dace na zo na same ki mu yi mgana baki da baki."

"Haba Nene don wannan shi ne sai kin zo da kanki? Ai da kirana kawai za ki yi a waya na je gida na same ki "
Na faɗa cikin sanyin murya amma cike da biyayya. Ko ban ɗauketa a matsayin uwata ba na ɗauketa a matsayin uwar mijin da ta haifa min miji na aura sannan uwar mijin da ban taɓa samun matsala da ita ba. Tsakanina da ita akwai girmamawa da mutuntatawa mai yawan gaske.

"A'a maganar ta ki ce, shi ya sa na ce gwara na zo da kaina."

Ta faÉ—a ta na kallona, sai na jinjina kai ban yi mgana ba.
"Sadiya kan mganar auren Tafida da Saudatu ne."
Duk da na san maganar, kuma daman a cikin wani shashe na zuciyata na faɗa min ƙila dalilin zuwan Nenen kenan amma a yadda na ji maganar a bakinta ya sa sai da gabana ya amsa. Wannan abun da ya tokaremin a ƙirji na ji ya taso min amma sai na danne ban nuna komai ba illa kai da na gyaɗa mata amma na kasa iya furta wani abu.

"Na san kin ji labari. Tun da jiya Tafida ya je cikin damuwa ya na sanar da ni kin ji labari ba tare da shi ya sanar dake da bakin sa ba."

Kaina na sunkuyar domin na rasa ma abin da zan ce, Au ashe daman ya san na sani? Na rasa ma wani suna zan kira Yallaɓai da shi a dai dai wannan lokacin ba ma, kawai kai na rausayar ina jin kamar duk duniya ko marayu ba su kai ni zama a bar tausayi ba.

"Ba ki  ce komai ba Sadiya."

Nene ta ƙara katsemin tunani da maganarta na ɗago na kalleta itama ni ta ke kallo cikin karantar yanayina rasa abin da zence ne ya sa na gyaɗa mata kai kafin na ce" E. Na sani."
"Tun yaushe kika san da labarin?
"Tun a ranar da aka É—aura auren."
Na bama Nene amsa kai tsaye sai ta jinjina kai kafin ta ce" Ba zan yi mamaki ba. Domin mgana in ta wuce mutun É—aya ta fara kirga uku to ba ka isa ka rufe bakin kowa ba, in ka rufe na wani, na wanin ba za ka iya dakatar da shi daga mgana ba. Ba kuma zan matsa sai na ji daga wajen da kika ji ba, zan je kai tsaye kan batun da ya kawo ni wajen ki Sadiya."

Kaina dai na ƙasa ina ta wasa da gefen hijabina amma zuciyata zafi ta ke yi, kiran sunana ta sake yi na amsa sannan ta ce" Zan ba ki labarin yadda lamarin ya faru, ba domin ki yarda Tafida ba da gangan ya ƙi faɗa miki ba sai domin na ƙara samar da kyakyawan fahimtar juna a tsakanin ku."
Chapter 16 · 0% Book details