← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 89

Sashe 20

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka na fara yi sannan na shiga kitchen na soya naman nan gabaɗaya. Kayan miyan ma na yi blanding ɗin su, na tafasa na ɗiba na yi miya sauran na saka a fridge kafin wani lokaci na gama aikina na gyara kitchen ɗin wajen ƙarfe uku na rana ina falon yara lokacin mun gama waya da Balaraba kenan na ce Saude ta yi zamanta kawai sai gobe  sai ga kiran Hauwa a waya wai gobe ta na nan zuwa na ce Allah ya kawo ta a raina na kuduri niyyar sai na yi ma Hauwa tsinin baki domin ina jin haushin su ita da Munnira.

Ina gida har yamma yara sun dawo daga makaranta har sun ci abinci. Mun yi waya da Yallaɓai ya na tambaya akwai kayan marmari? Na ce sun ƙare sai ya ce gashi nan zuwa zai taho dashi. To bayan mun yi mangariba muna azkar da yara ya sake kirana.

"Sadiya ta."

"Yallaɓai."

Na amsa masa a sanyaye.

"Ina Gwammaja yanzu haka bayan na tashi aiki sai na biyo zan duba Daughter daman ba ta jin daÉ—i da safen ma sai da Nene ta ce in na fito na zo na duba ta. To ina sauri ban biyo ba sai yanzu na kuma zo na iske ta ta na ta amai zan kaita asibiti a duba ta yanzu."

Cikin danne abin da ke taso min na ce" Subhanallah. Ku je mana a duba ta ka yi mata sannu Allah ya ba ta lafiya."
"Amin Sadiyata. Take care sai na dawo "
Da haka muka yi sallama ban bari na saka tunanin komai ba muka cigaba da azkar din mu bayan mun gama ni na ɗora da karatun Qur'ani Allah ya cire min lamarin a cikin zuciyata. Kafin Yallaɓai ya dawo na sake wanka na yi masa kwalliya sai tara da rabi ya shigo gidan muna tare da su Jidda a falo muna kallon Cartoon ya shigo gidan suka tashi suna masa oyoyo ya tarbe su ni ma na miƙe ina masa sannu da zuwa ya amsa ya na kallona duk da bai furtamin ba amma na ga jin daɗi a fuakarsa da muryansa da ya ganni cikin kwalliyata kamar ko yaushe.

Ledan hannunshi na karɓa zuwa kitchen na cire kayan marmari a leda na saka a frezer sauram kuma na wanke na yayyaka mana a Filet na kawo falon ya na zaune tare da su ya na yi musu hira.

"Ya mai jikin?

Na faÉ—a ina zaman gefen jidda, min jera da shi ya na gefen Jidda Baby kuma na kan jikin shi.

"Ta ji sauƙi. Ulcer an saka mata drip da mganguna."

"Ash. An ba ta gado ne?

Na faɗa ina kallonshi sai ya kalleni kafin ya ce" No mun dawo gida. Sun ce dai ta riƙa cin abinci ta shan mganuna nan da sati ɗaya sai ta koma ta ga likita."

"Allah ya ba ta lafiya."
Ya amsa da Amin Baby sarkin mgana ta fara tambatyan waye ba lafiya?
Shi kuma sai ya ce musu Anty Gimbiya ce da ya ke yaran suna son ta daga Jidda har Baby suka fara ma sa magiyan gobe ya kai su suke su duba ta sai ya fara cewa akwai makaranta su bari weekend su sai suje.
Ina gefe na ce" Ya yi nisa. Ko da daddare gobe haka Yallaɓai?

Na faÉ—a ina kallon shi, sai na ga ya kalleni kafin ya ce" To shike nan sai mu je É—in."
Suna jin haka suka fara murna. Nan muka bar su da shan su kankana ni da shi muka shiga ciki sai da ya yi wanka sannan na haɗa masa tea na kawo masa abinci tare muka ci tunda ni daman ban ci ba tuni su Jidda suna ɗaki sun kwanta muna ci muna ɗan taɓa hira ya ce min jibi Jumma'a zai shiga Kaduna domin ya duba aikin nan na ce Allah ya nuna mana.
Bayan mun gama ya ta ya ni muka kwashe komai zuwa kitchen, muka kakkashe hasken ɗakunan da falo sannan muka koma ɗaki muka yi shirin kwanciya yau dai ban hana shi kaina ba na saki jiki mun farantama juna, muna riƙe da juna cikin yanayi na ma'aurata sai wayarsa ta yi ƙara alamun shigar saƙo sai bayan mun natsa har ma mun yi wankan tsarki ya duba ashe cikon kuɗin aikin da ya yi na gina tiolets da wasu azuzuwaa makaranttun gwammatin kano na tuntuni n a ka turo masa.

Sai ya kamani ya rumgumeni ya na faɗa mini. Sai na riƙe shi nima ina mai ta ya sa farinciki. A zahirin gaskiya kuɗin nan ba su iya zuwa lokacin da ya dace ba. a can baya ne na yi zumuɗin zuwansu amma yanzu sai na ji ba na musu zumuɗi ko na so ko ban so wannan kuɗin da su za a yi shirye shiryen tariyan Gimbiya. Ana nufin kishiyar da za a kawo min wataƙila a nan wataƙila a wani gidan na dabam.

*Janafty*
*TKG*

06.

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

Yallaɓai fa miliyoyi sun dira a cikin account ɗin sa na banki ba zama. Tun safe ya fita ya ma riga yara fita saboda sauri, bayan kuma tun asuban fari ya fara waye waye da mutane bakinsa ya kasa shuru. Ni fa tun a farkon auran mu tun ina mamakin halin Yallaɓai har ya zame min jiki, in ya yi wani abin na daina ganin sa a sabo a wajena.
Tun da na san shi, shi ne mutun ƙwara ɗayan da zan ce na sani mai bayyana ya samu kuɗi a duniya. Kowa sai ya sani daman kuma tun kafin kuɗi su zo zai ta yi ma jama'a alƙwari da cewa in an biya shi kuɗin aikin sa na kaza zai baka kaza, a farkon auranmu na ga lamarin na shi wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara, tu ina yi masa mgana har na gaji na kama kaina domin na tabbatar da halin shi ne, ba zai iya dainawa ba.

  Ni dai kafin ya fita sai da na yi masa maganar kar ya je ya yi ta facaka da kudaɗen nan ya rage sauran basukan mutane da suke kansa. Sai ya ce min zai rage daman na Kawu Abba ne mai yawa zai biya shi sai na Tariq da ya karɓa a wannan aikin na kaduna amma shi ba zai biya shi sai an biya shi na kadunan. Sai yaran shi da zai cika ma kuɗin aikin da suke yi rabi ya ba su, wasu ma bai ba su komai ba saboda ba kudaɗe a hannun shi. Ya fita da cewa office zai je amma tunda ya na da kuɗi sai in da mansa kuma ya ƙare ya bar ni ni kaɗai a gida tun da su Jidda sun tafi makaranta suma.

Bayan fitan shi ba daɗewa ya kira wayata ya na faɗa min na rubuta list ɗin duk abin da muke buƙata a gida na kayan abinci da sauran kayan amfanin mu ni da yara, sai na amsa masa da to, bayan mun gama wayar na tashi na shiga Kitchen ina duba abin da babu. Sai da na gama gani sannan na koma ɗaki na rubuta a cikin wayata kayan amfanin mu kuma ni da yara sabulun wanka ne na su, sai nawa wanda na siya wajen Lame ya kawo gangara. Sai su man wanke kai da maclean sai izel da klin muna da komai su kaɗai ne suka yi ƙasa, sannan a raina na ce zan tuna masa da kuɗin makarantar yara domin wannan term ɗin ne ƙarshe, in suka yi hutu suka koma akwai biyan kuɗin makaranta. Test ma Jidda ta ce min suke yi sun kusa hutun kirisimet na ƙarshen shekara.
Allah ya sa ma ya yi dubara lokacin da zai biya a second term ya biya gabaÉ—aya na season É—in.

Sanin Saude na makaranta sai in ta dawo ne in ta na da lokaci ma ta ke zuwa. A ranakun makaranta zuwanta ya koma sau huɗu ne kawai a sati. Alhamis da jumma'a sai weekend na san yau za ta zo amma sai wajen biyu na rana, kuma ga shi Hauwa ta ce min za ta zo sai ban kwanta ba na miƙe na yi aikin gidana da kaina ban bari wani tunani ya ziyarce ni ba, karatun Qur'ani na saka a wayata ina ta ji, kuma ina bi da bakina ko kafin goma na safe na gama komai gidana sai kamshin turaren wuta ya ke yi, haraban gidan ne na ga ya yi datti sai na bar shi da cewa in Saude ta zo sai ta share ta gyara wajen.  Wanka na yi na shirya cikin wani leshi na mai sauƙakƙan nauyi, ina falon yara ina hutawa wayata na hannuna ina danne danne, yanzu sai na yini na kwana ban buɗe data ba, ba na so na ga ma abin da zai ɓata min rai ko ya ɗaga min hankali shi ya sa na kama kaina.

Ina nan zaune, ba kallo na ke yi ba saboda sun É—auke wuta yau tun safe ba su dawo da shi ba. Ina ta mamakin ma rashin dawo da shin da ba su yi ba, saboda in suka É—auke in ta daÉ—e ba su dawo dashi ba awa É—aya amma yau sama da awanni uku ba wutar. Karatun Qur'anin na cigaba ji a wayata ina kuma zaune na kishigiÉ—a a saman kujera a sannu sannu ina bin karatun, idanuwana a lumshe suke sai na ji karatun ya tsaya wayar ta fara vibration alamun ana kirana, a kasalance na É—an tashi daga saman kujeran da na ke zaune, ina mai buÉ—e idanuwana da suka yi min nauyi, domin sai na ji kamar barci barci ma na ke ji, hannu na saka na jawo wayar ina duba mai kiran nawa saboda kafin na É—auki wayar kiran ya katse.

"Yaya Aina ce."
Chapter 20 · 0% Book details