Sashe 3
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga jiya ne ya ke zumuɗi da fatan su sallama masa wannan shagon amma yanzu komai ya ƙare. Sai ya ji ma abin ya fita kansa. Abin da ya faru yau a Rano ya ɓata komai ɗin da ya shirya a matsayin zai ba ma Sadiya suprise. A cikin shagunan da ke ƙasan Office ɗin su ne wasu suka saki shi kuma ya yi mgana ya na so Saboda Sadiya su kuma masu wajen sun ce mai wajen ne zai yi amfani dashi amma ya na ce ya na so saboda kimarsa kuma akwai kyakyawan alaqa tsakaninsa da mai wajen ya sa suka sallama masa ya so ne ya ba ma Sadiya suprise da niyar in aka bashi kuɗin aikinsa na kaduna zai cika alkwari ya ba ta kuɗi ta yi oder ɗin kayan da za a sanya a shagon a buɗe shi cikin ƙankani lokaci. Ya san a duniya Sadiya ba ta da wani buri sai na buɗe shagon Saloon da tun da suka yi aure ta ke da wannan burin kuma shi ya karbe mata duka kuɗaɗenta da alƙwarin zai tallafa mata domin cikar burinta.
Amma a wannan lokacin sai ya ji ko ya nuna mata ma ba za ta yi murna ba in ya faÉ—a mata ya kara aure za ta fassara niyyarsa ta wani siga ne shi ya sa sai karsashinsa ya ragu.
Â
"Ok."
Kawai ya tura ma Musabahu daga nan ya maida wayar aljihu. Kunya ce ko nauyi suka sa ya kasa ta shi ya bi Sadiya cikin ɗaki ya zauna tare da su Jidda har suka gama bidirinsu sannan ya ce su je su yi brush su sauya kaya su kwanta shi kuma suka bar shi da gyara in da suka ɓata sauran cake ɗin da komai ya kwaaso su ya kai kitchen ya tura a cikin fridge. Sai ya leƙa ɗakin su Jidda ya tabbatar da sun kwanta sannan ya rage musu hasken ɗakin ya rufe musu kofa ko'ina sai da ya duba ya rarrage hasken gidan gabaɗaya sannan ya wuce bederoom ɗin su.
Na ji takun sa zai shigo da sauri na shigar da kaina cikin bargo na lafe kamar mai barci. Ahalin kuma ba barci na ke yi ba. Na ji shigowarsa kuma na ji tsayuwarsa a kaina na wani lokaci na ƙara lafewa ina nunfashi kamar mai barci sai kuma bai tashe ni ba can na ji ya buɗe kofa ya fita. Sai kuma na ji ya shiga tiolet leƙo da kaina na yi ina sauke numfashi tunda na shigo ɗakin nan tiolet kawai na shiga na kama ruwa na dawo na saka kayan barci na kwanta ina faman tunani na ɗauka in na keɓe ni kaɗai zan samu daman kuka sai kuma na kasa ashe ma kukan rahama ne suya kawai kirjina ke yi, wani tuƙuƙin abun da ya tokaremin a zuciyata tun a lokacin da Ma'u ta faɗa mini ya kasa wuce min. Na san Yallaɓai zai iya ƙara aure kuma na saka a raina zai iya auran Gimbiya amma ban ɗauka yau ba. Ban kuma kawo sa gobe ko jibi ko nan kusa ba. Lamarin ya shammace ni shammatan da ya firgitani matuƙa sai kuma yadda Yallaɓai ya munafunce ni? Zan hana shi kara aure ne? Ko zan hana shi yin abin da ubangiji ya ce ne? Takaicina ɗaya yadda na yarda dashi na ke yi masa kyakyawan zato daga karshe ya ci amanata ya yi aure ban sani ba. Ni kuma na yi ma kaina alƙwarin in dai bai buɗe baki shi da kanshi ya faɗamin ba zan ta ɓa nuna masa na sani ba zan jira na gani ina da sauran ƙima a wajensa da zai zaunar da ni ya faɗa min ya ƙara aure sannan ta yadda auran na shi ya zo bakatatan! Ko kuwa zai bar ni a rufe ne ya na yaudarata da kalaman bakinsa na ƙarya da munafunci.
Ina jin zai buɗe kofar tiolet ɗin sa na koma da kaina cikin bargo na lafe. Wallahi ban iya barci ba duk ina jin kai da kawonsa har ya gama ya zo ya kwanta ina jin sa a kusa da ni ya na kiran sunana na ƙara lafewa domin a ji a raina yau ko nema Yallaɓai ya yi sai dai tsinuwan mala'ikun su hau kaina amma ba zan iya yi masa wani amfani ba.
Ina jin sa sarai ya na ta kiran sunana na yi kamar mai barci har bargon ya ye min daga fuskata yana leƙani na yi bakam na ƙi motsi sai da dai ya ga kamar na yi barci. Sai ya gyara min kwanciya ya sake rufamin bargo amma bai rufe min fuska ba.
Kamar ya san ba na buƙatar sa bai raɓu da ni ba sai ya koma gefe ya kwanta. Na daɗe ina jin karin maganar nan ta hausawa da sukan ce yadda na ga rana haka na ga dare a baya in ta tunanin kawai sai ka kwana ba ka yi barci ba? Sai yau na samu tabbacin hausawa fa sun yi gaskiya domin nima yau ɗin nan yadda na ga rana haka na ga daren. Barci ko na minti ɗaya bai ɗauke ni ba Yallaɓai ma ya kusa raba dare ya na juye juye amma daga baya ya samu barci ni ko a kunnena aka fara kiran sallar farko na asuba a kuma lokacin ne na yaƙi sheɗan na miƙe na sauko daga kan gadon ina mai kallon Yallaɓai sai na ji wani shashi na zuciyata na ji tausayinsa yadda ya kwanta ya takure jikinsa sannan ni ya bar ma blanket ɗin bai rufu da shi ba. An ce mata da miji sai Allah sai na ji a wani shashe na zuciyata na yi ma Yallaɓai uzuri. Wani shashen kuma na ce min Yusuf ne fa! Wanda ya fi kowa fahimtar ki.
Kamar zan ƙyale shi sai kuma na fasa zuciyata mai imani da tausayi wacce ta gaza ganin baƙin Yallaɓai ta rinjaye ni na isa gare shi na ja bargon na lulluɓa masa sai na ga ya yi motsi ya ɗan gyara ya miƙe kafarsa. Ina tsaye ina kallon shi duk da akwai ɗan duhu amma hasken kwan lantarki haraban gida ya na shigo mana ta cikin bedroom ɗin mu.
Juyawa na yi na fita daga bedroom din Tiolet na shiga na É—auro alwala sai da na fito ne na duba agogon wayata 4:30am na asuba sai na shimfiÉ—a darduma na saka hijabi na tada sallah.
Sai da na yi raka'a huɗu sannan na zauna ina salatin Annabi da istgifari a cikin raina rokon Allah kawai na ke yi ya ba ni juriya domin na ji kamar zan gaza na ji kamar ba zan iya ba kuma gashi ina so na iya ina so na daure. Bayan na yi addu'o'ina na neman sassauci wajen Ubangina yau rana farko da na yi addu'a ban yi ma Yallaɓai ba kawai sai na ji gwara na yi ma kaina da ƴaƴana tunda yanzu Yallaɓai ya zama mallakinmu ba mallakina ba
Na tashi na sake tada salla Yallaɓai ya farka da fitilan wayarsa ya haskoni sai ya ga ina salla, ni kuma ina ganin ya farka saboda ba na son mgana ya sa ina sallamewa na sake miƙewa na ƙara kabbarta wata sallar. Sai na ga ya sauko daga kan gadon shima ya fice ashe alwala ya ɗauro ya dawo ya saka jallabiya ya zo kusa da ni ya shimdiɗa sallaya dai dai ina sallame raka'a ta biyun da na faro.
"Me ya sa ba ki tashe ni ba?
Sai na ji na kasa mgana a da na saba in dai zan tashi sallar dare ina ta da Yallaɓai mu yi tare yau kuma ban tashe shi ba. Saboda kar na yi masa mgana sai na sake miƙewa na kabbarta salla da ƙarfi na ce." ALLAHU AKBAR."
Ni na san Yallaɓai ya bi ni da kallo kuma ya na ɗan fara shan jinin jikinsa. Ban bi ta kansa ba sai da na sake yi raka'a huɗu sannan na zauna ina jan casbaha Yallaɓai ma raka'a shidda ya yi lokacin har an fara kiran sallah na biyu sai ya miƙe ya je ya ɗauko hula ya saka da casbahansa hasken ɗakin ya kunna ya na kallona kafin ya ce.
"Na tafi masallaci."
Kaina na gyaɗa masa ina ɗaga masa carbin hannuna alamun ina lazimi bai ce komai ba sai ya kaɗa kai ya fice daga bedroom ɗin ya ma mai rufo min ƙofar bedroom kamar an ƙwace ni haka na sauke ajiyar zuciya ina ta fitar da numfashi ta baki ina tunanin shi ya ta da yara bayan ya fita saboda ni ban fita ba sai bayan na idar da sallar asuba sai na leƙa su na ga sun tashi suna salla a ɗakin na zauna daman na zo da Qur'anina na fara karatuna so na ke yi zuciyata ta samu salaman da zan yi ma kaina tunani mai kyau kuma alhamdulillah na samu.
Sai da na gama karatun nawa a cikin suratul Maryam sannan na yi ma Jidda na ta karatun tare da Baby ina cikin yi ma Baby ne Yallaɓai ya shigo ɗakin daman sun san na hana su tashi in muna karatu daga zaunen suka gaishe shi ya amsa ya na daga ƙofar ɗakin bai shigo ciki ba hankalina da idanuwana na kan Qur'anin da ke gaba na na ce.
"Ina kwana."
Ban san yanayin sa a lokacin ba ya dai amsa nuryansa a sanyaye.
"Lafiya lau. Kin ta shi lafiya?
Ban amsa shi ba na cigaba da biya ma Baby karatu gajiya ina ga ya yi da tsayuwa ya fice sai dai na ji ƙaran rufe kofarsa na raka shi da harara ƙasa ƙasa.
Bayan na gama musu karatun sai muka yi azkar sannan na bar su na ce Jidda ta yi ma Baby wanka su shirya ni kuma na cire hijibina na ijiye anan É—akin yara na shiga kitchen na dafa musu ruwan tea sai na soya musu kwai na ce su karya da shi sannan kuma su tafi dashi yadda na ke jin kaina ba zan iya firan dankali ba kai aiki mai wahala ba na son yi saboda duk jikina ya mutu.