← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 89

Sashe 53

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na faɗa dai dai ina ƙarisowa da ɗan sigan zolaya haka. Sai muka kalli juna sannan ta yi min mirmishi na maida mata. Ta na sanye da hijabi mai ruwan ƙasa kalan doguwar rigar da ke jikinta takalmin kafanta mai saukaƙƙen tudu ne sannan ta saka safa irin na su dai na ƴan gayu. Ni kuma daman atamfata na saka wata mai purple sai na yi amfani da kalan Hijabin, kafata nima flat shoe ne da safa su Jidda ma Atamfa na saka musu da hijaban da na siya musu har ƙasa haka ma Marwa. Gogan na kalla ya na cikin mota zaune sai dai ya na amsa waya ne shi ya sa bai fito ba.

Hannu ta miƙa mini muka yi musabaha.

"Barkanmu da salla Madam"

"Barka da salla."

Nima na maida mata martani Marwa ta gaiaheta sai ta amsa ta na yi mata kallon rashin sani.

"Marwa. ÆŠiyar yayata ce."

Na faÉ—a ina dafa kafaÉ—an Marwa É—in. Sai ta yi mirmishi kafin ta ce" Barkan mu da salla Marwa."
Marwa ta amsa ta na mai ƙara gaisheta, daga cikin motan Yallaɓai ya ce ko a nan ne za mu yi sallar idi? Muna jin haka sai na buɗe gidan baya na ce Marwa su fara shiga ita da yara ni ban ma kawo ma kaina hawa gaban mota ba, saboda na ga Amarya a bakin wajen ta kame shi ya sa na shige baya abuna wata zuciya na ƙara tunatar da ni aka ma raba mijin gabaɗaya ballanta kuma gaban mota.

  "Ina kwana Madam ɗina."

Ya faɗa bayan yaran sun kuma gaishe shi ya juyo ya na musabaha da su. Nima hannun ya miƙa min sai na karɓa ina faɗin.

"Barka da salla Yallaɓai."

Sai ya jinjina min kai kafin ya ce" Barkan mu da salla Amintattaciya ta."
Kallon shi na yi, amma ban yi mgana ba hannuna na zare cikin na shi kawai ina mai cema Baby ta koma ta zauna ko na dake ta saboda sai faman zillo ta ke yi ma mutane kamar za ta koma can gaban motan.

Marwa ma ta gaishe shi ya amsa ya na faÉ—in" Marwatu barkanmu da salla."
Ta amsa ta na ɗan mirmishi, sai ya juya ya na mai kallon Gimbiya sannan ya ƙara juyowa ya na sake kallona ni kuma tuni na maida hankalina wajen jan kabbarorin da Annabi(SWA). Ya koyar da mu a lokacin tafiya sallar idi.
Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar. Walillahil hamdu. Har su Jidda ma na ce su yi ta maimaitawa.

Har mun ɗan fara tafiya muna ta haɗuwa da mutane kowa ya ci sabbin kaya yau ta ke salla Yallaɓai na juya ina kallon keyarsa da yadda ya kafa hula ya na tashin kamshi wata wagambari ya saka mai ruwan ƙasa duk da bai sauko daga motar ba amma ya yi kyau matuƙa shi daman Yallaɓai mai kyau ne kuma ɗan gayu ne komai ya saka a jikin shi sai ya yi masa kyau ina daga gefe ne ta bayan kujeran Gimbiya ba na kallonta amma shi ina ganin shi sai ya ɗan kalleta yana mirmishi ƙila itama murmushin ta ke yi masa sai kuma in ya ɗago mun haɗa ido ta madubi sai ya wani kashe min ido, ai da na ga ya na nemen rena mini wayau tuni na juyar da kaina ina gani  gilmar motoci da waɗanda ke kasa ina jin farinciki a ƙasan raina na ganin hada hadan mutane, a cikin raina ina ta hasaso yanzu haka a gida su Alhajinmu suma sun kama hanyar zuwa sallar idi shi da su Ya Hamza tun jiya da muka yi waya da Gwaggo ta ce sun iso Ya Auwal ma daddaren ya ce min sun sauka shi da yara da Laila. Muna da ɗakuna a gidanmu ga na Mama ga na Hajiya duk kuma a gyare suke, can ƙofar shigowa kuma ɗaku nan su Ya Hamza tun na samartakansu ya na nan in sun zo gida nan sukan sauka har su gama kwanakin su koma sun gyara shi sun saka komai na morewa rayuwa a ciki.

Har muka isa masallaci ban ƙara bi ta kan Yallaɓai da matar shi ba. Mun sauka a bakin hanya ya ce zai nemi wajen parking mu kuma mu karisa bangaren mata in an idar da salla zai kira mu. Daga nan muka ɗau darduman mu guda biyu itama Gimbiya ta zo da na ta, Marwa ta riƙe hannun Jidda ita kuma Gimbiya ta riƙe hannun Baby suna gaba ni kuma ina baya ina ta kabbarori. Mun samu wajen zama muka shimfiɗa sallaya muka zauna ba daɗewa aka ta da salla, bayan mun idar da salla aka fara hada hadan jama'a wasu na kafa sannan ga zirga zirgan ababen hawa waje ya cika makil ko'ina ga waiga jama'a ne kamar ba a mutuwa saboda cikowa.

Mun samu mun fita can bakin titi da kafarmu ni wayata ma a gida na barta Gimbiya ce ta zo da ƙaramar jaka shi ya sa ta ɗauko wayarta ta nan Yallaɓai ya kira mu, ya na ta faɗan wai ya na ta kiran wayata ban ɗauka ba na ce ta faɗa masa ta na gida na baro ta. Mun haɗu da shi a can gaba kaɗan sannan muka shiga motar wannan karon ma Gimbiya a gaba ta kame ni kuma na shiga bayan kamar yadda na zo.

"Ke haka ake yi sai ki bar waya a gida?

Sai na kalle shi kafin na ce" Za ta zame min kaya ne shi ya sa ban É—auko ta ba."

Sai ya yi shuru bai yi mgana ba, sai kuma can ya kalli Gimbiyar kafin ya ce" Daugther ki koma baya ki zauna."
Sai ta kalle shi kafin ta yi magana ya juyo ta baya ya na faÉ—in" Ke kuma Sadiya ki fito ki dawo gaba."

Sai na ga ta ɗan yi wani tsam kafin ta ce Ok. Tana ƙokarin buɗe kofar motar ne na yi saurin cewa" Ki yi zaman ki ni fa nan ɗin ma ya isa. Ba duk mota ba ce da bayan da gaban ai duk ɗaya ne"
Sai na ga kuma ta dakata da fitan kenan ta na son zaman gaban motan sai kawai na ga ya wani kalleni ya na wani haÉ—e rai.

"Na ce ki fito ki dawo nan ki zauna ko?

"Da dai ka bar ni anan É—in."

"Umarni ba jin ta baki ba. Ki fito ki dawo gaba ita kuma ta koma baya haka na ce."

Ya faɗa har ya na wani tattarre naman goshinsa waje ɗaya na fitina ina jin haka sai na buɗe murfin mota na fito, itama ta fito  sai mu ka sauya wajen zama sai da muka zazzauna sannan ya ta da motar muna tafe a hankali saboda gowslow shi ya sa Yallaɓai tafe ya ke gaisawa da mutane har dai na ga ji na kalle shi ina faɗin.

"Sannu. Wai kai kowa ka sani ne?

Ya na dariya kafin ya ce" Ba kowa ba. Amma saboda aikina ina harka da mutane sosai."
Ai ko na ga harka da mutane kafin mu fita wannan cunkosun Allah kaÉ—ai ya san yawan jama'an da ya haÉ—u da su sai dai ki ji ana faÉ—in Injinjiya kai ne anan? Mutane ba su cika kiran shi da Yusuf ba sai Injiniya a gida kuma daman Tafida ne in ka ji Yusuf sai dai irin tsoffin abokan shi tun na makaranta.

Har gida suka dawo damu kamar yadda suka ɗauke mu. Gimbiya dai fuskar nan ba Annuri ina ga ranta ya ɓaci ne da ya ce ta fito ta ba ni waje ni ko ban tsaya ma bi ta kanta ba a raina na ce kina da aiki. Mun rabu da Yallaɓai da cewa in ya maida Gimbiya gida  Gwammaja zai je ya yanka ragunan sallar nan sai anjuma zai leƙo. Yara ma suna ma Antynsu na su bye bye ba ta amsa ba muna dai tsaye suka juya kuma ta na bayan ba ta dawo gaban ba duk da na ga kamar ya juya ya na mata mgana kuma ina da tabbacin ce mata ya yi ta dawo gidan gaba ina ga za ta ce daga baya kenan, ni dai na buɗe gida muka shige a ƙasan raina ina ganin ƙokarinta Allah na tuba mene ne a zama gaban mota tare da miji. Ni Allah na tuba ina ga ita ce baƙuwa a harkan ni ba domin ya matsa min ba wallahi bai dame ni ba. To wai mijin kan shi fa raba shi kake yi da wata to mene ne a cikin zama a gaban mota? sai na ke ganin shi wannan ai ba wani abu ba ne.

Muna dawowa muka sulala indomie muka ci, sai can da rana Musbahu ya kawo kayan ciki na Yallaɓai da nawa sai naman ragon da ya yi min layya daman duk shekara yana yi min in kuma bai da shi ya yi nashi shi kaɗai. Kuma in dai ya yi min to ni ake kawo ma Naman na diɓan ma gida sauran kuma mu yi amfani da shi a gida na Yallaɓai kai da kafa kawai ake gyarowa aka wo naman kaɗan ne ake kawowa duk sai ya ce ya yi sadaka da shi. Yau ma ɗin haka na yi na diɓar ma Gidanmu na ba ma Marwa na adaidaita ita da Jidda suka je suka kai musu muna gida ni da Baby muna jiran su yaran nan sai yamma suka dawo suna faɗa min gida cike da matan su ya Hamza ana ta hidima sai na ji kamar na yi tsuntsuwa na ganni a gida, Alhajinmu ya ba ma Jidda goron salla ya ce Baby ta nemi na ta mijin ya ba ta, Baby na jin haka ta fara rigima sai ta je  mu na yi mata dariya.
Chapter 53 · 0% Book details