Sashe 24
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na amsa masa mganar, da ace bai matso kusa da ni ba, ko ta kanshi ba zan yi ba amma sai na ga ya rarrafo ya matso kusa da ni muka kwanta a jikin juna duk da ba mu yi komai ba amma mun kwanta tare mun kuma tashi tare, da sassafe ya ta fi kaduna tea kawai ma ya iya tsayawa ya sha ko yara yau ba su riga shi fita ba. Tafiyar ta sa ba ta kwana ba ce amma da yamma ya kira ni ya ce ya yi dare kuma akwai abin da zai tsaya ya yi a goben shi ya sa zai kwana sai ranar asabar zai dawo na ce Allah ya kaimu.
Ranar asabar ɗin ma sai yamma ya dawo ya na can kadunan aka kawo kayan abinci ni ma ya turamin kuɗi na abubuwwn da na ce masa ba mu da shi, ban je kasuwa ba ni dai na kira Aisha lame na siya lotion da shower gel, Marwa na kira ta zo na ba ta sauran saƙon bayan na rubuta mata, haka kurum na ji ba na son fita ko nan da kofar gida saboda ji na ke yi kamar ba ni ba.
Duk yadda Yallaɓai ya so mu zauna mu yi mgana na ƙi ba shi fuskar hakan, cikin haka ne ma na faɗa masa maganar tafiyar mu Yashe biki bai hana ni ba daman na san ba zai hana ni ba, ranar lahadi da daddare na faɗa masa tafiyar na kuma ce talata ya ce Allah ya tsare sai washegari litini bayan yara sun tafi makaranta ya na tashi daga barci kamar da ni ya tashi a ranshi ina kitchen ya leƙo ya kirani sai na wanke hannuwana daman ina fere doya ne, itama ta ƙare jiya Yallaɓai ya aiko Musbahu da ita tare da dankalin turawa da na hausa.
 Hannuna ya kama ina bin sa a baya har cikin bedroom ɗin mu ya zaunar da ni a kan gado shi kuma ya ja kujeren madubi ya zauna a gaba na ya na kallona.
"Me ya faru?
Na tambaye shi ina kallon shi cikin mamaki.
"Me ya sa ki ke gujema mganar da na ce za mu yi?
Ajiyar zuciya na sauke domin ya riga ya ritsani ba ni da mafita sai kawai na amshi laifina.
"Ka yi haƙuri."
"Na yi. Na yi Sadiya ta."
Ya faÉ—a ya na min mirmishi.
"Ina jin ka. Me zamu tattauna?
Gabana na ta faÉ—i, saboda karshen wata saura kwanaki ne kaÉ—an. Sati biyu ma ba wani abu, ina tsoron na ji wata mganar da za ta tada min hankalina.
"Kan mganar tariyan Daugther ne daman."
Daugther. Daughter ƙaniya. Ai wani daughter da Daddy duk ta ƙare yanzu tun da an ɗaura auren.
"Maganar gidan da za ta zauna ne daman."
Ras! Haka na ji, fargaba na taso min sai kawai na kalle shi ban yi magana ba.
"Na saka a nema min haya gida. Jiya dai an kirani an samu wani a can anguwan Taurani sai wani a sharaÉ—a yau na ke so mu je da ita ta ga gidan"
Na É—ago ido ina kallon shi sai ma rasa me zan ce masa?
To wai me ya rage ne? Ni fa duk wannan ga ya min fa Yallaɓai ya ke yi bai burgeni ba da ya sani da ma ya yi shuru da bakinsa ni a wajena da ya fi. Ko kaɗan ban ganin kirkinsa ta wannan fannin
Amma dai na samu salama, tunda dai ba tare za mu zauna ba. Daɗin abin ma ta na can wata anguwar mai nisa da in da na ke, gwara hakan domin gwara kazantar da ba ka gani ba akan kazantar da agaban idanuwanka ya ke faruwa hausawa dai sun ce ƙazantar da ba ka gani ba sunanta Tsafta.
*Janafty*
*TKG*
07.
Kamar a zahiri kallonsa na ke yi amma a baÉ—ini ba shi na ke kallo ba. Hankalina da tunani ya yi nisan kiwo. Jikina gabaÉ—aya ya saki sai na ke jin kamar ba zan iya ba, kamar za'a ga gazawata in tafiya ta yi nisa.
"Kin yi shuru ba ki ce komai ba Sadiya."
Shi ya katse min tunani da ya sa na dawo hayyacina. Ajiyar zuciya na sauke kafin na maida hankalina zuwa ga kallon ƙasan cafet ɗin da ke gefen gadon. Ina so na yi magana amma sai na ji kamar an ɗaure min baki zuciyata ta yi wani irin nauyi sannan numfashina sai na ji kamar ya na sarƙewa sai na buɗe baki da niyyar magana sai na kasa sai da na ƙara sauke ajiyar zuciya na fitar da iska daga bakina sannan na fara jin ina dawowa cikin hayyacina.
"Are u ok?
Wani kallo na yi masa, tsabar ma Yallaɓai ya raina min wayau ya zaunar da ni yana min labarin kishiyan da ya yi min shi ne kuma ya ke tambayata ko ina lafiya? Kaɗan rage ban ce masa ban sani ba amma sai na danne zuciyata kamar yadda na saba amma ni kaina na san ina yi ma zuciyata gaddama sannan ina faɗin saɓanin abin da ta kitsa min.
"To me zan ce?
Haka na faɗa ina kallon sa, sai ya ƙure ni da ido, ni kuma sai na maida kaina ƙasa sai ma na kama wasa da zoben zurfan da ke hannuna. Ba tsammani kawai na ji ya riƙo hannayena cikin tafukan hannayensa sai na ɗago ina mai sake kallonsa a cikin kwarmin idanuwana akwai alamun taruwan ruwa, amma duk ƙoƙarina domin na hana su bayyana ne a gaban Yallaɓai a karo na biyu ne shi ya sa na ke ta ɗagagga ido na sama ina ƙokarin maida kukan da ke ƙoƙarin taso min.
"Me za ki ce haka Sadiya ta? Ke ko ke da abin cewa?
"Ko?
Sai ya gyaɗa min kai ya na mai ƙara damke hannayena cikin na shi.
"Saboda me?
Haka na tambaye sa saboda sai na ga kamar Yallaɓai so ya ke ya kureni to in ba ƙurewa ba, ina ruwana da labarin hayan gidan da zai kama tun da ba ni zan zauna a gidan ba, abin da ya shafe shi, shi da Gimbiya ne.
"Na faÉ—a miki ki daina cewa saboda mene Sadiya. Kar ki manta ke fa matata ce. Kuma uwar Æ´aÆ´a na."
"Sai me?
Haka na faɗa, lokaci ɗaya ina ƙwace hannayena daga cikin na shi, sai ma na miƙe tsaye lokaci ɗaya ina faɗin" Don ina matarka sai me? Me ka ke so na ce? Duk abin da zan ce ai na gama cewa tun a baya Yallaɓai."
Na ƙarishe faɗa ina mai kallon shi. Ya na shirin sake magana na yi saurin ƙara tare shi da cewa"Allah ya sanya alheri."
"Amin"
Na ji Yallaɓai ya faɗa, har na juya zan fita daga bedroom ɗin jin abin da ya ce ne, ya sa na juya ina yi masa wani irin kallo, ganin irin kallon da na ke yi masa ya sa wajen ya kwaso maganar da za ta kare sa sai ya ƙara yaɓa ma kansa ɗanyen kashi.
"To ko za ki zo mu je Tare ne?
"Mu je ina?
Na faɗa a zabure saboda sai na ji kamar Yallaɓai na shirin dukana da bulalan kalamanshi ne.
"Duba gidan mana."
Ya faɗa ko kunya, sai na ƙara jin kamar ya watsa min ruwan sanyi sai da tsikar jikina suka ta shi yam! Kallon Yallaɓai na ke yi da dukkan zuciya wai daman wanna ne cin mutumcin irin na mazan irin sun ƙara aure! Wato ni tun kafin ma tafiya ta yi nisa Yallaɓai ya fara ƙokarin nuna min na shi halin, wata irin zuciya ce ta yunkuro min kawai sai na dawo gabansa na tsaya ina kallonsa ido cikin ido kafin na buɗe baki da na ke jin tsabar zafin da ke cikin zuciyata ina jin hucin sa daga cikin bakina.
"Me ka ce?
Sai ya yi shuru ya kasa maimaitawa ganin yadda na yi, mirmishi ya yi ya na ƙokarin ya mai da maganar ta sa wasa.
"E. Ki shirya mu je mu duba gidajen tare ai ba wani abu ba ne ko?
Ban san na ɗaga hannuna ba sai da na ga ina nuna sa da yatsa manuniya. Cikin kakkausan muryan da Yallaɓai ya ke daɗewa bai ji ni na yi masa magana da ita ba na buɗe baki na kira sunan shi.
"Yusuf."
Haka na faɗa ina masa gargaɗi da ido, shima jikinsa ya yi sanyi domin ya san duk ranar da na kira shi da sunan Yusuf ya san ba zaman lafiya a tsakanina da shi. Miƙewa tsaye ya yi cikin kwaso maganarsa.
"Tsaya ki ji. Ni fa ba da wata manuf.."
"Yusuf ko dai ni ce zan tashi daga wannan gidan Amaryanka ta zauna, ni kuma gidan hayan da za ka kama shi ne nawa?
Na faɗa ina mai tsare shi da ido, ƙokarim riƙe ni ya ke na yi baya ina mai ɗaga masa hannu, faɗi ya ke yi cikin rawan murya wai shi ba haka ya ke nufi ba a fusace na ce" To in ba haka ka ke nufi ba! Me ka ke nufi da na shirya mu je duba gida tare? Ina ruwana da maaganar duba gida? Ko ya shafe ni ne?
Na ƙarishe faɗa cikin tsawa ina mai zazzaro masa ido. Sai kawai ya sarke hannayensa duka biyu a saman ƙirjinsa ya na faɗin" Ba ki fahimce ni ba ne Sadiya. Ni fa ba da wata munafa na faɗi haka ba, saboda kar ki ji ba daɗi ne ya sa na ce haka amma tun da ranki ya ɓaci ki yi hakuri."