Sashe 26
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da a niyyata yau ba zan yi girki ba, sai kuma daga baya na ga bai kamata ba. Ya fita bai karya ba yanzu kuma ya dawo ba abinci? Duk da wata zuciyar tawa mara kirkin ciki na faɗa mib sun je duba gida da amaryansa kika sani ko sun biya gidan cin abinci sun ci? Amma ban biye mata ba na yaƙe ta, na miƙe na faɗa kitchen bayan na yi sallar mangariba na bar su Jidda a falo suna duba littafan makaranta domin ta ga ya min next week monday za su fara jarabawa shi ne na ce maza su ɗauko littafan su mu yi karatu, mun fara kenan tunanin dafa wani abu ya shige ni sai na tashi na bar su, suna yi su kaɗai.
Ina shiga kitchen ɗin bayan tsayawa na tsawon mintina goma da nazari na ji kawai tuwo na ke son yi, to amma Yallaɓai bai cika son tuwo ba wani lokacin, na so na kira shi amma sai na fasa kar ya zo suna tare da Gimbiya sai na koma falon na ɗau wayata na tura mata saƙo.
"Na yi mana Tuwo yau?
Kamar ya na jira duka duka da turawan ko minti biyu ba a yi ba sai ga amarsa shi.
"Da kin faranta mini zuciyata Madam."
Sai da na yi mirmishi da na karanta sakon. Ni na san ya na can cikin damuwa bai yi tunanin buɗe masa mganar da na yi ba ɗazu ya fita cikin sanyin jiki ya na tunanin ina can ina fushi da shi, ni ko bai san abin da na faɗa ni tuni ya wuce daga wajena ba, na dai fitar da abin da ke raina ne saboda ba na so ya ƙara maimaita abin da ya yi yau, sannan kuma ya daina min kame kame ni da shi duk mu san gaskiya.
Nan take na kunna gas na dora ruwan tuwo na deɓo shinkafar tuwo ina ɗan gyarawa, wanketa na yi na zuba na rufe sannan na dauko sauran man suyan salla da na saka kasusuwan da suke rage daman tuni tuni na ce miya zan yi da shi na yauƙi na ci tuwo da shi, to na duba kubewata ta kare sai kawai na ce ba ri na yi miyar zolagale, saboda dare ya yi sai na kunna wani gas ɗin na ɗora miya saboda ina so na gama a kan lokaci kafin Yallaɓai ya dawo.
Allah ya taimake ni bayan isha'i na gama tuwon, har na ɗaure a leda, kuma daman bai da yawa saboda ma ɗumamen safe ne, miyan ne a kan wuta ba ta karisa ba sai tashin kamshi take yi sannan na saka mata man shanu tunda akwai sauran shi, Jidda na bar ma sallahu in miyan ta ƙarisa ta kashe gas ɗin duk da na ɗan rage ni kuma na je na yi wanka na ɗauro alwala na yi sallar isha'i sannan na sauya kaya na saka wasu riga da wando pakistan Mimisco ce ta taɓa kawo min tsaraba da ta je England. Kitson 2steps a ka yi min sai na zubo shi ta baya, saboda hulan da na saka tsakiyar kai ana gani shara shara ce ta na dai da tuntun love daga tsakiya, hulan mai adon pick irin adon jikin pakistan ɗin da ke jikina har da su jan baki na saka na sha gazal da mascara.
Har taran dare Yallaɓai bai dawo ba, Baby ta yi barci ni da jidda kawai muka ci tuwon muna ta santi faɗi ta ke yi" Umma tuwon nan ya yi daɗi."
Ina mirmishi na ce" Na gode É—iyar Umma."
Kallonta na ke yi ina mirmishi ni kaÉ—ai bayan mun gama ci ita ta kwashe komai ta kai kitchen, nima bin bayanta na yi na wanko hannuna sai da muka dawo falo ta na tattara littafanta na kira sunan ta.
"Jidda."
"Na'am Umma."
Ta amsa min ta na mai mayar da hankalinta a kaina.
"Gobe za mu tafi biki Yashe ni da Ummar ku Rahila."
Ina kallona sai na ga ta buÉ—e baki amma ba ta yi magana ba.
"Kuma sati É—aya zan yi in sha Allahu."
Ido ta zaro kafin ta ce" Sati É—aya Umma? Ina dariya na ce" E ko ya yi kaÉ—an ne?
Sai ta dawo gefena ta zauna ta na faɗin" Umma zan biki don Allah ban taɓa zuwa ba."
"A'a makaranta Jidda. Ki bari dai in an yi hutu in da mai zuwa sai na haÉ—a ku ku je tare."
Ta na wani kwabe fuska ta ce" Umma to da wa za mu zauna a gida?
"Da wa kuwa? Ga Abban ku.'
Sai ta yi shuru ba ta yi magana ba amma ta ɓata rai, a raina na ce tafiya fa ba fashi ko ya riƙa dawowa gida da wuri ko ya kwashe ku zuwa Gwammaja wannan duk ya rage na shi.
Ina zaune Jidda ta kwashe duka littafab makarantar su ta kai ɗakin su, sannan ta zo ta ta da Baby suka shige ɗaki na bi su da cewa su yi fitsari kafin su kwanta kar kuma su manta addu'an barci shigan su ba daɗewa sai ga Yallaɓai ya shigo gidan, ya siyo min kwaakwa mai yawa saboda ya san ina so, akwai halin Yallaɓai da na ke matuƙar so shi ne ba ya shigowa gida hannu rabbana ko ba shi da kuɗi sai ya san abin da ya tsaya a siya a hanya ko saboda yara in ba su yi barci ba su ta so suna masa oyoyo sai ya ji nauyin in bai taho musu da wani abu ba, ni kaina in dai ya san abu ina so to ko a ina ya gan shi sai ya siyomin ya taho min dashi.
Bai ma tsaya wanka ba ya ce na zuba masa tuwon yana gaya min tun safe kankana ce kawai a cikinsa muna kan dining zaune lokacin ina zuba masa tuwon na ce"Kai. To me ya sa ba ka tsaya a gida ka karya ba.?
Na faÉ—a ina tura masa filet É—in gabansa, sai da ya saka cokali ya fara kai lomar farko ya haÉ—iye sannan ya kalleni ya na faÉ—in" Saboda kina jin haushina."
Waro ido na yi kafin na ce" Ni? Sai ya gyaÉ—a min kai lokacin akwai tuwo a bakinsa sai da ya haÉ—iye sannan ya ce" E. Haka kika ce min da safe ko kin manta ne?
Ya faɗa ya na mai kallona sai kawai na ce Uhm! Daga nan ban ƙara mgana ba shima sai da ya ci ya koshi ya haɗa da ruwa sannan ya yi hamdala, ni daman tun farko na ce masa na ƙoshi mun ci tare da Jidda.
"Girki ya yi daɗi. Allah ya yi miki albarka amma a bi ni bashi zan biya tuƙwaici."
CMirmishi kawai na yi ban yi mgana ba, hannun shi kawai na ji a wajen wuyana ya na jan jelan gashina lokaci É—aya ya na faÉ—in" Kitso a ka yi ba a gaya min ba? Kai tsaye na ce" Kitson tafiya ne"
"Tafiya kuma?
"E. Ka manta za mu je can Yashe biki."
Sai ya kaÉ—a kai kafin ya ce" Na sha'afa. Tafiyar ba sai jumma'a ba ne?
Ina kallon shi na ce" Gobe ne."
"Gobe fa?
Ya maimaita cikin mamaki ni kuma sai na ƙara gyaɗa masa kai, bai ce komai ba kamar dai ya na mamaki ne ni kuma sai na shanye masa mamakin na miƙe ina tattara kwanukan da ya ɓata na ɗauka zuwa kitchen, lokacin da na dawo ba shi a falon ya shige ciki, ni kuma bayan na gama abin da na ke yi sai na kashe hasken falon na rufe ɗakin su Jidda na leƙa na duba su, bargo na gyara ma Jidda a kafafunta da ya janye Baby kuma kai ba ɗankwali sai da na binciko mata hula mai igiya na saka mata tana ta ture min hannu a cikin barci bayan na gama na rage musu hasken ɗakin na jawo musu kofa bayan na tofa musu addu'an barci.
Har falon yara da kitchen sai da na rage hasken wuta na kashe komai sannan na wuce bedroom na iske Yallaɓai har ya yi wanka ya na saka kayan barci sai da na shigo na tuna da akwatina da na bari a kan gado sai na saka hannu na dago shi na sauke shi a gefe.
"Kwana nawa za ki yi ne?
Na ji Yallaɓai na tambaya, ban juyo na kalle shi ba na ce" Sati ɗaya in sha Allahu."
Na kalle shi, ya na goge kansa da ƙaramin towel ne a lokacin amma sai da ya tsaya kawai ya na kallona ni ko na sha kuni na ƙarisa gaban wardrop na buɗe ina neman kayan barcin da zan saka.
"To yara fa?
"Su zauna anan ko Gwammaja."
 Na faɗa ina mai tube rigar jikina bai ce komai ba, nima ban neme wata mgana ba har muka gama shirin barci mu ka kwanta gabaɗaya. Ina jin sa ya na ta juye juye ya na so ya yi magana amma ya kasa, ni ko da gangan na mulmula na haye jikinsa na sagalo hannayena ta wuyansa na yi lamo har na yi barci ina jin bugawar zuciyarsa sannan hannayensa da ya riƙe da su duk a sanyaye, ni dai ban san lokacin da barci ya kwashe shi ba, ni dai sai asuba na tashi saboda zan yi tafiya kuma har ga Allah ya ba ni tausayi shi ya sa ya na dawowa salla asuba na rumgumeshi ina faɗin" Mu yi ɓarnan ruwa ne Yallaɓai na? Ko na bankwana ba za ka nema ba?