Sashe 50
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ta yi shuru ta na dariya ni kuma ina hararanta. Kafin ta cire Hijabin da ta shigo da shi na ce tsaya na ta ce shayin nan ta miƙa ma Yallaɓai da ta wuto su a falo, ita na ba ma shayin ta kai masa sai ga shi ta dawo ta na ce min" Umma ɗayan baƙon fa ya ce shi ina na shi Shayin?
Ina dariya na ce ta juye sauran a fulas ƙarami ta ɗau Mug ta kai musu falon daman akwai siga a can saman dining za su yi amfani da shi.
Zuwan Marwa ya sa na koma na zauna ta karɓe ni daga aiki ina falo ina duba wayata ana ta siyan Hijabai tun da salla ta karato bai fi saura kwana goma ya rage ba, ina nan zaune Yallaɓai ya leƙo ya na cewa na zo mu yi sallama Kawu zai tafi, sai na rarumi Hijabin Marwa na zura tunda nawa na kai sa cikin ɗaki.
Na ɗauka ma har ya miƙe ne sai kuma na je na gan shi zaune suna hira da Yallaɓai ina daga tsayen na ce" Kawu har an gama yi mana yinin?
Ya na dariya ya ce" Taho ki zauna ai ban ga ta tafiya ba tun da ban yaÉ—a munafata ba."
Cikin mamaki na zagayo na zauna kujeran zaman mutun ɗaya. Kawu na ke kallo duk da ina ganin mutumin nawa na ta kallona ni kuma sai na ba ma banza Ajiyar a cikin raina ma sai na ɗauka kamar bashi a wajen ba dai ni zai wulaƙanta ba wallahi sai ya ga ne bashi da wayau da ni ya ke zencen ba ya ce Gimbiya ta yi masa komai ba to zan bar shi da ita ta yi masa abin da ma ni ban taɓa yi masa ba.
"Kawu me ya faru?
Na faÉ—a ina kallon shi, wani lokacin in ce masa Uncle wani lokacin kuma Kawu. Amma dai Uncle É—in ya fi kama bakina.
"Ba nan muka fara magana na ce miki na ga wani iri a gidan nan ba?
Da sauri na gyaÉ—a masa kai kawai sai ya cigaba da faÉ—in" Ga irin nan muna zaune a falon nan ta shigo. Ita ce wacce ki ka aiko ta kawo mana shayi."
Ido na zaro ina kallon shi kafin na yi magana Yallaɓai ya tare ni.
"Wai Marwa?
Ya faÉ—a ya na kallon shi, shi ma kallon na shi ya yi kafin ya ce" Ina ruwanka? Da kai na ke magana."
"Allah ya baka haƙuri."
Yallaɓai ya faɗa ya na ɗauko wayarsa daga cikin aljuhu ya yi kamar hankalinsa na kan wayar amma ni na san hankalin shi na kanmu ne.
"Sunan ta Marwa ne?
Kawu ya tambayeni ya na kallona cikin mamaki da ya kasa ɓoyuwa a saman fuskata na gyaɗa masa kai kafin na ce" Sunan ta Marwa."
"Ya kuke da ita?
Ina mirmishi na ce" ÆŠiya ta ce. ÆŠiyar yayarmu ce Ya Aina uban mu É—aya da mahaifiyarta."
Sai kawai ya koma ya É—ora kafa kan É—aya kafin ya ce" Alhamdulillah."
Ina dariya amma ban yi magana ba amma ni kaina lamarin ya zo min a bazata Marwa fa? Yanzu duk Æ´an matan duniya Kawu Marwa ya gani kuma ya yaba ikon Allah.
"Wato haƙiƙa tun ranar bikin tariyan wannan yaron na ganta lokacin ta kawo mana abinci na yaba da natsuwarta to na ɗauka lamarin wasa ne shi ya sa ban yi magana ba. Sai kuma da na koma gida ina ta tunaninta ta na yawan faɗo min a cikin tunanina na so ma na kira ki a waya sai sabgogi suka sha kaina sai yanzu da na ƙara ganin ta sai na ji zuciyata ta ƙara yin wani nauyi a kanta."
"Uncle.."
Na faɗa ina ta dariya ina jin wani farinciki a ƙasan raina ba ni kaɗai ba hatta Yallaɓai fuskar shi ta cika da Annuri domin ni dai yau ce rana ta farko da Kawu ya zauna ya taɓa yabon wata mace duk wacce aka yi masa tayin ta sai ya kushe ta. Amma wai Marwa ce ta yi masa ikon Allah ya fi gaban wasa.
"Kawu ka ce kawai ka faÉ—a tarkon so."
DaKafarsa ya zungure shi ya na faɗin" Wai ba na ce ba ruwanka ba! Ina mgana da surukata kar ka ƙara saka min baki malam."
Yallaɓai na danne dariyan shi ya ce" Kawu"
" Ka sake kiran sunana zan iya yi maka baki."
Ya faÉ—a ya na hararan shi kafin ma ya ce" Kai tashi ma ka fita"
"Allah ya huci zuciyar ka."
Sai ya yi kyaci sannan ya dawo da hankalin shi kaina ya na gyara zama.
"Kamar dai ina son ta ne fa."
Ni kaina na kasa danne dariya ta sai da na sake ta jin kalaman Kawu har ya na wani gyaran murya, Yallabai ko har ya na duƙewa Kawu ya kai masa naushi sai ya kauce ya tashi ya sauya kujeran zama, sai ya koma ya na kallona kafin ya ce" Surukata dariya kuma kike yi?
Ina danne dariya ta na ce" Na isa Kawu. Yanzu dai ya kake so a yi?
Sai ya yi shuru kafin ya ce" To za ku iya aura mata tsoho kamar ni?
Kai na gyaÉ—a kafin na ce" Me zai hana in dai ta na son ka?
"To kina ganin za ta so ni? Kalle ni fa ba ma arba'in baya."
"Me zai hana ta soka Kawu? Ai kawai nema za ka shiga yi har sai ciyo mana yaƙin a cikin zuciyarta."
"Ko? Kina ganin zan iya?
Ina mirmishi na ce" In sha Allah za ka yi."
"To kina ganin in ta aminta da ni za ta iya zama a Rano.?
"Me zai hana Kawu? A ko'ina aure ya kaita ai za ta zauna in sha Allahu."
Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Haka ne. Shekaranta nawa ne?
"Ashirin da uku."
"Ta na makaranta ne?
"E. Ta na makaranta koyon aikin jinya a garin tsafe amma yanzu ta dawo gida ne ta na pratical."
"Ta kusa gamawa? Ji na ke yi kamar ba zan iya jiran wani dogon lokaci ba."
Ina dariya na ce" Ina jin ta kusa gamawa gaskiya."
Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Sadiya da gaske ina son ɗiyar ki tun ranar farko da na fara ganinta ban ƙara tabbatarwa ba sai yau da na ganta. Allah ya sa ku ba ni ita."
"In sha Allahu za mu baka ita in rabon ka ne Kawu"
Ina danne dariyata ganin duk ya susuce Yallaɓai ya kalla da ya kasaƙe da waya a hannun shi ya na jin mu.
"Kai wai ba ka so ka yi albarka ne?
"Me na yi kuma?
Ya faÉ—a ya na danne dariya Kawu Abba ya jinjina kai kafin ya ce" Ka ce wani abu mana. Ko fatan alheri ba za ka iya yi min ba Tafida?
Hannuwana ya ɗaga sama kafin ya ce" In ce me? Ni da ka ce ba ruwana in na ƙara saka maka baki a cikin maganar ka za ka yi min baki?
"To na janye kalamaina saka bakin ka na ji."
"Me zan ce?
Sai kawai ya tsaya ya na kallon shi, shi kuma ya na dariya kafin ya ce" Allah ya ba da sa'a Kawu na."
"Amin to in ma ba har zucci ba ne."
Ni dai ina gefe ina ta faman mirmishi zuciyata kamar farar takarda.
Kawai sai wayar Kawu ta fara ƙara alamun ana kira ya na duba sunan mai kiran ya kalleni sannan ya Kalli Yallaɓai kafin ya ce" Gaskiya Tafida ka cika tsurku"
"Me na yi?
"Me ka faÉ—a ma Tariq ya ke kirana?
"Ni? Me na faÉ—a masa kuwa? Ya dai ji kana faÉ—a da bakin ka"
"Au recording ka yi ka tura masa munafuki da matan ka biyu kana gulma?
"Wani recording? Direct ya ji Soyayya ya fara zautaa ka."
Kawu sai kawai ya tsaya ya na kallon shi har wayar ta katse bai ɗauka ba shi kuma Yallaɓai na yi masa dariya.
"ÆŠauki wayarka fatan alheri zai yi maka fa. Ko ba ka so?
"Ina so mana. Ko da bai kai zuciyar ku ba."
Ya faÉ—a lokaci É—aya ya na É—aga wayar amma ya sa ka a speaker.
"Kawu ina kwana."
Tariq ya faɗa daga can bangaren Kawu ya haɗe rai kamar ya na ganin shi kafin ya ce" kirani Abba na ko Abdulmu'iz domin ni ba Kawun ka ba ne."
Kaina na ƙasa ina danne dariya Yallaɓai ko har ya na ba ta sauti saboda dariya.
"Mu ba Æ´an'uwan juna ba ne?
"Ni ban haÉ—a komai da kai ba Mallam."
"To na ji ina yi ma Tafida kara ne."
"Shima ai ni ƙanin uwarsa ne ba na Ubansa ba."
Yallaɓai dariya har ya na ƙyaƙyawata ya na kallona da mun haɗa ido sai na haɗe rai na juyar da fuska.
"Haka ne. To a bar mganar."
"Yauwa yi fatan alherin ka ina mgana da Surukata ne ka katse ni."
"Kawu ashe kuma an faɗa tarkon so? Ƴar yarinya ta susuta haka?
"E ko ban kai ta susutanin ba ne?
"Ni? Ban ce ba haba ai ka isa ma har ka gota. Kawu Allah Ubangiji ya sanya alheri ya sa a wannan shekaran za mu sallama ka."
"To Amin."
Ya faɗa ya na ɗan mirmishi kafin Tariq ya cigaba da faɗin" Mutumina kawai Tafida na kirana ina ɗauka ba sai na ji kana ruwan haruffan ƙauna ba. Wai wata yarinya ce ta susuta ka haka! Na san ta kuwa?
"Ba ka san ta ba."
"Tafida."
Tariq ya ɗaga murya ya na kiran Yallaɓai shima ya amsa ya na faɗin" Ɗan'uwa nawa ka tara? Kasan mun yi alƙwarin biyan sadaki da kuɗin gaisuwa fa?
Tariq ya ce" Ai asusu na yi. Shekaru sama da goma. Ka ce lokacin fasa asusu ya kama mu."
"Tabbas. Domin da gaggawa ya ke so da wahala ma ya iya jira."
"Allah. Ka ce Kawu dai ya faÉ—a
da yawa."
"Ba ma a mgana sai ma ka gan shi duk ya susuce."
"Yo min Video É—in shi mana."