← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 89

Sashe 48

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sake taso min babu nadama ma a cikin maganganun sa sai kawai na sake fashewa da kuka wani abu mai É—aci na sukan zuciyata.
kawai sai gani na na yi na miƙe ina faɗin" Yau ni kake yi ma gorin ban kula da Nene ba Yusuf? Ni kake yi ma gori?

Sai ya yi shuru bai yi magana ba sai kawai na yi murmishin takaici ga hawaye wasu na korar wasu, sai kawai na kaɗa kaina kafin na ce" Zan faɗa ba domin ina so ka yarda da ni ba. Tunda Nene ta kwanta asibiti har ta dawo gida ban taɓa fashi ba, ko ban je na kwana da ita a yanzu a baya in ka manta na yi ƙila sama da abin da ka ke jijiyan wuya matarka ta yi. Mganar ban je Gwammaja ba ranar kuma ba ni da lafiya ne kwanciyar da ka ga ina yi ba ta lafiya ba ce, kuma na yi ta kiran wayar ka na faɗa ban samu ba ne, shi ne ka ke tunanin da gangan na ƙi zuwa? Kai iya naka zuciyar alherin kenan Yusuf?

Na faÉ—a ina kallon shi, ina kuka saboda zuciyata ma zafi ta ke yi min ina numfashi sama sama kamar mai ciwon Asthama."

"Wa kika faÉ—a ma ba ki da lafiya! Kin faÉ—a min? Ko ina da Allah musuru ne da zan san ba ki da lafiya.?

Ya faÉ—a ya na kallona amma ya É—an sassauta muryan shi.
Kawai sai na kalle shi, sai ji na yi kamar juwwa za ta kwashe ni sai kawai na taka na fice daga ɗakin ina ji kuka na taso min daga ƙasan raina falon yara na koma na zauna na ci kukana kamar zan shiɗe, na tabbata in na cigaba da kuka nan zafin da zuciyata ta ke yi za ta iya bugawa na mutu Yusuf ba shi da asara. Ni wai yau Yallaɓai ya kalli tsabar idona ya na faɗa min Gimbiya ta yi masa komai wato ni kuma ban yi masa ba kenan ya manta tarin alherina a gareshi yau ni ce na zama mara zuciyar alheri, ina hawaye ina tuna baya, akwai wani lokaci a baya lokacin na haifi Jidda Nene ta yi wani ciwon kafafu mai zafin da ko bayi sai an kaita ni na koma Gwammaja da ga ni har Yusuf muna kwana acan ina kula da ita. Lokacin Mimisco ba su kasar ita da mijinta Anty Bahijja da Anty Maimuna kowacce na da iyalanta Halima ce lokacin kuma ta na makaranta ni ce na zauna da Nene har ta samu lafiya sannan na koma gidana a lokacin Yallaɓai ya ce na gama masa komai a duniya shi ne yau zai manta baya ya kalli tsabar idona yana faɗin Gimbiya ce ta yi masa komai ni kuma ban yi masa ba tunda zuciya ta ba alheri a cikinta, anan na kwana a falo a kan kujera ina kuka kukan baƙin ciki da takaici dare kuma mafi tsawo a wajena, ya ce wai daga na ce ya yi min kaza sai na ce ƴan'uwan sa sun yi min kaza ban da namiji mai manta alheri ni me na ce sun yi min? Ya manta yadda a baya na bauta musu na yi musu biyayya, amma yau duk ya manta sannan ya ce ni na tsani matarsa yaushe na ce na tsane ta? Kawai dai laifin nawa ne ya yi masa ƙaranci shi ya sa daga ya ce na yi kaza sai ya ce na yi kaza amma na kudira a cikin zuciya zan kiyaye ma komai na Yallaɓai yau ko korata ya yi a gidan shi ba zan buɗe baki na ce masa don me ba! Tunda ya iya kirana mara alheri na tabbata a gaba zai iya aikata komai.

Har gabda asuba idona biyu sai a lokacin na samu barci sai sa na ji Jidda na tashina har sun yi salla, na tashi da karfin zuciyata amma idanuwana har sun kumbura saboda kuka. Tiolet din su na shiga na kama ruwa, sannan na zo muka yi azkar tare na shiga kitchen na ɗora musu abin breakfast ko ɗakin ban fatan komawa Yallaɓan ne ba na son gani saboda gabaɗaya baƙin sa na ke gani a cikin zuciyata shi ya sa ko hanyar ɗakin ma ban sake bi ba, a kan dining na jera masa abin karinsa na shige ɗakin su Jidda acan na yi wanka Allah ya sa na leƙa Yallaɓai ya shiga tiolet sai na lallaɓa na dauko kayana da abubuwan amfanina na fice na barsa ma ɗakin.

Yadda na ɗau gaba dashi haka shima ya ɗau gaba da ni. Tun daga ranar ban ƙara kwana a ɗakin ba a ɗayan ɗakin na ke kwana, kuma kafin ya dawo mun shige ciki ban son na kwana da yara su fahimci wani abu, in kuma da safe ne kafin ya fito na gama masa komai na ijiye masa na koma cikin ɗaki. Wani lokacin ya ci wani lokacin kuma ya bar min kayana, ni kuma ban damu ba domin duk abin da Yallaɓai zai yi min ko zai ƙara min ba zai ba ni mamaki ba.
Ranar junma'a Musbahu ya kawo min cefane duk da bai faɗamin ba a raina na ce ƙila Gimbiya za ta koma ne illau ko da yamma ya zo gidan ina jin shigowarsa na shige ciki sai can na ji tafiyarsa sai ga Jidda ta shigo ta kawo min man shanu da kuɗi 10k sannan ya ce a faɗa min Gimbiya ta koma gidanta ƙala ban ce ba na karɓi kuɗin na ijiye man shanun kuma na kai kitchen na ɗora tukunya na soya shi, a daran nan sai ga Ya Aina ta zo duba ni  Baban Marwa ya kawo ta ai na ce na ji sauƙi nan na roƙa na ce Marwa ta zo ta min weekend don Allah, baban ta ya ce ai Marwa ƴa ta ce umarni kawai zan ba da sai a faɗa mata sun ɗan jima kafin su tafi kuma na ji daɗi ɗan'uwana mai daɗi, a da ji na nake yi kamar a cikin kurkuku duk in da na yi tunanin zuwa sai na ga ba zan iya tambayan shi ba gwara na haƙura in ma shekara za mu yi a haka sai dai a yi.

Washegari asabar su Jidda sun tafi Tahfez a ranar aka kawo min Hijabai daga zariya Musbahu daman ke karɓan min a nan Zaria road motar in ta shigo cikin gari sai ta tsaya nan ya karɓa min, shi ya kawo min har ya na ce min na ijiye masa guda biyu ni kuma na tasa shi da tsiyan ko ya samo mata ne.

"Sai Yallaɓan ki ya sallame ni tukunna ko zan ɗauko maganar aure."

Ina dariya na ce" Haba tun yaushe ya sallame me ka."

"To ina ga ko Sabon Office ɗin nan na ƙasa in da muke na wa ne?

Cikin zolaya ya faɗa, ni da ya ke ban ma san da shi ba amma ban nuna ba sai na ce ƙila na ka ɗin ne, mun yi ta hira har muka gangaro maganar gidan Bulo ya na faɗa min an fi wata biyu ba a aiki, Yallabai duk ya bari wajen na neman mutuwa.

"Anty Sadiya ki yi masa mgana don Allah kar ya bari wajen ya mutu. Tun da ya na jin maganar ki."

A raina na ce a da kenan, yanzu kam sai dai Gimbiya. Amma ban nuna masa ba sai kawai na ce zan masa mgana. Tuni na manta da takaicin Yallaɓai, na fara kiran mutane ina faɗa musu an kawo hijabai su siya na salla tunda babbar salla ke kusanto mu. Har Ma'u na kira na yi mata tallah sai ce min ta yi ai ta ji labarin ina sai da Hijabai ban yi mata tallah ba ne ya sa ba ta siya ba amma tunda yanzu na yi mata talla za ta zo gida ta duba ni dai a raina na ce kya ji da shi munafuka
Ya Muntari ma na yi masa talla na ce ya siya ma Rahila da yara. Har Nasir da Mutaƙƙa sai da na ce su siya ma matan su da yara. Kuma duk sun ce matan za su zo gida su duba. Ranar dai ban yinin kunci ba cikin walwala na yini ranar Yallaɓai bai zo gidan ba sai can dare na ga saƙon shi saboda haushi na goge shi ma.

"Ya kuke? Fatan kuna lafiya"

Na gani amma sai na goge na kama harkan gaba na. Washegari Lahadi sai ga Kawu Abba ya zo ya ma ɗauka Yallaɓai na gidan ne na ce masa ba nan ya kwana ba ya na gidan Amarya shi kuma ya ce ya na ta kiran wayarsa ba ya samu ya shigo garin ne kuma ya na so su haɗu.
A gidan ya karya ni na haɗo masa abin karyawa, muna ta hira da shi, kuma har lokacin bai samu wayar Yallaɓai ba sai daga baya ya ce ni na jara ba kiran shi a wayata mana ko zan same shi.

"Ka yi haƙuri Kawu ka cigaba dai da gwadawa in baka same shi ba sai ka je gidan mana."

Na faÉ—a ina kallon shi, sai kawai ya tsaya ya na kallona kafin ya ce" Me ya faru ne Sadiya? Tafida ya yi miki wani abu ne?

Idanuwana suka cika da kwalla na yi saurin basarwa.

"Bakomai."

"A'a da komai fa."

Ya faÉ—a ya na kallona lokaci É—aya kuma ya na nazartan yanayina.

*Janafty*
*TKG*

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

13.

Kaina na mayar ƙasa ina wasa da gefen hijabina. Sai na sake ɗagowa ina kallon shi jin ya yi shuru sai muka haɗa ido dashi da sauri na ƙara sadda kaina ƙasa domin har ƙwalla sun cika min ƙwarmin idanuwana tuna irin cin mutumcin da Yallaɓai ya yi min.

"Me ya faru?
Chapter 48 · 0% Book details