← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 89

Sashe 28

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amin. Ki yi hakuri kin ji ko?

Ya sake faÉ—a ya na mai kallona sai na girgiza masa kai kafin na ce" Kar ka damu bakomai."
Na faɗa ina danne yanayinaa shi kuma ya yi shuru ne kawai rasa abin cewa tun da na dakatar da shi faɗa min halin da Gimbiya ke ciki, ni dai a falo na bar sa ya shiga zurfin tunani na koma ɗaki kawai na yi tagumi, in lissafina ya yi dai dai saura kwanaki kaɗan tariyan Gimbiya. Kenan ya dai tabbata Yallaɓai ya zama namu ya tashi daga nawa ni kaɗai.

Na kai tunani zurfi na tuno lokacin da muka tare a wannan gidan. Lokacin da ya ya ma aka ƙarisa aikin gidan? Dakyar ne da soɗin goshi, sannan kuma lokacin ba ni da komai daga ni sai gado sai kujeru. Allah ya taimake ni yan'uwana suka tallafamin na fita kunya. Kayan ɗakina na siyar aka yi min sabon gado da kujeru, gadon shi ne a bedroom ɗin mu sai kuma kujerun a falon Yallaɓai, ɗakin yara kuma Ya Auwal ya taimaka min da kuɗi na yi musu gadajen ne, sai kuma na Ya Hamza shima da ya bani, na siya kayan kitchen ko na ce na ƙara sai cafet ɗin falo sauran kayan duk a hankali a hankali na riƙa siyan su, ko falon yara adashe na shiga na tara su kuɗi na yi kujerun nan da cafet sai dispanser abin da Yallaɓai ya siya daga Tv sai fridge duk ni na gama faɗi tashina kuɗaɗena duk suna kan shi, in na yi magana sai ya ce zai ba ni zai buɗe min shago in aka biya su, sai ga shi kuɗin aiki nawa a ka biya shi? Yanzu ba ta ni ya ke ba komai da ya samu kan maganar Tariyan nan ce a gabansa.

Na ci kukana na share hawayena ni kaɗai ba wanda ya sani. Tariyan ya kama 28 ga wata ne, na kira Inna Maariya na faɗa mata ta ce za su zo in sha Allahu. Sannan ba tunanin auran nan da Yallaɓai ya yi ba ne zai saka ni gyara ba domin ni ɗin daman mai gyara ce na kira Surayya Halin yau na ce ina son haɗin uwargida, ta ce an gama sannan na sake siyan man gyaran jiki a wajen Aisha Lame, saboda ko Yallaɓai ya sha ce min fatata kamar ta Baby saboda taushi. To mayuka Aisha lame ni masu saka taushin fata da santsi, a can group din gida na sanar da tariyan Yallaɓai na kuma ce ina gayyatan kowa da kowa a ranar a gidana zan yi taro, Ya Auwal ya kirani ya ce Laila za ta zo garin daman suna da biki itama na ce na ji daɗin haka Amina ma da ban yi zato ba, sai gashi ta kirani ta na faɗa min a bar ta za ta zo, kuma haƙiƙa na ji dadin jin haka har Faridan Tariq ma ta ce za ta zo kuma ta ce min a gidana za ta sauka tabbas na yaba da wannan karamcin.

Na kira Hauwa da Munnira sun zo mun yi shawara. Suka ce na siya kaya sabbi na ɗinka saboda in shiga in fita, haka ko aka yi na siya kala biyar atamfa uku leshi ɗaya, material ɗaya sai yara ma na yi musu duk da Yallaɓai ya yi mana shadda da ni da shi da yaran gabaɗaya. Ni ban ma san wa ya faɗa musu Abban su ya auri Anty Gimbiya ba sai da Jidda ta tambayeni na ce hakane ina tunanin lokacin da na je Yashe ne aka faɗa musu a Gwammaja ko baban na su ya faɗa musu da kanshi ban dai sani ba, maganar taron da zan yi kuma da kaina na samu Yallaɓai na faɗa masa ina so na yi taro ƴan'uwa ba su zo su taya ni zama da nuna masa farinciki.

"Shi ne ba ki faÉ—a min da wuri ba?

Ya faÉ—a cikin nuna mamakinsa ko bai yi tunanin zan yi taron ba ne.

"Na É—auka ka san uwargida na yin taro ko?

"E. Amma ban É—auka ke za ki yi ba."

Hararan wasa na yi masa kafin na ce" Ban kai yadda ka ke tunanina ba."
Mirmishi ya yi nima na ta ya shi, mun tsara za a yo cefane tunda muna da shinkafan tuwo za mu yi waina sai Nama da za a kawo da kayan Miya sannan shima ya ce min Kawu zai zo shi da Tariq suma suna son wainar na ce ba komai sai a yi da su gabaÉ—aya.
Ko bai faÉ—a min ba na san ya ji daÉ—in yadda ya ga ina ta masa dariya ina ta kuma shirye shirye, tun yana sharewa har dai ya furtamin da kansa.

"Na gode Sadiya ta. Ina ƙaunarki saboda Allah."

"Nima ai saboda Allahn na ke sonka ko Yallaɓai?

Na faɗa ina masa fari. Lokacin da daddare ne na fito wanka da sauri Yallaɓai ya ta so ya rumgume ni ya na shinshina min wuya, cakulckuli ya fara min na fara dariya ina ture sa.
Allah sarki rayuwa. Yanzu fa nan da kwanaki sai dai Yallaɓai ya zo mu gaisa da safe in dai ya na gidan Amarya.

Tabbas kishi ya na da zafi. Kuma zama Turken gida abu ne mai matuƙar wahala.

*Janafty*
*TKG*

08.

Ranar alhamis su Jidda suka yi hutun makaranta. Jidda daman ita ce ta ke ɗaukan first postion a ajinsu Baby kuma Third, sun karɓo kyatuttuka tunda an yi speach and prize giving day ban je ba amma Yallaɓai ya je musu tare ma suka dawo.
Ko da suka dawo mai kitso ta zo, da mai ƙunshi har an yi min ƙunshi saura kitso.
Marwa daman ta na nan domin ni na ce ce ta tattaro, ta dawo wajena sai an gama biki, Amina ma ta iso tun azahar Hauwa da Munnira suna gidan suma tun safe sai zlZaitunan yaya Abubakar.
Sameena ta kira ni ta ce suna nan tafe gobe ina mata tsiyan ita ko yar gidan amarya ce tana dariya ta ce.

"Matar Baba akwai amana ni ai ina bayan uwargidan Yallaɓai."

Haka dai muka gama wayar muna ta barkwanci, a bakin su Hauwa na ke jin mai gyaran jiki daga maiduguri Anty Bahijja ta ɗauko ma Gimbiya tun ana saura sati ɗaya ta sauka a gidan Nene. Taro ne Gimbiyar ta shirya sosai tun da ƙawayenta duk na Rano da Abuja da nan kano za su zo baban aminiyarta Naja dai daman suna tare ko da yaushe, tun da ba ɗaurin aure taron gabaɗaya na mata ne.
Ƙannen Gimbiya da matan yayyenta duk Kano za su zo, can Rano sai dai manya dangi dai na can amma taron gabaɗaya ya na nan ne, a ranar alhamis ɗin ma aka je aka gyara gidan Amarya Halima ta biyo daga can zuwa gidana ta ke faɗe, ni dai ina gefo ban ce komai ba,

Ban gayyaci kowa daga dangin Yallaɓai ba, sai wanda ya ga niyya ya zo. Amma ni dai na gayyato kaf ahalima har da Ma'u saboda na tusa mata haushi na ce ta gayyato min Shema'u.
Na kuma san ita kanta ta yi mamaki, na kuma san za ta je can ɗin za kuma ta zo nan tunda Anty Bahijja kamar ita ce ma uwar Amarya saboda yadda ta ke rawan jiki kan auran nan, daman burinta ne da daɗewa na daina juyi a gidan ɗan'uwanta ni kaɗai gani ta ke yi kamar wata tsiyar Ɗan'uwan nata ya ke ba ni, ni fa shi ya sa har gwara Anty Maimuna a kan Anty Bahijja matar nan sam ba ta da hali mai kyau akwai baƙin ciki amma ita ta na can gidan wani a dangi wasu ta na abin da ta ga dama.

Ni da ya ke ko a waya na rufe ta ba zan ga status ɗin ta saboda ina da tabbacin da gayya za ta yi ta ɗora abin da zan gani na ji haushi, ni kuma ba na so damuwa shi ya sa na kama kaina, ita kanta Gimbiyar ban san dalili ba ina jin ta aure min miji na goge lambarta a wayata cikin zafin ƙishi.
Kamar na san haka za ta faru Ranar jumma'a sun gudanar da walima anan haraban gidansu Nene a Gwammaja duk sun sha abayoyi sun sha kyau, tsabar ma renin hankali Anty Bahijja ta ce ma Yallaɓai wai nima na zo wajen Waliman tunda malama ce za ta zo ta yi wa'azi a kan aure, shi kuma da ya ke ya san a yanzu ina kan tsini ne magana ma ta arziƙi ta tsiya na ke mayar da ita sai bai yi min magana ba ya ce ta rabu da ni kawai su yi abin su.

Ni ban ma sani ba tunda Yallaɓai bai yi min maganar ba sai a safiyar jumma'an ta kirani a waya kuma daman na san da batun za su yi walima tunda Halima ta faɗa min, har ga Allah lokacin da na ga kiran Anty Bahijja a wayata sai da na ra ya a raina ba alheri a cikin kiran nata, amma ban ki ɗauka ba illau ko sai gashi ta na faɗa min wai ta aiko Tafida bai faɗa min saƙon ta ba ne?

Kai tsaye na ce" Wani saƙo kenan? Domin ni dai ba mu yi maganar wani saƙo da shi ba."
Lokacin ma bai jima da fita ba, ya tashi yau É—in da cewar ba ya jin daÉ—in jikinsa na É—auka munafuncin su na maza ne sai da na ji jikinsa ya É—au zafi sannan na yarda. Ya dai sha paracetomol ya fita da cewar zai je a duba shi.
Chapter 28 · 0% Book details