← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 89

Sashe 4

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau tare da yarana na karya ban ko jira Yallaɓai ba. Ban kuma koma ɗakin ba sai da Salisu ya zo suka tafi sannan na koma ɗakin ni dai na ji sa ya na waya sanda na shiga a mganar da na tsinta na karshe ce ya sa fahimci da wanda ya ke wayar. Uncle Abba ne domin na ji ya na faɗa min" Na kasa. Na kasa zama jarumi a gaban Sadiya Abba"

Daga nan na shigo É—akin sai kuma ganina ya sa ya yi saurin cewa" In na fita za mu yi mgana"
Da kuma sauri ya katse wayar ya na kallona. Ni ko sai na yi masa mirmishin ya ƙe kafin na ce" Wanka za ka fara yi ko sai ka karya?
Cikin ƙaramin sauti ya ce" Mu dai fara karyawa amma zuwa anjuma ko?
Kai tsaye na ce" To. Amma ni na riga na karya tare da yara.'
Ban bashi zarafin mgana ba na yi fit na bar masa ɗakin na faɗa tiolet ruwan zafi ya ƙare a tiolet sai da na fita kitchen na jona a buta ya tafasa sannan na juye na yi wanka da shi lokacin da na fito zan shigo ɗakin saboda ƙofar ba ta rufu ba sosai na ji sa ya na mgana kuma again kamar a waya ce.

"Haba Anty Bahijja ba na roƙe ku da kar ku bari  maganar auran nan ta fita ba tare da na faɗa ma Sadiya ba? Me ya sa kika yi status in ta gani fa?

Ban san me ta ke ce masa ba amma dai na ji ya amsata da cewa" Ko da kin cire ta don Allah ki goge. In ita ba ta gani wani na ta ya gani ya faÉ—a mata fa? Da wani ido zan kalleta? Duk bayanin da zan mata ba zan iya wanke kaina ba don girma Allah ku bari ni na samu jarumtar da zan iya faÉ—a mata ku bari ni mijinta ta fara jin mganar nan daga bakina."

Ban yi niyyar labe ba amma sai na ji ina so na ji har karshen mganar ta su. Kenan shima ya ga status ɗin da ta yi? Uhm wato ta cire ni amma ta manta ba ta cire yar'uwata Ma'u ba. Ko ta manta zan iya sani ta hanyarta ne? Jin ban ƙara jin mganarsa ba ne ya sa na san sun gama wayar kenan shi ya sa na yi gundubalan tura ƙofar na shigo ciki, ba shi da gaskiya shi ya sa ya wani firgita da ya ganni na shigo.
  Ta gefen ido na kalle shi sai kuma na basar da shi na isa kan kujeran madubi na ja na zauna ina shafa mai ina hangensa ta madubi wayarsa ce a hannunsa amma kuma hankalinsa na kaina ya kasa iya buɗe hira a tsakaninmu ni kuma daman tun a jiya na ji kamar an shimfiɗa wata tazara mai yawa a tsakaninmu na yi shuru kawai ina shafa mai bayan na gama na warware gashina na gyara sannan na tashi na isa ga wardrope na dauko wata doguwar rigar atamfata na saka ina cikin ɗaura ɗankwali na ji mganarsa.

"Yau sai aka karya a ka bar ni ko?

Ban juyo ba na ce" Tea kawai na sha."
Ya kasa mgana ni da na san Yallabai da hira amma yau kalaman bakinsa sun kare duk ya wani kama kanshi saboda na ƙure shi sai na juyo ina kallonsa kafin na ce" Lafiyan ka?
Da sauri ya ce" Me kika gani?
Cikin ido na kallesa kafin na ce" Bakomai."
Daman na latsa sa ne sai kuma bai bani kunya ba.
 
"Ni? Bakomai ke ce ma na ga tun jiya kin yi wani sanyi sanyi kamar ba ki da lafiya."

"Ko?

Na faÉ—a ina masa wani kallon tara saura kwata. Sai ya amsa da min E. Kafin ya É—ora da fadin" Ko duk laifina ne na jiya ba a gama hucewa ba?
Sai kawai na rausayar da kai kafin na ce" Ko É—aya ni fa lafiyata kalau. Kai ne dai na ha kamar a firgice ka ke."
"Ni?
Ya faɗa ya na kallona sai na gyaɗa mai kai kafin na ce" E.  Ka na yin abu kamar mara gaskiya. Yallaɓai me ka je ka yi ne ban sani ba?
Da gayya na tsare shi da ido ai sai Yallaban ka ya daburce yadda ya yi min kaÉ—an ya rage ban yi dariya ba.

"Rashin gaskiya kuma? Me kuwa zan yi miki ni Sadiya.?
A duburce ya ke mganar da ka ganshi za ka gane bashi da gaskiya sai na yi mirmishi kafin na ce" To na sani. Maza ai ba ku da gaskiya barin ma in kuka so ƙara auro."
Wallahi na hango tashin hankali ƙarara a idanuwan Yallabai mganta ya kashe masa jiki da ya sa ma ya kasa mgana.
Ni kuma saboda na kauda wannan firgicin ya sa na ce" Ranar Mandoy ina da komawa asibiti fa."

  "Allah ya kaimu. An gama duka gwaje gwajen ne?

Ina É—aukan wayata dake gefen in da na kwanta na ce" Saura É—aya."
Ina jin ajiyar zuciyarsa kafin ya ce" Allah ya kaimu."
Na amsa masa da Amin sai na fice ina faÉ—in" Ina falo."
Ban jira cewarsa ba na fice ina danne leɓena na ƙasa a raina ina tunanin to wai daman akwai irin wannan hanyar na cin uban maza da zullumi mata ke hauka? Ai wannan bakam ɗin kaɗai ya ishe su ba sai ka wahalar da bakin ka wajen faɗa ba.

Falon yara na koma na zauna sannan na kunna datar wayana. Duk da ina jin faɗuwar gaba ban fasa ba. Na kuma kasa iya sarrafa kaina sai da na je na ƙara duba sreenshoot ɗin da Ma'u ta turamin sannan na girgiza kaina na koma na duba status ɗin kaf yan gidansu Yallaɓai ban gani ba da gaske kenan sun ji roƙon sa? Ita kuma Anty Bahijja kamar yadda ta ce ne ta rufe ni ban gani ba.

Saƙon Munnira ne ya ɗau hankalina da ya sa na fara zargin ta san abin da ya faru.

"Matar Yallaɓai kina lafiya kuwa?

Haka ta rubuta mini sai na sha jinin jikina. To ni na ji ballatana ita? Ko mijinta bai faɗa mata ƴan'uwansa mata za su iya kirnnta ta su faɗa mata tunda an san muna tare. Na shiga na ba ta amsa da ina nan lafiya sai na fita ga waya a hannuna amma na kasa yin wani abu da ita ji na nake yi kamar ba ni ba, sai na ke jin kamar ba wancan Sadiya ba wannan Sadiyan da Yallaɓai ya gama shayar da ita mamaki ne.

Vibration É—in wayar a hannuna ne ya sa na dawo hayyacina sai na ga Marwa ce ke kirana. Da sauri na É—auka kamar a cikin wayar za a faÉ—a min abin da zai kwantar min da hankali.

"Marwa."

Na faÉ—a cikin sanyin murya.

"Umma ina kwana."

Nan muka gaisa na tambayi Yaya Aina da babanta ta ce duk suna lafiya.

"Umma kin ji ni shuru ban dawo ba ko?

Kafin na amsa mata ta cigaba da faÉ—in" Yau ne na je asibitin da zan yi pratical ne zaa kai report. Zan zo anjuma in sha Allahu."
Sai na amsa mata  da toh kafin na ce" Allah ya sa ba kaya kika zo ɗauka ba?
Tana dariya ta ce" Sai dai na zo Umma."
Na ce Allah ya kawo ta lafiya sannan muka yi sallama. A cikin raina na ke jin da gaske yanzu zan so ɗaukan Marwa ta dawo hannuna ina bukatar wani a gefe tunda yanzu Yallaɓai ya zama namu ba nawa ba.

Ban taɓa tunanin zan samu jarumtar iya faɗa ma wani Yallaɓai ya ƙara aure ba. Amma sai da na yi wani tunani sai na ga gwara ni a fara ji a bakina ina da tabbacin in na bari Ma'u ta yaɗa mganar nan kamar gazawata ce shi ya sa da hanzari na shiga group ɗin gidanmu na yi mgana.

"Assalamu Alaikum fatan mun tashi lafiya? Ya iyalai ya yarorin mu? Daman zan sanar da ku jiya an ɗaura ma Yallaɓai aure da yar'uwan sa Gimbiya(Saudatu) a garin Rano."

Na yi rubutu ya fi sau biyar ina gogewa kafin na yi dauriyan turawa ina gama turawa ya yi tickig ya ta fi na yi saurin kashe data na koma na jingina da jikin kujera ina maida numfashi.
  Mintina goma tsakani kawai na ji wayata da ke hannuna ta na vibration ina dubawa sai na ga Yaya Balki amma har ta katse ban ɗauka ba ta na katsewa kiran Rahila na shigo min itama nata na gamawa sai na ga na Amina.
Mirmishi kawai na yi na san suna so su ce min ne da gaske ne Sadiya?
Da gaske ne Sadiya? Nima tambayar da na ke yi ma kaina kenan shin wai da gaske ne Yallaɓai ya ƙara aure Sadiya? Amma har yanzu na kasa samun zuciyar da za ta ƙaryata wannan auran na Yallaɓai.
Wai daman haka kishi ya ke! In ko haka ya ke to tabbas Kishi ya na da ɗaci sannan na yi imani ga Allah ko ɗacin rashin wani makusancinka bai kai kishi ɗaci da maƙaƙi ba

Na daɗe ina kwatanta yanayin zafin shi. A yadda na ke kwatatanshi ban taɓa hasso shi a yadda na ji sa ba. Tabbas kishi kummallon mata na ƙara jinjina ma duk wata mace da a ka yi mata kishiya saboda ƙishi akwai zafi akwai ƙuna akwai ɗaci da radaɗi. Raɗaɗin da in ba akan ka ya faru ba labari ba zai iya gamsar da kai ba.

*Janafty*
*04 Wed. December 2025*
*TKD*

02.

Haka suka yi ta kirana amma na kasa iya jarumtar ɗaukar wayarsu. Sai na ke jin kamar da na amsa wayarsu suka fara jefemin tambaya da cewa shin da gaske ne Yallaɓai ne ya ƙara aure ? Na tabbata rauni ne zai zo ya yi min rumfa ɗan jarumta da na samu ya ƙwace min na saka kuka shi ya sa na kasa iya ɗaga wayar ko ɗaya daga cikin su.
Chapter 4 · 0% Book details