← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 89

Sashe 68

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me ya same ki? Me ta yi miki za ki zo har cikin gidan ta kina dukan ta? Kin san me kika yi?

Na yi tsaye ban yi masa mgana ba sai ya juya ya na duba Ma'u ya na yi mata sannu ya mikar da ita tsaye fuskarta ta yi ja da shatin hannayena idanuwanta sun yi ja sai kuka ni kuma ina kallonta ta na kuka ina ji a raina ba ta daku ba so na yi na yi mata dukan da ba za ta iya ma mgana ba.

"Sadiya me na yi miki!l? Ni ce fa Ma'u yar'uwan ki?

Sai na ji kamar ta jona min shoking a jikina a fusace na nuna ta da yatsa ina faÉ—in" Ke dai Ma'u ke dai Ma'u wallahi ke tsinanniya ce."
GabaÉ—ayansu suka zuba min ido, ita ko sai ta fashe da kuka ta na nuna kanta.

"Ni kike kira da tsinanniya Sadiya?

"Kin wuce tsinanniya. Ke sheÉ—aniya ce."

"Ya ishe ka haka fa Sadiya ina ganin girman ki"

A fusace na ce" Ka daina gani daga yau. Ba ruwan ka a wannan mganar ka matsa gefe ba dai kai na ke yi ba."

"Matata ce Asma'u ba ki da hurumin da za ki zo gidana kina tsine mata"

Sai na kalleta ta na ta kuka kamar mutuniyar ƙwarai kafin na nuna da yatsa ina faɗin" Ma'u Allah ya tsine miki albarka munafuka mai fuska biyu."

"Yar'uwan ki ce fa kike tsine mawa?

Ya faɗa ya na mai daka min tsawa, ni ma a fusacen a tsawacen na ce" Ni ba yar'uwta ba ce domin na raba jinin da ke tsakanina da ita har abada. Domin abin da ta yi min jinina ba zai taɓa yi shi ba. Kuma ki sani wallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da ke Ma'u."

Sai ya kasa mgana ya tsaya ya na kallona.

"Me ya faru?

"Ka tamnayi annamimiyar matar ka. Wacce ba ta ramin ta sai dai ramin wani."

Sai kawai ya fara lalubo waya daga cikin aljihun rigan shi lokaci É—aya ya na faÉ—in" Ni dai ban san me ya faru ba amma ba ri na kira Injiniya."
Megadi kuma megidan ya ce ya tafi abin shi amma ya daga can gefe ya na kallon abin da ke faruwa hankalin shi ya tafi ga kiran waya na shammace shi na ƙara yin kan Ma'u wannan karon ta so kare kanta sai muka fara ƙoƙowa amma duk da haka sai da cire mata ɗankwalin kanta na damƙi shegen gashinta mai kama da hammatan ɗan iska na fara ja sai ta fara ihu da gudu ya rugo ya shiga tsakaninmu burina kawai na bar ma Ma'u taɓon da duk lokacin da ta kalle shi sai na faɗo mata a rai shi ya sa na riƙa waige waige ina neman dutse ko sanda na rotsa mata kai dashi ta haka ne ya samu damar saka ta cikin mota ya rufe na ɗauko dutse da na gan shi a can gefen na rika bugun gilashin motar da shi, shi kuma ba ya son riƙe ni sai dai ya na ƙare wa kuma ya na kiran sunana da faɗin na shiga hankalina.

Ita kuma ta na cikin mota ta na kukan munafunci amma na ga lokacin da ta yi min wannan mirmishin nata ita a tunaninta ta yi nasara ne. Ƙarya ta ke yi ba ta yi nasara ba sai ma faɗuwa.

"Wallahi yau dubin ki ya cika Ma'u daga yau karshen ki ya zo domin sai na tabbatar da kowa ya san wacece ke. "

"Haƙuri koma me ya faru a zauna a tattauna?

Na kalle shi da jajayen idanuwana kafin na ce" Shari'a ce za ta shiga tsakanina da matarka."
Ina mgana ya na kiran waya sai ji na yi ya na cewa injiniya ga matarka a gida ta zo ta na jan Asma'u da faÉ—a ban san me ya ce masa ba na ji dai ya ce sai ya zo, ni kuma na kasa na tsare na ce ko ya fito da Ma'u ko na fasa gilashin motar ni na fito da ita.

"Haba Sadiya ki natsu mana "

"Yadda ta haifar min da rashin natsuwa. Nima wallahi sai na haifar mata da fiye da abin da ta yi min."

Shi dai ya babbage bakin mota ya na ta ba ni haƙuri domin ya ga yadda na ke a rikice zan iya aikata duk abin da na ga dama. Ɗamara na ci da mayafin jikina ina girgiza kamar zan yi bi iska shi fa ya tsorata ya ɗauka ina da aljanu ne har Ma'u ma ta tsorata kuma ta bugu domin har fuskarta ta kumbura, da dai na tuna in Yallabai ya zo zai hana ni ƙarisawa ofishin yan sanda ya sa na karɓi jakata da Alhaji Mustpha ke miƙamin tun ɗazu ban karɓa ba. Sai da na karɓa sannan na ce.

"Mu haÉ—u a gaban hukuma."

Ya biyo ni ya na ce min injiniya na hanya na yi banza ds shi megadi tun kafin na ƙarisobya buɗe min kofa ina fita sai ga motar Yallaɓai na karisowa ina ganin shi sai na juya na nufi bangaren yamma shi kuma da sauri har da gudu ya fito ya taka ya na bina lokaci ɗaya ya na kiran sunana Allah ya sa layin ma ba jama'a da mun zama ƴan kallo.

"Sadiya."

"Sadiya magana fa na ke yi miki. Ki tsaya don Allah."

Ban saurare shi ba sai da ya yi gudu ya sha gaba na, na kauce masa zan wuce ya riƙo ni da ƙarfi ya na kiran sunana.

"Ka ba ni hanya na wuce ko?

Na faÉ—a ina masa wani kallo da jajayen idanuwana da ina da tabbacin yanayin da ya ganni ya daÉ—e bai ganni a cikin sa ba.

"Ina za ki je? Kin ga yadda kike kuwa?

Sai da ya faɗa na kalli kaina da ɗamara. Kamar wata yar dambe sai na warware mayafin na yafa a kaina amma Yallaɓai ya ƙi sakina.

"Ka sake ni na ce ko?

Na faɗa a fusace ina kuma ƙokarin kwace kaina amma riƙon Yallaɓai ba na wasa ba ne na kasa.

"In na sake ki ina za ki je?

"Offishin yan sanda."

Na bashi amsa ina huci kafin na cigaba da faɗin"Wallahi ba zan ƙyale duk wanda ya nemi ya tozartani ba. Sai hukuma ta bi min kadin kazafin da suka yi min ni da zuru'ata."
Na karishe faÉ—a ina fashewa da kuka sai ya rike ni a jikinsa amma ina ta fizgewa ina faÉ—in ya sake ni domin ni ba zan bar wannan mganar ba.

"Na ji nima ai ban ce ki barta ba. Mu je ki shiga mota sai mu je police station É—in tare da ke."

Sai na kalle shi sai ya gyaɗa min kai ya na ƙara rike duka hannuwana ya na jinjina min kai, ban san me ya sa na yarda da shi ba na bi shi zalau zalau har bakin mota ya buɗe ya sakani a ciki ya rufe sannan ya taka ya isa bakin get ɗin gidan Alhaji Mustapha bai shiga ba amma shi ya leƙo sun yi mgana ba daɗewa ya dawo ya buɗe mota ya shiga ya ta da ita ya yi riverse muka bar layin tun da muka fara tafiya na ke kuka kuma da karfi ina yi har da jiniya bai kuma hana ni kukan ba.

"Ni Ma'u za ta tozarta? Ni yayarka za ta kalli idanuwana ta ce dangin uwata dangin asiri ne?

"Ki yi hakuri"

Yallabai ya faÉ—a a marairaice, ga shi sai kiran wayarsa ake yi bai É—auka ba.

"Yusuf lokacin da ka ce min matarka za ta zo ta zauna da mu me na faÉ—a maka? Ba sai da na ce ina tsoron wani abu kar ya faru daga baya ba!
To yau ni matarka ta saka ma da sharri sakamakon alherin da na yi mata. Ita wai ta ce ta na gidan kanwar mamana ta kawo min asiri. Ita ce fa ta faɗi haka Yallaɓai"

Na ƙarishe faɗa ina kallon shi ina kuka har da majina.

"Ita Saudatun ne ta ce haka?

Ya tambaya cikin mamaki.

"Abin da ya fi min ciwo Anty Bahijja ta zubar da abincin da na kawo ma Nene ta ce ba zan kashe muku uwa kamar yadda na so na zubar ma da Gimbiya cikin jikinta? Yusuf a zama na da kai na taɓa kwatanta wani abu na cutarwa gareka ko yan'uwan ka?

"Ba ki taɓa ba Sadiya"

"Na taɓa zagin su! Na taba musu wani abu na rashin ɗa'a? Tsakaninmu sai girmamawa amma yau duk alherin zaman shekarun aurena da kai ya koma na sharri da ƙazafi?

"Ki daina kuka don Allah Sadiya raina na ƙara ɓaci."

Ya faɗa cikin wani yanayi ya na kuma gudu a mota sosai daga gani ran shi ya na ɓace ne.

"Yusuf yau fa Anty Bahijja ta ce min ba ta ga abin da aurena da kai ya tsinana maka ba. Ta ce wai na wanke gaba na baka ka sha na mallake ka, shi ya sa na shiga na fita zan liƙa ma Kawu Abba ɗiyar yayata saboda shima a maida shi shanyayye kamar ka."

"To ina ruwanta in kin shanye ni? Sannan uban wa ya faÉ—a musu labarin Kawu da Marwa."

In kuka na ce" Munafuka Ma'u ce, shi yasa na ce maka sai na haÉ—a su da hukuma"

"Ban É—auka haka ta ke ba. Ma'u nan ta ba ni mamaki ".

Ya faÉ—a cikin bacin rai kafin ya cigaba da faÉ—in" Me ya sa na ki kirani da abin ya faru ba? Kin san dai ba zan zura idi a ci miki mutumci ba. Duk wanda ya ci miki mutumci to tamkar nawa mutumci ya ci."
.
Na kasa mgana sai kuka kawai na ke yi ina faÉ—in ya kai ni offishin yan sanda.

"Ki yi hakuri mu koma gida a zauna a yi mgana."

A fusace na ce" Ba zan zauna da kowa ba Yusuf hukuma ce za ta tuhume su."

"A'a."

"To ka sauke ni na tari adaidaita"

"Na ce a'a."

Ya faɗa a fusace cikin tsawa, kamar zai dake ni daga gani ran maza ya ɓaci.
Chapter 68 · 0% Book details