← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 94

Sashe 93

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 5 min read

Fadin"Bana Bukatar Abincinki.Tunda kema bazaki ba ba sai kin gayyatomin wata ba..Ai nasan da ita nace ke din ko..?gud dukkanku ku sha Zamanku..Nagode..! Daga Haka ya Figi Key din Motarsa ya Duka yayi ma Mansur karami Kiss wanda ke Barci ya Fice Rumana ta Bishi da Sauri Tana Bashi Hakuri bai Tssya Sauraranta ba Suna Fitowa sai ga Diza ta Fito Itama Cikin Shirinta Harda Trolley dinta agabanta Komai ya Faru ya Shige Motarsa Bayan ya saka Jakarsa yayi Hon megadi ya wangalemai get ya Fice abunsa,Rumana sai taji bata ji Dadi ba Diza kuwa Daman ta Dai Shirya ne ammh,Tasan hakan zata Faru Dukkansu ba wacce Tayi ma yar"uwanta mgana kowacce ta Shige Shashenta Cikin Sanyin Jiki. Rumana tayi ta kiran Wayar Mastur yaki Dagawa Har Washegari bai Daga kiranta ba Daga karshe ma sai ya kashe wayarsa Ita kadai ta yanke wani Shawara tace Diza ta Shirya kwana daBiyu ta Tafiyarsa,Kaduna sukaje Da Cuku cuku da komai Diza ta samu Jirgi zuwa Porthercourt,Diza Tayi ta mamakin Rumana sai da taji Taruwan Hawaye Daman tace mata Tazo da Shirinta ammh batace mata ga inda Zata ba..Bata bar kaduna ba sai da Jirginsu Diza ya Daga bayan ta Jadadda mata bayan sun Sauka ta Kira Mastur ta gayamai Tana Filin Jirgi ta Tabbata bazai kyaleta Daga karshe ta bata Shawaran ta bashi Hakuri ita kuma in ya Dawo sai su karishe dashi,ita da Mansur Karami ne Dare yayi mata sai ta Biya Gidansu Basma ta kwana Bayan ta Kira Mommy ta Fadamata Ta Rako Diza kaduna gata zata kwana Gidansu Basma. Mommy tayi mamakin jin Diza ta Bi Mastur alhalin shi yace da Rumana zai tafi ganin Rumanan bata mata wani bayani ba yasa Mommy bata nemi taji ba"asi ba. Bangaran Diza kuwa sai Bayan mangariba ta sauka a Porthercourt,Saboda Jirgin bai taso da Wuri ba Tana Sauka ta Kira Mastur sai da tayi mai kira Biyar ajere kana ya Daga Daman Yaga Text din Rumana ta Fadamai Diza na Hanya bai yi mamaki b Illah Jinjina Karamcin Rumana da yayi Yana Dagawa yace mata Sargent Inuwa zai zo yanzu ya Dauketa. Haka kuwa akayi shi yazo ya Dauketa Har Heaquater su acikin Gidan da ya zama mallakin Mastur shi din yana wajen aiki bai Taso ba Diza wannan ne zuwanta karo na Farko,Ammh Duk da Haka bata zauna ba Tayi amfani da Shawaran Rumana ta Zage ta Fara Tsabatace gidan ta Saka Turaran Kamshi Daganan ta Fada Kitchen akwai komai na Cefane, tayi Girki mai rai da Lafiya Bayan tagama ta Fada Bedroom dinsa Inda Tayi ma kanta Muhalli tashiga wanka taxo ta Tsantsara kwalliya Cikin wata Arniyar Rigar barci wacce bata Boye komai ba kuma tayi ma kanta wankan Turaran Humra mai kamshi Sai 11pm Mastur ya Shigo Gidan ya Zata ma Diza ta kwanta Ya shigo mata da Takeway,Sai dai kuma ya Tarar da gidan Cikin Ni"ima kamshin Turaran Daki Dana Abinci na Tashi bai gama mamaki ba sai da Diza ta bayyana agabansa Duk Dauriyan Mastur kasa Dauke ido Yayi Daga kanta ganin Tarkonta ya kama yasa ta Fada Jikinsa Tana kukan Shagwaba Lokaci Daya tana Bashi Hakuri bai ki karbanta ba Haka ya Zubar da Abunda ya Shigo Dashi ya Chachumeta zuwa Cikin Daki suka Fada kan gado Daganan zencen yasha Bambam da sunan Hukuncin Dayake Bama Diza na Laifin data aikatamai sai da suka ntsa sukayi wanka suka Fito Cin Abinci Shi yayi Feeding dinta itama tayi nashi Bayanan kuma aka sake Kwakwuman junan Mastur yana ta Famshen Bashin da Diza taci. Sai Washegari da Mastur yaje Office Ya kira Rumana yana Mata Fada ita dai Hakuri kawai ta bashi Shima din ma Taku ne irin na Maza ammh wane shi yaki Godema Rumana kan wannan alfarman Datayi mai..? Ya saka mata albarka yafi Cikin Botiki. Tunda ga Lokacin komai ya Daidaita wani Sabon Honey moon ne Diza da Mastur suka Bude a porthercourt,Daman ba wanda ya san ya kara aure sai Sargent Inuwa shine ma yake Fada musu ganin Dizan da Mastur suna Fita yawom Shaqatawa da yammah ko da Dadaddare yanzu su Yallabai an Daina kaiwa Dare a office an samu wajen Hutawa Yan sandan Dake kasansa suna ta Gulmansa,Ganin yanzu ya Daina Cika ma kansa aiki kamar baya Tunda ya Samu Diza a kusa Dashi,Rumana suna yawa dasu sosai koda yaushe ta Fara zuwa Makaranta sai take barin ma Hajja Mansur karami in ta taso Taje ta Daukesa su dawo gida shi ke Debemata kewa shi kanshi yasan waya in Mastur ya kira yayi ta Tsalle yana mai gauranci bai Damu da wata Diza ba itama sai take ma Rumana kara. Wannan Tafiyan Mastur yadan Jima sai da ya kusa wata Biyu kana suka Dawo Dukkansu sun Sauya sunyi Kiba Dagashi Har Diza,ita Har da Tsaraban Cikin Porthercourt wanda ta dawo Dashi ba wanda ya sani sai da yayi Sati Daya ya koma Shi kadai Bayan Tafiyarshi Diza ta Fara Laulayi Har da su kwanciya asibiti Dole ta koma gida Wajen Mommy Tunda Rumana na zuwa makaranta Farinciki wajen Mastur da Rumana ba"a mgana ashe itama tana Makale da nata ba wanda ya sani sai ranar a makaranta ta Fadi ana gwadata itama sai ga Ciki da Mastur ya samu Labari kamar ance ya Shiga Aljannah bai iya zama ba sai da ya Tattaro ya zo ya yi jinyar Matan nashi da kansa Mardiya sai ta Dawo nan tana Taimaka musu Sati Daya yayi ya koma Lokacin sun warware har Rumana ta Cigaba da zuwa makarantar ta Diza kuma bata zuwa Ko'ina Cikinta yafi na Rumana Laulayi Catering dinta sai ta ga Dama ta leka komai Tana Gudanar dashi ta wayanta. Iyaye da yan"uwa kowa sai taya Mastur Murna yake kyautan Allah a lokaci Daya Alhamdulillah Umma da Abba suma sai son barka zasu samu Jika akaro na Farko.
Chapter 93 · 0% Book details