← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 94

Sashe 65

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumana ita ta shiga Kitchen din Diza ta Dauko musu Babban Filet ta Bare musu alalan Ta saka musu Yaji ta kalli Diza Dake kan kujera tace"Ko zaki sauko ne muci kamar kasan zai fi mana Dadin Zama.."Diza ta ijiye wayar dake Hannunta Tana Fadin"Wlh kuwa zai fi Dadin ci..Balle ga yaji kana ci kana jan Yajin ka.."Ta karishe Fada tana yar Dariya Lokaci Daya tana Saukowa kasa Rumana ta mike Tana Fadin"Kin Tuna min bari na Dauko mana Ruwa.."Diza tace"Kai..Hanzarta
."Frigde din dake Falon Rumana ta Bude ta Dauko musu Goran Ruwa guda Biyu masu sanyi tazo ta ijiye ta koma Kitchen ta Dauko kananan kofuna tazo ta ijiye kana ta Zauna sukayi Bismillah suka Fara cin abinci ba wanda yayi mgana.
Chan Diza Data Tauna Alalan a bakinta tace"Uhm..Kai gaskiya Alalen nan yayi Dadi ban taba cin Alalan Dayayi min Dadi irinsa ba.."
Rumana na Dariya tace"Allah ko..?Kodai na saka miki waigi ne..!
Diza na Dariya tace"Bafa santi ne..Ina dai Fatan akwai Ragowa Domin ni anjuma shi zan ci.."Rumana tace"Akwai Har mai girma Honourble ma zai samu.."Diza tace"Daya saka miki albarka..Yana son Alale Koyaushe yana Min gorin ban taba mai Alale ba.."
Rumana tace"Su gori manya..Ina Ruwan Mansur.."
Diza ta gama Shan ruwa tace"Wai ni kam nace Ya Mastur Laifin me nayi mai..? Ko awaya bai kirani ba.."Rumana Tace"Kinsan baida Aikun kiran waya fa..Sai dai yayi mgana ma Mansur kema kin sani.."Diza tace"Daman mana..Rashin zaman Mansur ne kila da kinji Zencen sunyi waya yana gaisheni abakinsa.."Rumana tace"Eh kam haka din ne.."
Daganan basu kara mgana ba Har sai da suka gama cin Abincin Diza tayi Gyatsa da Hamdala Tana Fadin"Alhamdulillah..Naci na Koshi..Allah yasa kar nayi amai..'Tafada Cikin Bayyana Damuwa.

Rumana tace"Kada kidamu insha Allahu bazaki yi Amai ba.."Diza tace"Allah yasa hakan"Daganan Rumana ta Tattara abunda suka Bata zuwa Kitchen,ta Dawo Diza na zaune nan kasa Ta rasa ta ina Zata Fara ma Rumana mgana sai da Taga tana Shirin saka Mayafi kana takalleta Tana Fadin"Wai har zaki Tafi..?
Rumana tace"Wlh..karatu zan je nayi..Gobe Seminar gareni Shiyasa.."

Diza ta kada kai Tana Fadin"Da kuma mgana nake son nayi Dake in bazaki Damu ba.."Rumana ta Tsaya Bayan ta saka mayafinta Lokaci Daya ta koma ta Zauna Tana Fadin"Bakomai ina jinki.."Diza ta Dukar dakai ta rasa Ta ina zata Fara Dakyar tayi karfin Halin Fara fadin"Daman Hakuri zan baki Rumana kan abubuwan da sukayi ta Faruwa Tun Farkon zaman mu acikin Gidanan Don Allah ki yafemin Rashin Fahimtane Abunda ya Faru Ranar nan kiyi Hakuri komai ya wuce hakan bazai kara Faruwa ba..!
Diza ta karishe Fada tana wasa da Zoben Hannunta ita kuma Rumana sai Mirmishi Take yi Cikin Jin Dadi ta tashi ta karisa ga Diza ta Durkusa ta Dafa Kafadarta Tana Fadin'"Haba Diza..Miye na bani Hakuri ai bakomai zaman tare daman yagaji haka..Naji Dadi kwarai Insha Allahu komai ya wuce..Allah ya zaunar damu Lafiya..ke kuma Allah ya kara Miki Lafiya ya kuma Sauke mana ke Lafiya musha Shagali.."
Ta karishe Fada Tana Dariya Diza Taji kunya ta Sunne kai Tana amsawa da Ameen Ameen.
Daganan Rumana ta Koma Shashenta bayan ta barma Diza Sauran Alalan Data zo Dashi tace taci da Daddare sauran Kuma ta Rage ma Mansur Dizan Tayi ta Godiya..
Ita kuwa Rumana Tayi Farimcikin wannan Daidaitawar tasu ita da Diza ko bakomai Shi Zaman lafiya wani abu ne,mai matukar amfani bata da Damuwa game da Mastur Domin ta Tattarashi ta watsashi gefe Daya,ta Dauki auranta Dashi a mtsayin wata kaddara Ta rayuwarta wanda bazata iya Tsallake hakan ba.

Diza kuwa Kin yin barci Tayi saboda Tana son yau tayi mgana da Mansur yasa taki kwanciya Barci,Sai Allah ya taimaketa ya Dawo da wuri,Around 9pm koda ya Shigo yayi mamakin ganinta a Falo zaune kan kujera Tana kallo Lokaci Daya kuma wayace a Hannunta Tana Sarrafata duk don Saboda kada barci ya Dauketa.
Sanye take da wani Wando mai kama da plazo sai wata Shirt mai Ruwan Zuma Data lame ajikinta kanta ba Dankwali ta kama gashunta a tsakiyar kanta ssi Baza kamshin Turare take Zubawa kuma Duka adon yau tayi Shi Saboda Mansur ne Abunda bata Taba mai ba.

Da mamaki ya karisa gareta Lokaci Daya yana Sabule Babbar Rigar Shaddar dake jikinsa Tare suka isa ga Jikin juna itama Mikewa Tayi ta tarbeshi Fuskarta ya Tallafa da Hannaye Biyu yana mai kura mata ido kafin yace"My Firstlady..Meyasa Har yanzu baki kwanta ba kuma kinsan Yanayin da ki ke ciki ko ?
Lumshe ido Tayi ta Bude kafin tace"Taya zan iya Barci Alhalin kana Fushi dani..?
Ido ya Zuramata kafin yace"Ni bana Fushi Dake Matata..!
Wani Sanyi Taji yana Ratsata Wanda bata san Lokacin data kwantar da kanta Saman kirjinsa Tana Sauke Numfashi ba Abun ya bashi mamaki sai Jikinsa ya saki ya Tallabeta zuwa Jikinsa Yana Fadin"Kinyi sallah..? Kinci Abinci..,?
Kanta na saman Kirjinta tace"Nayi Sallah kuma..Naci na koshi..Rumana Tayi mana alale mai Dadi shi naci da Rana har daranan..."Cikin mamaki ya Dagota yana Fadin"Rumana kuma..? Kai ta gyada mai Tana Fadin"Eh..Kaima ta ijiye Maka naka.."Yana so ya Tambayeta sai kuma ya fasa ya Tallafeta Zuwa Cikin Bedroom dinsu kan gado ya Zaunar da ita yana Fadin"Nagaji..Bari naje nayi wanka...Duk da na Biya wajen Hajja naci Tuwo zan ci Alalan nan Tunda naga kina Santi nasan yayi Dadi sosai.."
Tana kallonsa batayi mgana ba har ya Ture kofar Tiolet ya Shige ya barta nan zaune kawai sai Taji Hawaye ya cikamata ido da Tsausayin Mansur ta Godema Allah Data gane gaskiya da Wuri kafin Lokaci ya kure mata data mutu Cikin wannan Halin batasn me zata gayama Allah ba.

Har Mansur ya Fito bata sani ba Sai da taji Dumin Ruwan Wankansa Saman Fuskarta yana Share mata Hawaye Tana Bude ido ta gansa Durkushe saman Gwiwoyinsa agabanta Yana Dafe da Cinyoyinta Cikin wani yanayi ganinta Tana Hawaye yace"Meya Faru ne Naga Hawaye a Fuskar Firstladyta..?yafada yana Bayyana Damuwarsa Kura mai Ido Tayi Cikin wani yanayi kafin taji kukanta ya karu kawai sai ta sakamai kuka nan da nan ya Rude ya mike ya Tarairayota Jikinsa yana Tambayanta ki me ya Faru..? Kasa mgana Tayi saboda bata san ta ina Zata Fara ba Kawai sai ta samu kanta da Fadin"Don Allah kayi hakuri ka yafemin..Duk Abunda ya Faru ba Laifi na bane..Wlh bansani ba.."Ta karishe fada Tana gunjin kuka kamar Zata Shide Dagota yayi Daga Jikinsa Cikin Rawan jiki yake share mata Hawaye yana Fadin"Wlh banta Rike ki da wani Laifi ba Diza..Na Dade da yafemiki Duka Laifin da kikamin da wanda ma zaki min nan gaba Diza..Ina sonki soyayyar da Bansan yaushe ta Fara ba..Kuma bansan Ranar da zata yanke ba kila sai Ranar da na Daina Numfashi Diza..'Ya karishe Fada cikin Sanyin murya da karaya Da Sauri Diza ta Dago tana kallonsa Cikin Zubar kwallah Kafin ta samu Zarafin mgana taji yace"Ko da bazaki Taba sona ba Diza..Ni na yarda nacigaba da sonka Har karshen Numfashina.."Da wani irin Gudu ta Fada Jikinsa ta kamkameshi Cikin kuka take Fadin"A"a..Nima Wlh INA SONKA...'!Ina sonka...! Tafada cikin gunjin kuka da Sauri ya Dagota yana Girgirzata cikin mamakin kalamanta yace"Da gaske kike Diza kin Daina son Ya Mastur ni kike so..? Ya tambayeta Cikin Wani irin Rauni da muradi mai girma.

Cikin Zubar kwallah idanuwanta na Runtse tace"Wata irin Matace ne da zan rika Begen wanda ya Haramta gareni..? Wata irin Bakar Zuciya gareni da zan juyama wanda ke sona da Duk Zuciyarsa baya..?Bani da wannan karfin gwiwan Mansur Wlh ina sonka..Ina kaunarka da Duka Zuciyata.."Cikin wani irin azama ya Dora Bakinsa kan bakinta nan nan da ta Bashi Dama ta Hanyar Budemai bakinta ta Cafki Harshensa suka Fara bama Junansu Sumba mai Tsawo Cikin Muradi da kauna Alokacin Diza ta Rude Madamai martani kawai Take ita ta karbi Ragamar abun Sai Mansur ya koma dan kallo Haka ta Rika Sarrafashi Har suka samu Natsuwa Mansur ya Gigice sosai Yana ma Diza kuka da idanuwansa yana Fadin kada ta barshi in ta barshi Zai iya Mutuwa itace Rayuwarsa,Karo na Farko Tun Bayan Auransu da Diza Tataba Bashi Hadin kai 100%shiyasa abun yazo mai cikin wani yanayin da bai Taba Zato ba.
Tare sukayi wanka Suna yi suna kara Tabbatar da soyayyar junansu bayan sun yi wankar Tsarki suka Fito suka shirya Cikin Kayan barci kana Diza ta gabatarmai da Alalansa suka taru sukaci Cikin Soyayya da kaunar da suka Tsinci kansu acikinta.

Awannan Daran Dare ne Masu Daraja da Tsada wajen Diza da Mansur domin tafi Daran Farkonsu Dare ne msi Cike da muradi da soyayya wanda suka kwana yima juna alkwarurruka da Sadaukarwa mai Tarin yawa Har garin Allah ya waye Dokin junansu bai sake su ba Ranar Mansur bai iya Fita ko kofar Gida ba Duka ya Kashe wayoyinsa yana Enjoying din Sabuwar Duniya da Diza ta Rika Tafiya Dashi Har Abada bazai Taba juyama wannan Sabon al"amarin Baya ba.

*Shakira...*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS...30*

*Kibiya ki karanta Cikin Salama 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran Abun sata*

*2 Month Later*

"Abubuwa Dadama sun Faru ayadda kowa yake so Domin a wannan Lokacin Zaman Diza da Rumana sai dai ace son Barka sun Hade kansu Tamkar wata Baraka bata taba Shiga Tsakaninsu ba Dama Diza ce Mtsalan kuma yanzu ta Zubar da makamanta.
Mansur yafi kowa jin Dadin haka sai Mommy da mardiya da yanzu Take jin Dadin zuwa gidan Fiye da Baya,in yau suka wuni Shashen Diza gobe Shashin Rumana zasu wuni indai Rumana na Gida girki kuma indai Tana nan ita take musu Gabadaya bata barin Diza Tayi wani aikin Wahala saboda Cikin Jikinta da yanzu yake Cikin Watansa na Biyar har ya Fito Dayake Diza Zatayi Girman Ciki.

Mastur yazo gida yayi Sati Biyu ya koma sai dai wannan zuwan Shima abubuwa sun Fara Daidaita Sanadin zuwan nashi Baba Habibu ne ya samu Hatsari akan Hanyarsa ta Dawowa Gida Mota taTureshi yaji Raunika sosai sai dai Ba karaya asibitin Abu Tudun wada suka kaishi,Washegarin Ranar Bayan Mastur yaji Labari ya Hayo Jirgi ya Taho hankalinsa yayi matukar Tashi Dawowarsa ne yasa ya Sauya ma Baba Habibu asibiti Zuwa ABU chika Dake Samaru.
Chapter 65 · 0% Book details