← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 94

Sashe 51

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da Tagama mganarta Kana ya kada kai ya Shige Dakin ya maida Kofa Batare da yayi mata Wata mgana ba Komawa tayi ta Zauna Aranta Tana ayyyana Haka Matan Miskilai suke Fama Bata sani ba Allah ya gani itama Miskila ce Mara son Hayaniya ammh Mastur ya Damata ya Shanyeta.
Ita dai bata kara jin Motsinsa ba Har tagaji da kallon Bayan ta Cinye Abunda ta zubo ta,koma Daki ta Dauki Novel dinta tacigaba da karantawa wayar Umma ce ma ta Katseta inda take gayamata Auwalu har ya kamo Hanya nan ma take gayamata Mommy ta Kirata Tana ta yi mata Godiya ita da Hajja ashe Hardasu ta aiko ma Sakon Bata sani ba Umma Har kara Tambayanta Tayi ta Aiko ma da Diza nata Sakon Tace eh Ammh Bata yarda Ta gayamata Yadda Diza Ta karbi Sakon ba Har sukayi Sallama.
Batayi Gigin komawa Shashen Diza ba ta riga ta Daukan ma kanta alkawarin kama Girmanta Insha Allahu ai tana gaba da ita ba ita ya kamata ta Dinga Binta ba Ita ya kamata ta Bita ammh Ko Kofar Shashenta ai Bata taba Takowa ba sai ita Datake ijiye Girmanta Tana Binta Tanamata Wulakanci Bazata Dauka ba ta Riga Tagama Daukan iya Abunda Zata iya Dauka.

Tana Dakinta Taji Fitar Mastur Bai Dawo ba sai Da Daddare Shi da Mansur suka Shigo Mansur yaShigo Da kayan Cefane Leda Leda yakai Kitchen Lokacin Tana Dakinta Ta Idar da Sallar Isha"i Tana Ji Mansur na Tambayanta Taki Fitowa Domin Batasan mgana ba Sai da tajiShuru alaman ya Fita kana ta Fito Kitchen din Ta Shiga Taga Ledoji Ta Duba Taga su Kwai ne da Dankalin Turawa sai kayan Miya sai Su Cabej green beans,Carrot da Sauran Kayan Girki nan da nan ta Cicciresu a ledata Sakasu Cikin Babban Fridge din Dake Kitchen din Taga ma Harda Nama daKifi ya Siyo Karamin Fridge din kuma kayan Sanyi ne aciki Bayan Tagama ta gyara Kichen din Ta kai Dattin Dusbin din Dake Wajen kana ta Fito Falo nan Taga Mastur Zaune wannan karon yana aiki Bisa System Dinsa ne Gaisheshi Tayi ya amsa da Lafiya lau Daganan ya Cigaba da aikinsa Dakinta takoma Tayi Shirin Barci Domin Tagaji yau ko Barcin Rana bata samu Damar yiba Tana kwanciya kuma sai Barci.

Washegari ta kama Lahadi Rumana Tatashi da Shiryan Shiryan ZUwa wajen aiki Gobe Shiyasa Take Cikin Farinciki Ta gama Shirya kayanta Duka acikin Wardropr Tun Safe Bayan Ta gama Hada Breakfast Ruwan Tea ta Dafa sai Buredi da kwai sai Plantai Kan Dinnig ta Jera komai Bayan Tagama cin nata ita dai ta Fita Hakkinsa koda bazai ci ba Mommy kuma Ita da kanta ta Kirata awaya bayan sun gaisa tace mata Ta bar kawo musu Abinci Hakanan Zata dinga girkawa da kanta Mommy tace Har Zata Fara Girki Da Sauri haka..!? Rumana tace bakomai Tana so Ta Dinga yi Da kanta Mommy Taji Dadin Tunanin Rumanan tace Shikenan Hakan Nada kyau Daganan sukayi Sallama Mommy Tana Sha"awar Rumana yarinya ce mai kwazo Ta kowani Fanni Diza sunyi mgana Tace Mansur yayo Cefane Itama Tana so taFara Girki Hamdala Tayi ma Sarki Allah Tare da Fatan Zaman Lafiya aTsakanin Ma"auratan Har Gaban Abada.

Bata san yaushe ya Fito Har ya Sha Tea din ba,Sai Plantain din Taga yaci kadan Mamaki ya kamata Bata Taba Zaton Zai Taba wanu abu ba Kwashe komai Tayi ta maida Kitchen tayi wanke wanke wani Karsashi take Ci Gre ing din Kayan Miya Tayi Ta Dora Girki Farar Shinkafa Miyar Kifa Tayi Cikin kayan da Ummata Aiko mata akwai Kayan Hadim Lemuka sai ta Hada Lemon kankana Ta saka a Fridge,Sai ta gyara Kitchen din kana taje Tayi wanka Tayi sallah Tazo Taci Abincin Tagama kenan sai ga Mastur ya Fito Cikin Shirin Fita Sanye Cikin Riga da wando Black and White Na kamfanin Armani Sai key din Motarsa Dake Hannunsa Rankwafawa Tayi ta Gaisheshi ya amsa yana kallonta Tashi Tayi Daga Saman kujeran Dinning din Tana Tattara Filet din Dataci Abinci dashi Kai Tsaye Taji yace"Anjuma ki Shirya zamu je Ki gaida su Hajja.."

Daga Haka kawai ya kada kai ya Fice Da kallo ta Bisa kafin ta gyada kai kawai ta wuce Kitchen Yanzu kam ta Daina Damuwa da Sha"anin Mastur,Ta Fahimci ya Wuce yadda Take Tunani
Abunda  ke bata mamaki Bashi yaje ya Nemi Auranta da kansa ba..? Ko kuwa Domin ta Fara Bayyanamai Sirrin Zuciyarta ne ta Chanchanci haka ita dai ta kasa Gane masa,Bayan Fitarsa Sai Tayi Tunanin Ta Diban mai Dambun Naman nan yaTafi Dashi pepe din kuma tasaka Cikin Fridge kada ya Lalace Wata Karamar Roba Ta samu ta Diban mai Tayi Rapping dinsi sai kuma taFara Tunanin bazata je Gaidasu Hajja Hakanan ba Ta samu Leda TaDiban musu Cincin da Cake da Donut mai yawan gaskiya,Pepe chicken din ma Ta Diban musu Fin Rabi Saboda kada ta barshi ya Lalace Tun kafin Mangariba tayiwanka Ta Shirya Tana Jiran Mastur ammh bai Dawo ba Mansur Baya nan Saboda Tun Safe Taji Tashin Mota Kodata Leka sai Taga Shine Ammh Taji Hayaniya Daga Shashen Diza Kila Tayi Baki ne,Zaune take afalo Tana kallo Har aka Kira Sallar Mangariba ta Shiga Ciki Ta idar da Sallah kenan Taji Shigowar Mota Ammh Bata ji Bude Kofar Shashenta ba Mastur yana da key Da yazo Zai Bude sai Zuwa Chan Taji Bude Kofarsa da Shigowarsa ya Shiga Dakinsa Daganan bata kara Jin Motsinsa ba Bayan kamar Minti Talatin Taji karan Wayarta Dake kan gado Mikewa Tayi ta Dauketa sai Taga Mastur ne Tana Dagawa Taji yace"Ki Fito mu Tafi.."
Daga Haka ya yanke Kiran Ajiyar rau ta Sauke kafin Ta ijiye wayar Hijabin Datayi Salla Dashi taCire ta Dauki Mayafin Leshin Dake Jikinta Kalan Golden ta Saka ta Dauki Karamar Jakarta ta Tusa wayarta Sai Flat Shoe din Data Saka ta Fito Batayi kwalliya ba Hoda kadai ta saka sai Lipstick Tana Fitowa ta Iskeshi Tsye yaJuya Baya yana Waya yana Sanye da Wata Shadda Sky Blue Dinkin Riga da wando na Zamani da Hula Kafarsa Sanye Cikin Wani Bakin Budadden Takalmi mai kyau da Tsari Ta manta da Sakonta Ta zo Gabansa Ta Tsaya Har ya gama wayar bai mata mgana ba kuma bai kalleta ba ya Wuceta Harta Fara Taku Zata Bishi ta Tuna da Abunda Zata kaima Hajja da Mommy sai ta Juya Waigowa yayi kawai yaga Bata Bayansa Cikin mamakin Ina Taje yake karema Falon kallo Sai Gata Ta Fito Daga Kichen din da leda Dakinta ta kara Shiga ta Dauko Atamfofi Guda2 din Data saka aciki Sai Kayan Kwalliya irin su Tiraran Wuta Dana Daki Wanda Zata kaima Mommy Atamfofin kuma na Hajja ne da Ayya Umma tace duk SandaZataje kada taje Hannu Rabbana ita kuma sai ta Hada musu da Zannuwa Mommy kuma tasan ko ta bata ba karba Zatayi ba Shiyasa Zata bata Turaran.
Mamaki ya kamashi Daya ganta da Leda kamar zai mata mgana sai kuma ya Fasa Shi ya Fara fitasai ita Suna Fitowa ya saka key ya Kulle Kofar Apartment din nasu Har ta Tatafi Wajen Motarsa Wacce Tata ke kusa Da nashi Taga Shi bai Taho ba Tana waigowa Taga yana Waya ne Sai Taji yana Fadin"Muna Haraba Mansur.."Sai abunda ya bata mamaki kenan Tafiyar basu kadai bane Tabbas Mansur ne ma ya Tsara ya kamata su kai su Gida su gaidasu Hajja dasu Mommy Tunda Gobe Shi Mastur Zai Koma Porthercourt Mansur Gobe Jirgi Zai Bi Zuwa Abuja Suna da wani Taro Dalilin Daya sa Mastur yace ma Rumana ta Shirya kenan.

Bata gama mamaki ba Sai ga Mansur ya Fito Shima Cikin Shigan Shadda mai Ruwan kasa Harda Hula Hannayensu Rike da Juna Shida Diza Taji Ubansu Gayu kamar Zata gasan kyau Wata Atamfa ta Saka Doguwar Riga mai kyau da yarari da gyalejta da Jakarta da Takalminta mai Tudu,Mansur ya Kulle Suma Kofar Shashensu kafin su kariso Mansur na Fadin"Yaya ayi Hakuri..Mun barku kuna Jira.."

Mastur dai bai ce komai ba kansa ya Kauda Domin baya son ganin Diza ita kuwa Shi take kallo Kafin ta isa Gabansa Rumana ce Takegaisawa da Mansur Diza kuma Sai da tazo Gaban Mastur kana Tace"Ina yini ya Mastur..! Cikin sanyin Murya Duk yadda yakai ga Dauriyansa sai da yaji Wannan muryan Har tsakar kansa Batare Daya kara mata wani kyakyawan kallo ba Yace"Lafiya.."Daga haka ya Wuceta Zuwa Motar Mansur wanda Har ya Shiga Mazaunin Direba,Shima Gaban ya Bude ya Shiga yana Kokuwa da Numfaahinsa Mansur ne ya Leko Yana Fadin"Bismillanku ku shigo mu Tafi.."Rumana Ce tayi Kokarin Tasowa Itama Diza ta kawo Sai suka Hade kallon kallon Sukayi ma Juna kafin Rumana ta Murmusa Tana Fadin"Diza ya Jikin naki..? Wlh Diza sai ta kauda kanta kawai ta Bude Murfin Mota ta Shiga Rumana bata Damu ba ta Zagaya itama ta Bude taShiga da Sallama Mansur kadai ya amsa Banda Diza da Mastur wanda ko sun amsa itadai bataji ba Ribas Mansur yayi Lokaci Daya da Hon Megadi ya wangale get din suka Fice Daga Gidan Yana Binsu da Fatan Dawowa Lafiya.

*ki biya ki karanta cikin Salama 09069067488*

*Janafty...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS.. 24*

*Ki biya ki karanta cikin Aminci da Salama 09069067488 mace mai aji mallakan komai nata takeyi bata jiran abun sata*
Chapter 51 · 0% Book details