← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 94

Sashe 4

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka akayi Auran Maryama aka kaita Maruka sun sha kukan Rabuwa ita da Habibu,Maryama Tayi kuka sosai Kuma Ta makale ma Habibun Sai da yaje dashi aka kaita Chan Maruka Gidan su Sule Inda zai zauna a Babban Gidansu Tun Wannan Zuwan Mahaifiyar Sule ta Fara yada mgana kan Wani Sabon Salo ne Za"a kawo amarya Harda Kato ana mata Bayani Yayanta ne, Bata ma Tsaya Saurara ba Domin Har acikinta Ranta Bataso Auran Sule da Maryama din ba an dai fi karfinta ne.

Tun da Maryama Ta auri Sule Take Cikin Mtsala Da goggonsa Mace ce mara Hakuri gata Fitinanniyar Bata kaunar Maryama Ko kadan kuma Sun Hada kai da matan ya"yanta yayyin Sule suna Muzguna mata Sai dai Tsiranta Daya Mijinta yana Matukar sonta Burinsa ya kyautata mata Saboda Habibu ya Jadaddamai ya Rike mai kanwarsa Amana Domin Duk Duniya ita kadai garesaa kuma baya son wani abu ya sameta bama Domin haka ba Yana Tsananin kaunar Maryama Tun baya Fahimtar Halin Dayake Ciki Har ya Fara Fahimta sai yaji ya kara Sonta Domin bata Taba gayamai Tana Fuskanta wata mtsala ba ballatana Kuma in taje ta gayamasu Inna Hasiya wani Abu Koda sun Tambayeta ya Zaman ta da Dangin Mijinta sai tace Komai Lafiya bata Taba Bude baki ta Fadi wata mgana Saboda bataso su Shiga Cikin Damuwa Saboda ita ba.

Habibu Shi ya Fara karantar Halin da Maryama ke Ciki..Domin Daman Duk Sati yana Hanyan zuwa Gidan Maryama Din Dauke da kayan kwalaman Dayake Siya mata na Tsaraba Duk Abunda yasan Tana so in ya samu kudi zai Adanasu baya Tsinana ma kansa komai sai Maryama,Tun yana zuwa yana Tambayanta me ke sakata Rama tana cewa bakomai Har dai Ranar yaje Gidan ya iske Goggo Ta tasata Tana Zaginta Maryama na Duke Tana kuka Ranar Duka Gidan sun ga Kalan Fushi da Bacin Ran Habibu Bai tsaya Jin ba"asi ba ganin Maryama na kuka yace ta Hado kayanta Su Tafi Gida Bata da yarda Zatayi Haka ta Hada Ta Bishi ita kanta Goggo sai Ta Raina kanta Daga baya.

Sai dai su Baba Jibo suka Gansu kwatsam,nan Habibu yake Maida musu abunda yafaru Inna Hasiya ta Fara Fada Tana Fadin bai kyauta ba Taya zai Dauko ta batare da Izinin mijinta ba Haka ta Dinga Fada Tana Nuna Bacin Ranta,Shi dai Habibu Bai ce komai ba Baba Jibo ma bai yi mgana ba Saboda Inna Hasiya ta Rigatayi mgana kuma Bayaso Habibun yayi wani Tunani Tunda Maryama kanwar sa ne ko suna da rai Shi mai Tsayawa kan mganar Maryama ne.

Adaran Sule ya zo Ririwai yana Rokon su Baba jibo suyi Hakuri su bashi Maryama su koma,Baba Jibo yace basu zai bama Hakuri ba Habibu zai bama Hakuri mgana na Hannunsa Dole ya Duka yana Rikon Habibu Shi kuma yace Zai Tafi da Maryama ammh Da Sharadin wlh ko kallon Banza aka kara mata ba Zagi ba sai ta bar Gidansa Ba Dole ba wai Basu sonta bane suka Aura mai ba kuma ba Jaka suka kai mai ya Dai ja mai kunni Daga karshe Sule yayi alkawarin Insha Haka bazata kara Faruwa ba,Cikin Girmamawa Sule ya Dauki Maryama suka koma Washegari kuma yayi Tsiya agidan ya kuma Tsoratar da Goggo Cewa in aka kara Takura ma Maryama Wlh zai Dauketa su bar garin Jin haka yasa ta koma Tayi Lambo Sanin Halinsa gashi kuma Auta ne tana Matukar Ji Dashi Bata son yayi mata Nisa.

Dalilin Faruwar haka yasa Maryama ta samu yanci Duk da Dai anayin ammh ba kamar baya ba Sai ta samu kwanciyar Hankali Ta maida Jikinta Har Aran Habibu yake jin Dadin ganin Maryama Cikin Farinciki Sai dai me Shekaran Maryama Biyu da Aure bata Taba ko batan wata ba Dalilin Daya saka Goggo Ta kara yunkurowa kenan Tana Fadin Maryama Juya ce bata Haihuwa,Tun abun baya Damun Maryama har ya Fara Damunta Itama Tana so ta Haihuwa ammh kana naka Allah na Nashi ne har ta kwarari Shekara Biyar Gidan Sule Bata Taba ko da Batan Wata ba zuwa Lokacin abubuwa sun Riga sun gama Rikicewa Goggo Ta Daka Tsalle tace sai Sule ya kara aure shi kuma yace bazai yi ba,Tun Maryam Din bata saka baki ba Har tazo ta Fara Rokon Sule Daya ji mganar Goggo ya kara Aure ko Zata samu Sassauci Daga Goronta mata da gorin Mutanen Gidan.

Daga bangaransu Baba Jibo basu da yarda zasu yi da Halin da Maryama ke ciki Sai dai suna Tayata addu"an Allah ya bata Haihuwa Tunda shi ne mai badawa Habibu kuwa Duka Salolinsa Maryama yake sakaawa Yana Rokon Allah ya bata Haihuwa sadaka kullum sai yayi Domin Farincikin Maryama Shine nashi Cikin wannan Halin Goggo ta matsa Sai da Sule ya kara aure da yar Aminyarta Zainabu kuma Ta tare nan kusa da Dakin Maryama din.

Auran Sule da Wata Biyar Habibu ya auri Hajara Diyar Mallam Yahaya wanda Hadin na Baba Jibo ne,Habibu yaro ne mai Biyayyah bai taba ma Iyayansa Gaddama ba Ballatana Hajara Data kasance yarinya mai kunya mai Hakuri alokacin Tana da Shekara 16 ne akayi musu auran Suka Tare nan Gidan Inda Baba Jibon da shi Habibun suka Gida Dakuna Biyu Dake Barayin Inda Habibun ke Zaune Ginin Jar kasa da mai yaben ganye aka Shafeshi da Farin Fentin Farar kasa na Mutanen kauye

Lokacin Maryama ta koma Maruka Bayan Tazo Bikin Yayanta Habibu ta iske Zainabu Nada Ciki Lokacin Gori da Habaice Habaice duk ya Tashi Sai Dai maryama ta koma Daki Tana kuka Domin Da Zarar ta Fito sunanta Juya Bata samun wani Jin Dadi sai Sule ya Dawo wanda Daman Goggo Tuntuni Take Fadin Ta asirceshi ne baya ji baya gani sai akanta.

Haka Zainabu ta Haifi yarta Mace Maryama na cikin Halin Tsagwama da Bakinciki Ko yar ma ba"a bataa ta Dauka ba,wai kada ta kasheta saboda bakincikinta Ranar tayi kuka kamar Ranta zai Fita sai dai Da Sule ya Dawo yaji Labari sai ya kara musu yace sunan yarsa Maryama aikuwa kan Haka sai da Goggo Ta mareshi Shi kuma yace bazai Sauya ba Maryaama Ta Riga ta sani Sule na Sonta kuma Har Abada bazai Taba Juya mata baya ba Shiyasa Koda Tana Cikin Damuwa da Zarar ya Dawo sai ta Kirkiro Fara"a da Annushuwa ta Dora saman Fuskarta aranta Bata Fatan Taga Damuwa akan Fuskar wadanda baza sukuni in suka ganta Cikin Damuwa Wato Yayanta Habibu da Megidanta Sule.

Daga Barayin Hajara ma Shuru ne ba wani Labari Su basu Damu ba Tunda sun yarda Allah ne bai bayarwa ammh Kuma Habibu Shima yana son Haihuwa Kodomin ya mallaka ma Maryama Abunda ya Haifa ta Daina kukan Rashin Haihuwa aduniya sai kuma Allah bai bashi Haihuwan da Wuri ba, ammh bai gaji ba yana gayama Allah akoda yaushe

Bayan Auransu Ba Dadewa Allah ya Dauki Ran Mallam Yahaya Hajarah Inno da Ayyah sai yayarta karime kadai suka Rage mata Sauran kaneenta yara ne itace Babbansu sai dai Bata da wani Damuwa Habibu dasu Baba Jibo sun kasance mata tamkar wasu garkuwa gareta Maryama kuma Ta kasance Kamar wata yayarta Shiyasa ma take kiranta Adda Maryama.

Kwantashi ba wuya awajen Allah har Zainabu ta kara Haihuwan Yarta Mace taci Sunan Goggo Mardiya,Maryama Shuru wanda ba Domin sule na kaunarta ba Tuni Goggo Da Zainabu sun yi Sanadiyar da Ta koma Gida Sai dai sun yi sun yi sun gaji Maryama ta Zame musu Ciwin ido basu yarda zasu yi da ita acikin wannan Halin ne Ciki ya Bulla Jikin Hajara Murna ba"a mgana Tun Daga Lokacin Maryama Take Shirin Tarban Abunda Hajara zata Haifa Cikin Kiwonta Ta Dauki Rago Daya ta wareshi na Sunan Abunda Hajara Zata Haifa Ko Habibu Baya Dawainiya da Hajara yadda Maryama take yi Ko bazata zo ba in Sule zai zo Zata aikosa da su Goriba aya da Sauransu aka wo ma Hajara Su Baba Jibo suna mamakin wannan kaunar Dake Tsakanin Maryama da Abunda ke Cikin Hajarah.

Haka Hajara Tayi ta Ronin Cikinta Da Taimakon Inna Asiya da Habibu Da Maryama Har Cikinta ya isa Haihuwa ta Haifi Mastur kamar yadda Maryama ta Zabamai suna da kanta Wanda Maryama bata iya Runtsswa ba Tun bayan da Habibu ya Kirata yace Hajara na kan gwiwa kuma Farinciki bai Saketa ba sanda ya kirata yace mata ta Sauka Ta gode ma Allah kuma Taji kaso mafi yawa Daga Damuwar Rashin Haihuwanta ya Ragu Tunda yau Taga Da"an Dan"uwanta Datake matukar so kuma Take ji Dashi.

Wannan kenan..!

*****

Haka Rayuwa ta Cigaba da Gungaruwa Cikin Koshin Lafiya da Tsarawan Ubangiji,Hajara na Cigaba da kulawa da Mastur haka ma su Inna Hasiya ba"a barsu abaya ba Balle sun samu Jika Lokacin da karfinsu ya Fara karewa
Bangaran Habibu ma ba"a barsa a baya ba ga Maryama wacce kusan kullum tana Hanyan zuwa ganin Mastur wanda yaron ya Shiga Ranta Kamar ta Daukesa Sai dai bata da yarda Zatayi Tunda bata da Nonon da Zata bashi,Abunda bata sani ba Habibu yayi ma kansa alkawarin Ko iya Mastur kadai zai Haifa zai mallakama Maryama Shi kuma ya Zauna Haka ya gwammace ya Cigaba da ganinta Cikin Farinciki Har Abada Daya ganta Cikin kunci Da Damuwa Shi kadai ya yanke ma kansa Hajara na yaye Mastur zai Damkama Maryama Shi Halas malak.

_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._
Chapter 4 · 0% Book details