← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 94

Sashe 29

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima abangaran Mastur Yaso matuka yaji wata yarinya ce Mansur din yake so bai taba gayamai ba duk yadda suka kasance abokan Sirrikan juna Wata Zuciyar tana ta wani sake sake Kada abunda take Hasasomai ya zama gaskiya in ya Lura da Statement din Mansur din sai dai baya bama Zuciyarsa Daman yadda da hakan Bai samu Lokacin da zasu zauna suyi mgana bane kuma Daya koma Porthercourt Hankalinsa ya koma kam aikinsa ko sunyi mgana da Mastur Sai dai kawai su gaisa basu samu Lokacin da zasu Tattauna ba Duk da Mansur din yana Su Tattauna mganar Domin yana so kafin Lokacin Zabensu Ayi bikinsu da Diza din Shi kuma Mastur din yace ya bari in ya samu Lokaci zai Kirasa su Tatttauna.

Diza kuwa har Titsiyeshi Tayi Tana Tambayansa wayake so..? Daman yana da wata wacce yake so ne ko Labarinta bai taba Bata ba,Kin gayamata yayi yana ganin kamar ta sani kawai jan ajin nan ne na mata ammh Shi anashi Tunanin yana Tunanin Da Zaton kamar yadda yake sonta Ba tun yau ba ita ma hakan take Sai dai ya saba Lamba Bai san Diza bashi take so ba Dan"uwansa yaya mafi Soyuwa garesa take son ya Zama Bangonta Har Abada,Kuma ma yaso ya Fahinci wani abu Lokacin Daya bata Labarin Busharan Inna karime Har da Nuna mata Vidoe Yaga Tsantsan Tashin Hankali da Damuwa Da Kishi acikin Idanuwan Diza yaso ya Fahinci wani abu ammh kuma sai bai Taba Saka Tunanin haka aransa ba sai yayi Tunanin kila Saboda Taji mganar Busharan Daga sama ne Sai da taji yace ya gayamata yadda suka kare da Inna karimen da Abunda Mastur yace ne yasa yaga Ta Sauke Numfashi Fuskarta ta Saki Daga Lokacin kuma Tatashi ta koma Gida Wuni Tayi Cikin Damuwa aranar ma Ta gwada kiran ya Mastur yafi sau goma Tana Fasawa Tana ji kamar ta Kira Mastur ta gayamai Sirrin Zuciyarta kafin wata ta Rigata Samun Zuciyar abun sonta sai dai kuma ta kaasa Tana Jin Nauyi Kuma uwa uba ba wani Sakewa ko Sabawa a tsakaninsu Tayi Tunanin ko Mansur Zata gayamawa ya gayamai Sai kuma ta Fasa Tana sakawa tana Warwarewa ammh Tabbas mganar Bushara ta girgizata Duk da Taji ance yar kauye ne ammh Kishinta ya Turniketa Diza Tana san Tana da Kishi ammh Kishinta kan Mastur Dabam ne bata kaunar ma wata taRabeshe abaya ma Datake Zaune bata Damu ba Sanin Datayi Shi Mastur Daman yake Aboki ma bashi Dashi ballatana Wata Budurwa kuma ta Tabbata inda akwai wata Tabbas Mansur zai Sanar da ita,ammh yanzu kam Lokaci yayi da Sirrin Boye zai Fito Fili itama Tana Bukatar kasancewa dashi a matsayin Matarsa.

*******

*Bayan Wata Daya..*

University of Lagos Da Misalin karfe 12:30pm na ranar Jumma"a
Alhamdullillah su Rumana sun kamallah Jarabawansu ta Karshe Aranar Sun Firfito Kowanne kagani Fuskarsa Cikin Fara"a da Farinciki mazan su da matansu suma sanye da Farar Lapcoat ne,Suna ta Daukan Hotuna Cikin Murna mara Misaltuwa Ruma gefe ta koma Ta Dauki wayarta ta kunnata Wanda Tunda suka Fara Jarabawan ta kasheta Karatu kadai ta saka agaba,ba kama Hannun yaro bata kira ba"a kiranta Umma ta kira Tana Dagawa Cikin Farinciki tace"Umma Mun fito Last paper dinmu yanzu.."

Umma Dagachan Bangaran Tace"Masha..Allahu Ruma..Allah yasa abunda kika karanta albarka Allah yasa kiga sakamako mai kyau.."Cikin Farinciki Rumana ke amsawa Da"Ameen Umma..Nayi kewarku keda Abba..Ina Goggo Jummai da juma..? Umma tace"Kowa lafiya..Abbanki ya Fita yana kamfani Goggo Jummai na Daki ta kwanta Kafarta na matsa mata Juma kuma tana Kitchen..Muna kewarki Rumata yaushe Zaki Dawo..?

Ruma tace"Allah sarki..Ki gaishemin da goggo ta Umma..Zan Dawo sai Next week.Zan tsaya in yi Clearence,sai kuma akwai Dinner da muka Haada In kuma gama Sai na Dawo gida,in sakamako ya Fito da kuma in sunkiramu Indection..'Umma tace"Shikenan Allah yayi Jagora Ruma..Ki kira Abbanki Ya Damu kullum sai yayi Zencenki.."

Rumana Tace"Zankira shi yanzu Umma.."Da haka suka yanke kiran Abba ta Kira Cikin Farinciki ya Daga wayar,yayi murna da Farinciki Da Rumana tace sun gama jarabawa yayi mata addu"a sosai ya Tambayeta yaushe zata dawo tamai Bayanin da tayi ma Umma ya Fahimta suka Rabu bayan ya Tambayeta ko tana Bukatar Wani abu tace A"a bata Bukatar komai da haka sukayi sallama ko Cikin makaranta Bata bari ba zuwa Hostel Taga Sakon 100k Daga Abba ya Turo mata Murna da Farimciki ya Cikata Har Abada tasan ita yar Gatace.

Abba kuwa Farimcikinsa Daya Rumana ta gama karatu zata Dawo gabansa,Yana son Ruma Tayi aure yaga Jikokinsa Ita kadai ya Haifa aduniyar nan yana Bukatar ganin Tsatsaon Ruma kafin ya bar Gidan Duniya Ko da Farko bai so ta Fara Karatu bai aurar da ita ba Sunsha mgana da Alhaji Sunusi kan hakan Shiya ya Dinga Bashi Shawaran ya barta ta Cika Burinta,Nayi karatu Allah barshi In Allah ya kawo mata Mijin ko Tana cikin yin ne sai aurar da ita sai ta Cigaba da karatunta adakinta da wannan Shawaran ya Tsaya mata Har ta Cimma Burinta Sai dai abu Daya na Damunsa na ganin Rumana bai Taba gani ko Jin Labari wani Saurayinta ba Har Umma ya Tambaya tace Batajin Rumana Nada wani Saurayi ammh dai bata sani ba,Hakan yasa Hankalinsa ya tashi yana so Rumana Tayi aure yana son yaga ya'yanta.

Alhaji Sunusi ya kira yagamai Abun Farinciki Shima ya Tayashi Murna sosai ya kuma ce in Lokscin Indaction dinsu ya Tashi ya sanar dashi Shida Mommy Har da Diza zasu je mata Har Lagos Abba yaji Dadi Sosai yace insha Allahu,Daganan suka gangaro kamar mganar kasuwancinsu Da haka suka Rabu,Daddy yana Dawowa yake gayamawa Mommy Lokacin suna Falon Sama Har da Diza Mommy ta kalli Diza Tana Fadin"Diza Zaki ma yar"uwarki Lagos ko..?ki tayata Murna ta Zama likita.."

Diza na Faman latsa wayarta Tace"In bani da wani aiki Mommy..zani insha Allahu.."Daddy yace"In bata da Lokaci ki kyaleta Asiya..Ni Dake sai muje.."Mommy tace"A"a da ita zamu je..Haka zasu ta zama basu san juna ba..? Tun suna Yara ba Rabonsu da juna.."Daddy yace"Zasu san juna mana..Ai Rumanan ta Dawo Gida ko Daga baya Sai taje Tayi musu ko Kwana Biyu ne suga juna.."Mommy tace"ai shikenan.."Diza na jinsu bata tankasu ba,Bata jin ma Zata samu Zuwa bata kaunar Tafiya mai Nisa kuma in Tatafi wazata bar ma aikinta,Sai dai in kafin Lokacin ta samu wacce Zata rika Taimakonta Tana nan dai tana Dubawa bata son ta Dauki Shirmanmu ne,So take ta samu Kamar Hauwa wacce Take da kokari kan aikinta.

******

Ranar lahadi ta kama Weekend ne Tun Safe Mastur na Apartment dinsa bai Fita ya gaji Shiyasa yasha Barcinsa Sallar Azahar ma acikin Gida yayita sai da ya idar ya Daga waya ya Kira Sargent Inuwa yace yazo Gida yana Nemansa ba Dadewa sai gashi yazo kudi ya bashi yace yace yayimai Takeway din Tuwon Shinkafa miyar agushi da Nama ba Dadewa ya Dawo ya kawomai,ya Sallameshi cikin Gidan ya Dawo yaje kitchen ya Dauko Filet ya Juye ya Zauna yaci ya koshi ya Dora da Ruwa Dayake shan Lemukan Turawa basu Dameahi ba Nan Falon ya Zauna kan Daya Daga Cikin kujerun Falon yana Hutawa,Sai Tunanin Mansur ya Fadomai kan mganar Dayace zasu yi Tashi yayi ya koma Cikin Bedroom dinsa ya Dauko Wayarsa Wacce Sai personal mutane yake kira dashi kamar su Hajja Daddy da Sauransu Yana Dawowa yaje ya Dauko Karamin Kofi na Tangaran ya Zubo Coffea Daya Dafa da Safe yazo ya zauna yana kurba yana Laluban Wayar mansur din sai yaji wayar tana Ringing bai Daga ba sai ya Juya akalan kiran ga Baba Habibu suka gaisa yana kasuwa sai ya Kashe ya Kira Hajja suka Dade suna mgana Har ta bama Aiya sukayi mgana Daganan ya Kira Umma da Abba dake Sokoto suka gaisa nan ne ma Abba ke gayamai Gama Karatun Rumana Gobe ma Zata Hau jirgi ta Dawo Gida ya Tayata Murna kwarai yace zai Kirata Daganan sai ya Kira Wayar Daddy bayan sun gaisa Daddy ya karamai mganar da sukayi Dayazo Kan mganar Aure ya kuma ce yakamata Tunda Mansur yace Yana da wacce yake so shima yasan Abunda yake Ciki Dahaka suka Rabu da Daddy Duk sai Mastur yaji ya Damu ba wai bai Tashi Aure bane baisan Ta Ina zai Fara ba yaso sai sun samu Daidata da Fahimtar juna Tsskaninsa da Diza kafin komai ya Biyo baya,Shi bai san ta ina zai Fara ba kwata kwata bai da wani sani kan Harkan Soyayyah ba Shiyasa ya kasa yin wani yinkuri,Abunda ke Damunsa ma Rashin Sakewar da bashi Dashi Tsskaninsa da ita.

Yana cikin wannan Tunanin Wayar Mansur ta Shigomai bayan ya Dauka sun gaisa Mastur yace ina ya shiga ya Kira bai Daga ba Mansur yace"Ina Daki Ya Mastur..Na kwanta ne nagaji banga kiranka ba.."Mastur yace"Ina Fatan kayi sallah ko..?

Mansur yace"Yanzu na tashi..Nayi yaya ya aikin..?Mastur yace'Aiki Lafiya lau..Ya Siyasar taku..? Mansur na Dariya yace"Siyarku dai Ya Mastur..Kai ma ai yayan Dan Siyasan ne.."Mastur Mirmishi kadai yayi bai yi mgana ba Mansur yace"Yaya Mastur kun kara mgana Da Daddy kan Mganar nan ne..?

Mastur ya lumshe idi yana kara kwantar da kansa Saman kujera yace"Eh yanzu ma da mukayi waya sai da yamin mganar.."Mansur ya mike Zaune yana Fadin"To yaya kai kana da wacce kake so ne..? Ni dai nasan baka Dashi..Baka iyama Hira da Namiji Dan"uwanka ballatana Mace..? Ya fada yana yar Dariya Mastur yayi Shuru kafin yace"Kai ma ka sani ashe..? Ni na rasa ta ina Zan Fara ne Ammh Tunda ka iya Zan zo ka Koyamin Honourable.."Dariya ta kama Mansur yace"Nima ban Fara Gwajin bafa Yaya Mastur.."Mastur ya gyada kai yana Fadin"Meyasa..?bakace aleady kana da wacce kake so ba.."?
Chapter 29 · 0% Book details