Sashe 58
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 6 min read
Gidan Daddy ta Fara Yada Zango Har Cikin Haraban Gidan ta Shiga da Motarta Megadi na Mata maraba ta Fito Tana kara gyara Zaman gyalenta asaman kai Bayan Motan ta Bude ta Dauko Kwandun abinci guda Daya Ta Nufi Cikin Gida Tana Shiga Taci karo da Mommy a Falon kasa Tayi bakuwa Tana ganinta Tatashi Tana Mata Maraba Kasa Rumana ta Duke Tana gaida Mommy da Bakuwarta Bayan ta ijiye Abunda ke Hannunta agefenta Mommy ta Shiga kwalama Mama Fadime Kira sai gashi ta Fito da Gudu Tana Zuwa Mommy tace"Maza ki kawo ma Rumana Ruwa da Lemo.."tafada Tana komawa Ta zauna Da Sauri Rumana Tace"A"a Mommy a koshe nake..Ai Daga Gida ne ma.."Mommy tace"Allah Sarki..Nazata Daga asibitin kike Domin Yanzu nan Diza tatashi Daganan ta Shiga wajen su Hajja ne Zata je ta Duba Usmanun Balaraba ba Lafiya nake Tambayanta kina ina tace kila kina asibiti.."Rumana Ta Murmusa Tana Fadin"Yau ban je ba Mommy sai Ranar Talata.."Mommy tace"Ayya..Kice Mastur ya gayamiki kenan Zaku je gaida Usmanun Balaraban kenan..? Sai yanzu Rumana Ta Fahimci Dalilin kiran Da Sauri Tace"Eh Mommy.."Mommy tace"To Tashi maza ki Hanzarta Ku tafi Tare da Diza Ta Shiga wajen su Hajja.."Rumana Batayi gaddama ba ta yunkura ta Mike Tana Fadin"Mommy ga abinci.."Tafada Tana Turamata gabanta sai Mommy ta saki Baki ta Juya tana kallon kawarta Hajiya Barira Tace"Hajiya kinga Abunda nake gaya Miki ko..? Rumana Diyar albarka Harda Abinci kuma..? Rumana tana Mirmishi tace"Eh Mommy..Na kawo muku ne keda Daddy.."Mommy tace"Mungode Allah yayi Miki albarka Rumana.."Mommy ta Fada Cikin Bayyana Farincikinta Rumana Batace komai ba sai Mirmishi take Tace"Mommy bari naje..Zan Dawo kafin mu tafi gida.."
Mommy tace"Ok.Sai kun Dawo ki samu Diza gidansu Hajja.."Rumana ta amsa da toh ta Fice Daga Falon Mommy ta Bita da kallon Sha"awa Kafin ta maida kallonta kan Hajiya Barira Tana Fadin"Kinga abunda nake Fada Miki yanzu ko..? Rumana tafi Diyarki wayau da Hankali Wlh yarinyar nan bata Zuwa min Hannu Rabbana Koda ace muna Dashi ammh ai Wayau ne kasan zaka zo waje ka Riko wani abu..'Hajiya Barira tace"Hakane..Kinsan kuma da yanayin gogewar ilimi da ita Rumanan Tafi Dizan Hajiya Asiya.."Mommy ta Jinjina kai Tana Fadin"Da wannan kuma don wannan..'Tafada Lokaci Daya tana Jawo kwamdon Ta Bude ta Ciro kulan ta Bude Kamshi ya Dakesu,Mommy Ta shaki Numfashi Hajiya barira ta Leka Kulan Tana Fadin"Kai wannam Delecious din fa..Zuba min Zan ci Hajiya.."Ta karishe Fada Tana yar Dariya itama Mommy Dariyan taketa Dago Zobon Tana Fadin"Harda Abunda nafi so Zobo.."
Mama Fadime ta kwalama Kira tace tazo da Filet da Cokula.
Rumana na Fita Bata Tsaya Daukan Motan taba ta Dauki Kwandon Abinci da Jakarta ta Fita Zuwa Gida wajen su Hajja Tana Sallama kuwa taci karo daDiza Zaune afalon Kan Kujera Ayya na gefenta suna Hira Batayi msmaki ba Domin taga Motarta a Kofar Gidan Wanda Dazu Bata lura da ita ba Ayya na ganinta ta Fara mata Maraba sai ga Hajja ta Fito Daga Daki Da Hijabinta wanda ta idar daSalla Kasa Rumana taZauna tana gaishesu da Tambayan yamai Jiki suka amsa mata Cikin kulawa Hajja ta kalli Rumana tana Fadin"Yanzu nake Zuci Zucin na idar da Sallah nace Diza ta kiraki taji ko kin Taho..Tunda munyi mgana da Babban Mutum yace zai kiraki ya gayamiki Kizo ku leka Gidan Balaraba ku gaida kawunku bashi da Lafiya.."Rumana ta Sadda kai Cikin Ladabi Tana Fadin"Eh Hajja..ban dade da zuwa ba Dayake na Shiga Wajen Mommy mun gaisa.."Hajja tace"Allah sarki..Tana Lafiya..? Rumana tace"Lafiyanta kalau..Daga haka ta Mike da kwandon Abincin zuwa gaban Ayya ta Ijiye Tana Fadin"Ayya ga Girkin nayo Miki.."Ayya ta Washe baki Tana kallon kwandon lokaci Daya Tana Fadin"Ah..Kaga Uwargida mai kaunar Amaryata..Lalle na yarda kina Maraba Dani Diyar nan Hajara kalli wani abun Arzikin..! Tafada Tana Nuna ma Hajja wacce take gyada kai tana kara Girmama Rumama acikin Ranta Cikin Farinciki Ta kalli Rumana Tana Fadin"Rumana Bakya gajiya Da Hidima..? Kan Rumana na kasa Tace"Bakomai Hajja.."Hajja ta gyada kai Tana Fadin"Allah yayi albarka Rumana."Ayya ta amsa da Ameen Diza na gefe Tana Latsa wayarta Daman tun Shigowar Rumana ta Dauke kanta Kmar bata ganta ba yanzu ma Kara Hade Ranta Tayi Kamar bata Taba Dariya ba Rumana ganin Idanuwan su Hajja yasa ta Daga kai Tana kallon Diza Tace"Diza ashe kin Taho kina ta Jirana..? Kuyi hakuri abincin ne ban Karisa da wuri ba..!
Diza ko kallonta Batayi ba Ta Tabe baki Lokaci daya Ta Mike Tana Fadin"Uhmm muje ko..? Tafada Tana Yarfa ma Rumana wani kallo Mikewa Tayi Tana Kallon Hajja tace"Hajja bari muje mu dawo.."Hajja tace"Ku gaisheshi..Sai an juma zamu leka Nida Hajiya.."Ayya ma tace su gaishesa suka Fice Daga Falon Ayya da Hajja suka koma Yabom kyawawan Hallayar Rumana.
Diza kuwa suna Fita Bata ma Tsaya Jiran Rumana ba Tayi gaba tana wani Takun yanga Da Takalminta mai Tsini ita dai Rumana tana Binta abaya Sanin bata san Gidan ba Bawani Nisa sai gaahi sun iso Diza ce kan gaba suka Rafka sallama suka Shiga Gidan ba kowa a tsakar gidan Balaraban ne ta Leko Daga Dakin Kawu Usman din Tana musu Maraba ta ganesu Gaisheta sukayi kafin ta musu Jagora zuwa Cikin Dakin yana kishingide kan Katifa yana Jin radio suka Shigo,Kan Tabarman Dake Dakin suka Zauna Diza ta Fara gaisheshi ya amsa sai Rumana sukamai ya Jiki yace da Sauki ganin yana musu kallon Rashin Sani ne yasa Inna Balaraban ta kallesa Tana Fadin"Baka gane su ba ko..? Surukanka ne Matar Mastur ne Rumana da Matar Mansur hadiza fa.."Baki ya Rike yana Fadin"Ba Shakka..kuyi hakuri Tsufan yazo..Sannunku Allah yayi muku albarka Allah ya baku Zaman lafiya.."Balaraba ce ke amsawa da Ameen Ita dai Rumana kanta na kasa Kawu Usman ya kalli Rumana yana Fadin"Megidan naki yana chan wajen akin nashi ko..? Ai dazu ma munyi mgana Dashi Allah dai yayi ma Mastur Albarka Kullim sai ya Kirani yaji Jikina..Shima Mansur din kullum sai yazo ya Dubani Duk da Siyarsa tasu ta karato Allah ya Biyasu Duka Hidimata su sukayi su da Iyayansu Habibu da Alhaji Sunusi Babu Abunda Zance iya ce musu sai Allah ya Biyasu da aljannah.."Suka amsa Dukkansu da Ameen kafin ya Dora Da Fadin"Ya wajen Jikin Baban Mijin ki Khadija..? Diza ta Rausayar dakai Tana Fadin"Da Sauki kawu..Gobe ma zamu koma mu Dubasa Har dasu Ayya.."Ya gyada kai yana Fadin"Masha Allah..Ba Domin ina kwance da Balaraba ta Biku taje ta gaisheshi.."
Diza tace"Bakomai kawu ai ma ya samu Sauki Har an sallamosa Daga asibiti.."Yace"Toh Alhamdulillah Allah kara mana Lafiya.."Suka amsa da Ameen sun Dade yana ta Jansu da Hira Yana da Barkwanci da Hira Har Balaraba ta gama Dambum Masara ta Zubo musi sai Diza ta Mike tace ta Koshi ita kuma Rumana Ganin bazasu ji Dadi ba in Basu ci ba sai tace ta saka mata a kwano Zata Tafi Dashi Gidan su Hajja taci achan da Farinciki kuwa ta saka mata Cikin Sabuwar Samira ta Basu Har Kofar Gida ta Rakasu Tana Godiya ganin haka yasa Rumana ta bata 3k,gashi Daman basuzo da komai ba Dakyar ta amsa Tana ta Godiya.