Sashe 30
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mansur ya mike Tsaye yana Shafa kansa yace"Ai ban taba gayamata Sirrin Zuciyata ba ya Mastur..Ina sonta Tun ban san kaina ba na Fara sonta Tun Ranar Farko Dana Fara ganinta a Lokacin kuruciyarta..Ban Fahimci hakam ba sai da na Fara mallakan Hankalin kaina na Fahimci itace komai nawa ya Mastur.."Mastur Dayaji kalaman Mansur kamar dashi yake yasa yaji Jikinsa yayi sanyi Zuciyarsa ta Fara Tsalle waje Daya kada yazo Suna Tarayyah Shi da Dan"uwansa wajen son Abu Daya Bai ma samu Zarafin mgana ba yaji Mansur na fadin"Duka Tsarin Rayuwata Burinta ne ya Mastur...Duk da ban gayamata ba na tabbata itama Tana Sona kamar yadda nake sonta.."Mastur Dayaji Kamar Wutar Lantarki yajashi ya Mike tsaye rike da Kofin Coffea din Dake hannunsa Cikin Bushewar baki yace"Waccece..ita Mansur.."?
Mansur yayi Mirmishi yace'"Nasan zakayi mamaki ya Mastur..Yar gida ce...DIZA ce...!! Dam! Dam! Dam! Mastur yaji gabansa ya Fadi kansa yayi wami Mugun Saramai,Hannunsa da Jikinsa na rawa Lokaci Daya Kofin Hannunsa ya Sulale ya Fadi ji kake Tus ya Fashe Tsakar Dakin Saman Cafet din Dake Falon,Wayar ma Dake Hannunsa sai ta Sabule ta Fadi Saman Cafet din Jikinsa Jallabiya ce ammh Haka yake gumi da Zufa Har yana Tsiyaya Har kuwa da A.C dake Falon da Fanka wacce ke Gudu Tana bada iska.
Dagachan Bangaran Mansur yaji karan Faduwan abu Tus..Rike wayar yayi yana Fadin"Hello Ya Mastur..Kana jina..? Hello..? Yaji Shuru Domi Mastur yana jin Hello din Mansur ammh Jikinsa ya Daskare waje Daya ba zai iya Daga Hannunsa ba Ballatana har ya Duka ya Dauki Wayar kansa yana wani Saramai Lokaci Daya yana jin Amsa kuwan Mansur na Fadin Diza ce Zabinsa itace wacce yake so Tun tana Lokacin kuruciyarta Kenan Sun Fara son Diza Shi da Mansur alokaci Daya kenan..? Hasbunallahi wani"mal wakeel.."Yafada Lokaci Daya yana Dafe kansa Dayaji kamar zai Cire lokaci Daya yaji yayi yaraf ya Fadi na saman Cafet din Har hannunsa yana Dafa Glass din Daya fashe na Kofin,jini ya fara zuba ammh bai takai ba Halin da Zuciyarsa take ciki yafi Jinin Dayake Zuba Mansur kuwa gajiya yayi ya yanke wayar yana Tunanin Network ne sai dai kuma ya kara Kiran Wayar Mastur naji ammh ya kasa ma kallon Wayar Balle ya Dagata Har ta karaci Ringing dinta bai iya wani Motsin Kirki ba.
Kansa ya Dafe da Hannun Bibbiyu Jinin Daya bata Hannunsa Dashi yasa ya Dafe kansa Dashi Bai damu ba Cikin Wani irin Fuzgar Numfashi yake yi Domin Yanajin kamar Numfashinsa zai bar gangar Jikinsa Numfashi ya Fara saki Daya Bayan Daya Lokaci Daya yana Jawo Numfashin nashi kafin yaji ya dawo Daidai,Maida kansa ya jingina jikin kujera yana Jin kamar ya Rusa ihu,Ajiyar Numfashi kadai yake Saukewa yana jin Wayarsa nata Neman agaji yama kasa Tashi ganin kamar zai iya Shiga wani Hali yasa ya fara Kiran Sunan Allah,Cikin ikon Allah sai yaji shi ya Fara dawowa Cikin Hayyacinsa har ya iya Rarrafawa ya Mike Tsaye kan kafafunsa,Allah ya Taimakeshi bai Taka kwalban ba ya Tsallake komai Harda Wayarsa ya Fada Bedroom dinsa yana Rangaji kamar zai Fadi ya Fada kan Katifarsa Kamar wani matacce Yana so ne yaji ya yi kuka ko Radadin Dake zuciyarsa Zata Ragu gabadaya Jijiyoyin kansa sun mike Radau kamar mai wani Cuta Haka yake jin gabansa na wani Rugurugu kamar ajalinsa yazo Innalillahi wani'inna Illaihirraju"un wannan wani irin al'amarin ne Taya sukayi Tarayyah wajen son Abu Daya da Dan"uwansa..?meyasa ma bai Taba Tunanin Soyayyah Tsakanin Mansur din Diza ba..? Yake kallon haka kamar Shakuwa ce..?kuma itama Tana sonsa..Bazai Taba zama Sanadin Shiga Tsakanin Abunda Dan"uwansa yafi so akan kowa ba ko da Soyayyar Diza zai Kasheshi ya Zama Dole ya Binne wannan Soyayyar har Abada ya Cireta aransa Ta zama wani mafarki na Dabam Ya zama Dole yayi SADAUKARWAR SO ga Dan"uwansa Mansur Dagashi sai Allah suka san yana kaunar DizaDaga Rana mai kama ta yau bazai Taba bari wani ko wata yasan wannan mganar ba Ballatana Mansur ko Dizan susan da wannan labarin ba,kansa yaTura cikin Filo yana so yayi kuka ko zai ji sanyi ammh kuma abun akasan Ransa yake sukansa abu kamar waasa sai ga ciwom kai da Zazzabi mai Zafi har ya RufeShi Har yamma yana cikin wannan HALIN Har akayi Sallar La"asar bai iya Tashi ba yanaji Zuciyarsa ta Saukar ma da Jikinsa wani Nauyi,har aka Kira Mangariba ya kasa Tashi Sargent Inuwa ne yaga anyi Sallar La"asar ba Yallabai anyi mangariba ma Shuru yadda kowa yayi Shedansa baya wasa da Sallah akwai mtsala Shi yazo Gidan Ya Duba Tundaga Falo ya Tsorata ganin Fashashen glass ga Jini Sai daiHalin Daya samu Mastur aciki yafi Firgitashi Cikin Firgici yaje ya Kira Sauran Sargent din suka Tarairayesa zuwa mota Sai wani private Hospital,suna kaisa Sanin matsayinsa yasa nan da nan aka karbesa aka fara bashi Taimakon gaggawa,basu samu sukuni ba sai da suka Tabbatar da an kaisa Daki na musamman Bayan an sakamai Drip an mai alluran barci.
Mastur Farkawa kawai yayi Washegari ya gansa a asibiti sai alokacin abunda ya Faru ya Dawomai wannan Nauyin kan nashi yana nan har yanzu,Ba zai iya Tuna Rabonsa da Ciwo mai Zafi irin haka ba tun wani Ciwon Typiod Daya Taba yi yana Hassan Gwarzo har sai aka Dawo Dashi gida a Tearm din bayan Lokaci bazai iya Tuna wani DogonCiwo Dayayi ba ma sai dai irin Ciwon kai haka da Ciwon Gabobi na gajiya,ya takura azaman asibiti sannan kuma shi ba Ragon Namiji bane Jarumi ne Tsayayye bazai Taba zama saboda mace ya zama haka ba Dole ya gagice yana cema Likita ya bashi Sallama ya samu Lafiya sai dai bai Saurareshi ba Domin ya gayamai Jininsa ne ya Hau Lokaci Daya bai yi mamaki ba Domin yanayin Daya shi ga Ya zata ma Mutuwa zai yi.
Ransa bai kara baci ba sai da Sargent inuwa yazo ya kawo mai wayarsa da Jallabiyansa da Boxers Dayaje gida ya Daukomai Shine yake gayamai yaga wayar nan yashe afalo Shine ya Dauko mai yana Hanya Mansur ya kira ya Daga yagamai Yana asibiti bashi da Lafiya Ran Mastur ya baci kamar ya kwada ma Sargent Inuwa Mari,Haka ya karbi Wayar bai iya amsa Wayoyinsu Baba da Daddy da suke ta Kiransa ba Yariga ya sani Mansur ya gaya musu Bashi da lafiya,kuma shi yanzu bai san me zai ce musu ba shiyasa ma ko Taba wayar bai yi ba Duk da yaga Tarin Kiransa da akayi tayi kuma baya Raba Daya Biyun Kiran Duk na Mansur ne.
Sai da ya kwana Biyu Likita ya sallameshi da mganguna da kuma Gargadi mai girma kan kada ya saka ma kansa Tunanin Daya fi karfinsa Saboda Kada ya Kamu da Hawan jini Shi kuwa aransa yacr na nawa kuma ai yama kamani Tunda na Rasa Diza da toh kawai ya amsa bayan ya karbi Duka mgangunan Sargant Inuwa ya Tukasa Zuwa gida a Daya Daga Cikin Motocin Heaquater nasu Kudin asibitin ma da komai su suka Dauki Nauyin komai.
Koda ya koma gida ya iske har an Tsabtace Falon kuma yasan ba kowa bane sai Sargent inuwa bai ce komai ba ya Shiga Ciki ya Bisa da kayansa da magungunansa kafim ya saramai ya Fice Bai iya wani Tunani ba Domin Tun Daga Lokacin da Mansur ya gayamai Diza yake so ya rasa Duka wani Tunaninsa wanka yayi Ya zo ya saka Saukakkun kaya Saboda Jikinsa ba karfi,Lokacin an kira Sallar azahar Sai kawai yayi Sallarsa sai ya Dauko Wayarsa yaga Tarin Misseds na su Baba,Hajja,Mansur Daddy,Mommy Harda Diza abun mamaki Da kamar zai kyalesu sai yayi wani Tunanin kada suji Shuru su Zata ba Lafiya su Dauko Hanya Mansur ya Taba zuwa Har Cikin Apartment dinsa kuma ya Tabbatar da zai iya cewa Su Taho wannan Tunanin Da yayi yasa ya Lalubi Lambar Baba Habibu ya Kirashi wanda ya Daga da Gaggawa yana Tambayansa Lafiyansa..!
Cikin Dauriya Mastur yace"na samu sauki Baba har na Dawo Gida..likita ne ya Hanani Daga waya Shiyasa kukajini shuru.."Baba Habibu Dake kasuwa yayi ajiyar Zuciya yana Fadin"Alhamdulillah..Ai mu hankulanmu ya tashi..tunda Mansur yazo yagayamana Sargent dinka ya gayamai baka da Lafiya kana asibiti Muke ta kiran wayarka Shuru baka Daga ba Hankulanmu sun Tashi har ma Zuwa gobe Babanka da Mansur din sukace zasu bi jirgi Suzo nan Porthercourt din su Dubaka Ko lafiya..!?
Mastur yace"Basai sun zo ba..Suyi Zamansu Baba na samu Lafiya.."Baba Habibu yace"Shikenan Allah kara Lafiya."Mastur yace"Ameen..Ka gayamusu Baba basai sun zo ba..Zan kwanta ne nasha mgani zuwa anjuma zan kirasu.."Baba Habibu yace"Shikenan..Allah kara lafiya.."Daga haka suka katse kiran Mansur Baba Habibu ya kira ya gayamai sunyi waya da Mastur ga Abunda yace sai Lokacin Hankalinsa ya kwanta ya gayama su Hajja kowa yaji Natsuwa jin yana Lafiya,Daddy kuma Mastur din ya Kirashi da kansa ya gayamai sun Dade suna mgana yana mai Fadan ya Rika kula da kansa.
******
Bayan kwana Biyu Mastur ya gyagije ya Fara Fita Office ba wai Domin Zuciyarsa ta warke ba ya mike ne Tsaye ga Kakafunsa Saboda kada Gyambon da Raunin Dake Cikin Zuciyarsa ya shafi gangan Jikinsa alhalin ya Riga yayi ma kansa alkawarin Sadaukar da Soyayyar Diza zuwa ga Dan"uwansa Mansur.