← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 94

Sashe 2

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shekara Biyar sukayi da aure Shi da Hajara sai yau Allah ya basu Haihuwa sai dai ba wannan ne ya sakashi kuka ba yana Jin Raunin Dake Zuciyarsa Raunin Tunawa da Tilon kanwarsa ce Maryama Wacce ta Shafe Shekaru Goma da Aure Bata Taba ko Bari ba Kallesa yadda yake Farinciki Ya samu Karuwa yaya Zuciyar Maryama Take Ciki na Rashin Haihuwa..? rauninta me yawa ne ya sani Sai yaji Dama Dama Allah Ya bashi Zabi Tun Farko Da Zai ce ne Maryama Ta Haihu Taga kwanta aduniya ko da Shi Zai koma ga Allah bai Haihu ba Rauninsa bazai Bayyana ba Inhar Maryama Zatayi Farinciki kuma Zata Dauwama cikin Annurin Samun Haihuwa a Rayuwarta.

Cikin Siyasa ya Share Hawayensa Lokaci Daya ya Fara Tofamai addu"a Da Neman Tsari da albarka Duniya suna nan Tsaye Inna Hasiya ta Fito da Hajara Zuwa Daki Baba Jibo Ya Dauki Buta ya Shiga Makewayi zai kama Ruwa saboda an Fara Kiraye Kirayen Sallar Asuba a wasu massallatai,sai Habibu ya Bi bayansu Zuwa Dakin yana Shiga ya iske Har Inna Hasiya ta Turara Dakin da Turaran Kamshi Hajara na saka kaya Ganin ya Shigo sai ta Fita ta basu Waje Tace Zata je ta Dama ma Hajara kunu ta kuma Dumama mata Tuwo Taci.

Tana ganinsa ya Shigo Tayi Saurin Komawa Ta Zauna Daman kunzugu tayi ma kanta Saboda Tare Jinin Dake Zuba ajikinta,Kunya take ji sai Sunkuyar dakai take yi Bata son Hada ido Dashi Ganin haka yasa yayi Mirmishi ya isa gefenta ya Zauna Yana kallonta Cikin Taushin Murya yace"Hajara...!!

Cikin Sanyin Jiki Ta Dago kanta Tana kallonsa Mirmishi ya sakarmata yana Fadin"Sannu da kokari..Allah ya Biya Miki Bukatanki Nagode Yau sanadin ki zan amsa sunan Uba.."Kai ta kara Sunkuyarwa bata ce komai ba Sai ya kara Fadin"Ba ki ce Ameen ba Hajara..?

Kanta na kasa tana Tura kanta Cikin Lullubinta Tace"Na Fada acikin Raina.."Kai kawai ya Girgiza yana Tura Mata yaron Jikinta Lokaci Daya yana Fadin"Kinga Kyautar da Allah yayi mana ko...?

Kanta ta kara maidawa gefe Tana Fadin"Nagani.Allah ya rayamana shi.."Cikin Farincikin addu"an ta yace"Ameen Hajara..Ameen ya Allah."

Ta Fahimci acikin Jikinta kallonta yake yasa tace Cikin Sanyin murya"Ka Kira Adda Kuwa..?
Cikin Dafe kai yace"Kai..nayi Babban Mantuwa..Wlh ban Kira Maryama ba Bayan Kin Haihu..'

Inna Hasiya Dake Shigowa Dakin Tace"Hanzarta ka Kirata..Domin Nasan yanzu haka Tana chan hankalinta Tashe Tun bayan Kiran Dakayi mata ka Fadamata Hajara nakan Gwiwa.."

Cikin Sauri ya Mike yamikama Hajara yaron sai taki karba ta kauda kai Sai kawai ya Ijiyeshi Saman gado ya Fice Ya bar Inna Hasiya Tana Tsiyayama Hajara Kunun Kanwar Data Dama Mata acikin Katon Kofi Gefe Daya kuma ga Dumaman Tuwo Miyar kuka Tana Turiri.

Yana Fita ya Lalubo wayarsa Cikin Aljihun wandonsa wanda Tun Bayan da Ya kira Maryama da kansa ya Fadamata Abunda ke Faruwa bai kara bi Ta kan wayar ba Yana cirota ya Dannata sai ya iske Kiran Maryama har sau Uku Cikin Sauri yabi bayan Kiran Bugu Daya ana Biyu Ta Daga Tana Fadin"Yaya Habibu ina ta kiranka Baka Daga ba Hankalina ya Tashi Yaya Hajaran ta Sauka Lafiya kuwa..?

Cikin Mirmishi yace"Afuwan kanwata..Laifinane Wayar tana Aljihuna ban ji Kiranki ba..Hajara ta sauka an samu D"a Namiji Kanwata.."Yafada Cikin Farinciki Maryama Dake kan Darduma acikim kuryan Dakinta Bayan Ta idar da Raka"atulFajir,Domin Tun bayan Kiran da Habibu yayi mata Ya Fadamata Halin da Hajara take ciki bata koma Barci ba Alwala Tayi Ta zo ta Fara Salla Tana addu"an Allah ya Sauketa Lafiya Megidanta Sulaiman yana kwance yana ta Sharan Barcinsa Harda Minshari baisan Abunda yake Faruwa ba.

Cikin Farinciki Maryama Tace"Alhamdulillah..Yaya Barkanmu.Fatan Dukkansu suna Lafiya..? Yace"Lafiyansu kalau kanwata..Nasan baki koma barci ba Don Allah kada ki ce Zaki Taho Tun Safe Ki bari ki kwanta Ki Huta Kinji ko.?

Cikin Mirmishi Kaunar Dake Tsakaninta da Dan"uwanta Tace"Haba yaya Ace Yaya Hajara ta Sauka kuma sai Tun safe ban Taho ba..?kada damu kanka kayi mata barka kace ma Innanmu ta ijiyemin kunun kanwata Da Safe ina Tafe.."Bai da tace wa Sanin Ko yace kartayi Sammakon Zuwa sai Tazo Shiyasa yace mata"Shikenan kanwata sai kin zo..ki gaida Megidan naki.."

Daga haka suka yanke Kiran Maryama Ta Daga Hannu sama Tana kwaroroma Allah Godiya Cikin Zubar Hawaye,Sule mijinta Daya ji sheshhekan kukanta ya Farkar dashi ya Tashi ya Mitsike ido Cikim mamaki yake Fadin"Maryama Lafiya.?

Waiwayowa Tayi Tana Kallonsa kafin tace"Abun Farinciki ne..Yaya Hajara Matar Yaya Habibu ce ta Haihu an samu Da Namiji.."Tafada Cikin Farinciki Yana Daga kwance ya Tashi Zaune yana Fadin"ah ba Shakka..Kya yi Dariya..Allah ya Raya kema Allah ya baki naki Maryama.."Daya Fadi Haka sai kawai ta Murmusa kafin ta Mike Tana Fadin"Ka tashi an Fara Salla awasu masllatan fa.."

Daga Haka ta Tada Kabbaran Sallar,Da ido ya Bita dashi na Tsausayinta Allah ya sani yana son Maryama kuma Har yau har Gobe bai Taba Jin sonta ya Ragu Daga Zuciyarsa ba Rashin Haihuwanta Ba Daga ita bane Daga Allah ne,Ammh Goggo Tana Dora,komai kan Maryama Ganin ta matsamai ya kara Aure kuma Har sun Haihu da Zainabu Har ya"ya Biyu.

Yana Jin Muryan Goggon Tana Mgana da Zainabu Daga Tsakar Gidan Hakanan ya Mike Jikinsa a sanyaye ya saka Rigarsa ya Dauki Butan Da Maryama ta Cikamai Da Ruwa ya Fita Zuwa makewayi Goggo Bata Wajen Kila Ta idar da alwala ne ta Shigs Dakinta tayi sallah Zainabu kadai ya gani Tana alwala Gaisheshi Tayi ya amsa Sama sama ya Fada makewayi Tabisa da kallo Tana kunkuni Kasa kasa.

Shima Habibu suna gama Mgana da Maryama Ya Daura alwala suka Fita shi da Baba Jibo Zuwa massallaci Domin yin Sallar asuba koda suka je ba"a Tada Sallar ba sai suka koma Chan Baya suka Tada Raka"atulFajir Kafin Lokacin Sallah yayi suna Idarwa aka Tada Salla sai suka matsa Gaba suka Hada Sahu aka Tada Salla Dasu.

Kafin wayewar gari Haihuwan Hajara Matar Habibu ya gama Yada anguwa Har Gidan Iyayan Hajara Inno Domin Mahaifinta ya Rasu kuma Aminine ga Baba Jibo Baba Yahaya kenan ya Rasu Bayan Auran Hajara da Habibu Da Shekara Daya Abokiyar Zaman Inno Din Wacce suke Kira Ayyah ita tazo Da Safe ganin Sabon megida da kuma Taimaka ma Inna Hasiya da wasu ayyukan Kowa kagani Baki Har kunni Saboda Farinciki Makota sai Shigowa suke Barka Habibu kuma da Baba Jibo tun Safe suka Tafi Gona Dayake Tun kafin a Haifi Habibu Kowa yasan Sana"ar Baba Jibo Noma ce ammh Basu bar Gidan ba sai da Habibu ya Cika Duka ma zuban Ruwan gidan da Ruwa Saboda amfanin Masu Jego.

Wajen Karfe 9am na safe sai ga Maryama Ta iso Da kayan wanka Iri Iri Jakarta kuma Cike da kayan yara,Murna wajen Inna Hasiya ba mgana na ganin yarta Maryama Tare da Sule suka zo Shi ya kawota kan Mashin Karfe karfensa Dayake acikin Garin Maruka Take Aure Har Ciki ya shigo suka gaisa da su Inna Hasiya da Ayyah ya Shiga yayi ma Hajara Barka Ya Karbi Jaririn da Tunda Maryama Tazo Ta Daukesa Take kamkame dashi Yaji kamar yayi mata kwallah acikin Ranshi yana Rokon Allah ya Nuna ma Maryama Itama ta Haifi Danta Daga Cikinta.

Bai Dade ba ya barta nan ya tafi,Cikin kasuwar Doguwa Saboda anan yake da Shagon Sai da kayan Kwalliyan mata wato Costometic,Sai ya Tashi kasuwa da yammah Zai zo ya Dauketa su koma Gida.

Nan Maryama ta Wuni Har yammah Suna ta Hidima da Hajara da Jaririnta Sai Gabda mganriba kana suka Habibu Shigo Haduwar Yaya da kanwar wani Haduwane da kamar Zasu Hadiye Juna Daman hakan take kasancewa In dai suka Hadu kamar kada su Rabu Kuma ko yaushe ko Maryam Batazo nan Ririwai din ba Shi Habibun Koda yaushe yana Hanyan zuwa Maruka ganin Maryama din.

Sai da sukayi Sallar mangariba suka Dawo Inna Hasiya ta kaima Baba Jibo Abincinsa Dakinta Shi kuma Habibu Maryama Ta kawomai nan Dakin Hajara Ayya kuma ta Wuce Gida sai da Safe zata Dawo.

Umartanta Yayi data wanko Hannuwanta Tazosuci Tuwon Tare,Tashi Tayi taje ta wanke Hannuwanta Tazo Suna cin Tuwon suna Hira Sama sama,Hajara na gefe Tana kallonsu Abun nasu Sha"awa yake bata Tana ji Dama itama Tana da yaya mai kula da ita kamar yadda Habibu ke kula da Maryama..? Sai wata Zuciyar tace mata Ki Godema Allah Hajara Habibu ba iya Miji bane gareki Ya Shanye Miki Kuma ya kare Miki Duka Kishiruwan uba da yaya agareta yana Bata kulawa Daidai gwargwado.

Sai da suka gama Cin Tuwon Maryama ta kwashe komai takai Madafi kana ta Dawo Dakin Ta Dauko Jaririn Ta Mikamai Tana Fadin"Yaya kasan yaron nan Dakai yake kama..? Kayi ma yaya Hajara wayau..!

Yana Dariya ya karbesa yana Fadin"Kece kikayi mata wayau..Domin dake yake kama ke Hajara tayi ma Haihuwa kanwata.."Tana Zama agefensa Bakinta yaki Rufuwa tace"Da gaske Ni aka Haifama wannan yaron..? Cikin Tsausayinta yace"Tabbas..Shiyasa ma kece zaki Zabamai sunan da zamu sakamai kanwata..!

Hawaye suka kawo Idanuwanta Tayi Saurin Maida su Tana gyada kai kafin tace"A kullum Ina ganin nayi ma Sauran kanne Zarra wajen samun yaya kamar ka...Bantaba ganin mutum mai kyakyawan Zuciya ba irinka ba Yaya na Rasa da wani kalma zan Gode maka.."

Yaron ya Mika mata ta karba Yana Fadin"Karbi D'nki ki Zabi sunan da zamu Dinga Kiransa.."

Sai da Ta bata Lokaci Tana kallonsa kana Ta Dago Tana kallon Habibu da Hajara da suka Zuba mata ido Cikin Zubowar kwalla tace" MASTUR...! Mastur nake so a sakamai Yaya.."

Ko Gaddama bai yi mata ba ya gyada kai yana Fadin"Allah ya Raya Mastur Da"n Maryama Gobe da Safe Baba zai Mai Huduba da Mastur.."Farinciki ya kamata ta Hada da yaron da Ya Habibu taa Rumgume Habibun Shi kuma yana Lallashinta Dagowa Tayi Tana kallon Hajara Tana Fadin"Yaya Hajara baki ce komai ba..?

Mirmishi tayi kafin tace"Me zan ce Adda..? Gaskiyasa ne Haihuwan taki ce..Allah ya Raya Mastur.."Atare suka amsa da Ameen suna Mirmishi Har Inna Hasiya ta Dawo nan Maryama Take gayamata itama tace Allah ya Raya Mastur suna nan zaune sai ga Sule yazo Daukanta ya shigo suka gaisa da Su Baba da Yaya Habibun,Nan Maryama sai da Tagayamai ita ta sakama Danta Suna,sai murna take Dukkansu sun ji Dadin ganinta Cikin Farimciki Dukkansu.
Chapter 2 · 0% Book details