Sashe 91
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafiyar Mota yayi shiyasa sai Wajen 10pm na Dare ya iso Duka Zaratam matan nashi ba wacce ta Runtsa suna ta kiransa Tun yana Hanya Domin suji ko ya kusa karisowa,Tunda sukaji Hon da Budewar get kowacce ta Fito Daga Shashenta Cikin kayattaciyar kwalliyarta Diza Tayi mamakin ganin Rumana itama Cikin adonta na wani Less Riga da sikat ya kamata karma ma sabo ne Tayi Daurinta Zahra Buhari Tayi matukar kyau Ita kadai ta Fito kila Mansur Karami yayi barci ne. Abun ya sosa ran Diza ganin ai ita kadai ya kamata ta Tari Mastur saboda ita kedashi ayau din ammh Sai Rumana tazo Zata mata mata ranta ai Diza bat taji Kamar ta Mutu ba sai da taga Rumana ta Rigata isa ga Motar Mastur din Tun kafin ya gama parking ta Bude mai Murfin Mota Tanayi mai wannan Munafukin Mirmishin nata wanda Diza ta Tsana Da farko taso ta jure itama ta Kariso sai ta kuma Kafafuwanta suka gaza Daukanta ganin Mastur na Fitowa ya jawo Rumana jikinsa ya Rumgume kamkam Cikin Shauki da wani Farinciki da Muradi mai girma Wannan Mugun ganin da Diza Tayi yasa ta tsaya Cak Ta kasa gaba ta kasa Baya Ta kuma kura musu ido Tana jin Zuciyarta na Bugawa ganin in ta Cigaba da kallonsu Zatayi samun Bugawar Zuciyasa yasa ta juya kawai Zata koma Shashenta sai taji an Riko Hannunta ko daga yanayin Zafin Hannun ta Fahimci ko waye Mastur ne,juyo da ita yayi Lokaci Daya yana Fadin"Taya zaki juya alhalin baki zo kin min Oyoyo din ba Uhm Amarsu..! Yafada Cikin Zolaya,Lokaci Daya Ya Rumgumota jikinsa Har Lokacin yana Rumgume da Rumana itace ma ta Zame Jikinta tana yar Dariya ganin yadda Sam Diza Fuskarta ba Fara"a. Rumana Tayi saurin Saita kanta Tana Fadin"Bari na Shiga Ciki..Sai da Safe..! Tafada Tana Sakin Mirmishi Lokaci Daya Tana mikama Diza Karamar jakar data Dauko Daga Motan Mastur,Diza kamar bazata karba ba sai dai ta karba Fuskarta ba Fara"a Tayi gaba kawai ganin Mastur din ya Riko kafadan Rumana suna mgana kasa kasa bata san me suke cewa ba ita dai ta Shige da Sauri Har Tana Tuntube ganin in ta Tsaya ta Cigaba da kallonsu Zuciyarta Zata sakata aikata abunda bata yi Niyya ba. Diza tafi Minti Biyar da Shigowa Kafin ya Shigo Shima a gajiye yake sosai ga yunwa yana ji,Kamar Ta Sharesa sai taga Rashin Dacewar haka Ita ta Taimakamai yayi wanka ya Rama Salollinsa Kafin tajashi Saman Dinning ta Zubamai abincin Data Wuni tana Shiryamai yaci yana santi wanda Duk cin nashi ma ita ta Rika bashi a bakinsa,shima Bayan yaci ya koshi ya ci da ita sai da ta koshi kana ya kyaleta Daganan ya Dauketa Cak sai Cikin Bedroom dinsu,a tsakiyar gadonsu ya Direta Cikin Lokaci Ya Fara Nuna mata irin Zalamarsa da kewar ta da yayi itama a kage take Da sauri ta Rika Taimakamai Da Zafi Zafi suka Rika aikama juna Sakonnin junansu,Cikin Lokaci kankani suka Rikita juna bakajin komai sai Tashim Numfashinsu Lokacin da suka gama Raba junansu da Suturun Jikinsu. Shudewar Awanni uku Bayan Lafawar komai sun yi wanka Mastur ya Sanya karamin Wando 3quater,Ita kuma Diza Ta sanya wata Yaloliyar riga karama mai Budadden Kirji,Ta manne a jikinsa kanta na kan kirjinsa Tana wasa da kananun gashin Kirjinsa Shi kuma Yana Shafa gashinta kanta zuwa Bayanta Kowannensu yayi Shiru suna Sauraran Bugawan Numfashin juna. Diza Kuma acikin Ranta tana ta auna irin yadda Zata Tsara kalamanta Wajen Tambayan Maatur izinin Cigaban karatunta,Har dai ta samu matsaya Shiyasa ta muskuta Tana Fadin"Ya Mastur..!. Cikin sanyin muryanta Shima amsa mata yayi da Fadin"Ban yarda ba..Bana son wannan yaya..Ko ki sauya min suna kamar yadda Ruma ta sauyamin ko kuma ki rika kirana da Sunana kawai..! Yafada Cikin Rada in ba ita Datake kusa dashi ba bazata jisa ba Saboda Salon muryan Daya sa yayi mganar. Ranta Tuni yayi bakikirin Da jin sunan Daya ambata sai taji Bama zata iya Sauyamai sunan ba,Duk a abaya tasha Auna irin sunayen da zata Rika kiransa Dashi ammh a yanzu Daya ambaci Rumana ta Rigata sai taji abun ya Fita kanta. Cikin Haka ne taji yana Fadin'Umh ina jinki..! Sai alokacin ta Daidaita kanta Tana Kara Shafa Kirjinsa Ta Fara Fadin"Daman ina so na Tambayeka ne ko nace neman izininka..! Sai ta dakata Tana jan Numfashi Yana Kara Riketa yace"Izinin me Hadiza..? Dakyar ta samu jarumtar Cigaba da Fadin"So nake ka barni na koma makaranta..Nima ina so na Cigaba da Karatu In ka amince zan yi Jamb in na samu sai Daddy ya Min Hanya na samu ko nan Abu ne..! Tunda ta Fara mgana ya Cika da mamaki bai katseta ba sai da ta gama kana yayi Mirmishi kawai batare da yayi mgana ba,Sai da Tagaji ta Dago Tana kallonsa ta Dan Hasken Dumlight din Dake Dakin tace"Kaji..! Ajiyar rai ya Sauke kafin ya Mike Zaune Lokaci Daya ya saka Hannu ya kunna Hasken Wutar Dakin,Haske ya bayyana Suna kallon Fuskokin juna shi da ita. Wani irin kallon kin makara yayi mata kafin ya karkace kai yace"Ki bar wannan mganar bamai yuyuwa bace..! Yafada kai tsaye da Sauri Diza tace"Saboda mene..? Kura mata ido yayi kafin yace"Saboda ke kika zabi hakam Tun Farko..Lokacin da akayi ta baki Zabin karatun ai kince bkya Ra"ayi sai yanzu da Lokaci ya kure miki..? Ki bar mganar komawa makaranta hakan bazai Taba yuyu ba..! Yafada Lokaci Daya yana komawa ya kwanta Diza da wani Kololin bakinciki ya taso mata,yasa Hawaye ya Cika mata ido har ya Zuraro mata,Cikin Takaici tace"Saboda nace bana Ra"ayi a baya..? Ai ba Hujja bane..Tunda yanzu nace ina Ra"ayi sai abarni nayi in fa adalci Zakayi..! Yana jinta Kamar bazai Tamka ba sai chan yace"Wannan shine adalcin bakisan ance Apportunity Comes ones in Life ba..Kin samu Dama kin yi wasa da ita yanzu kuma ta Riga ta wuce ki Har Abada bazata Dawo ba..! Jin haka yasa ta Fashe da kuka Cikin kukan Take Fadin"Dole kace haka..Ni ka hanani Nayi karatu ammh ga Rumana nan ka barta Tayi karatu ta zama Likita bai isa ba yanzu hakama wani karatun zaka kara Biyamata Tayi Har sai ta gaji ita baka ce Damarta ta wuceta ba sai ni..Daman ba Tun yau ba na Fahimci baka min adalci Tsakanina da Rumana akomai ita kake ambata kafin ni kada dai ka manta Nice ka so Tun Farko ba ita ba..Ko yaya Matar sotafi Matar Chuse Daraja..! Ta karishe Fada tana wani Gunjin kuka Duka kalamanta Daki Daki suka Shiga kunnuwansa Lokaci Daya yaji bacin rai ya Rufeshi Zuciyarsa ta Fara zafi wanda yasa yayi saurin Mikewa yana bin Diza da wani kallon irin Kada ki kara mgana in ba Haka ba Ranki ya Baci. Bayason Bacin rai Shiyasa ya Mike Daga kan gado zai barmata Dakin ganin haka yasa Diza ta Dago Tana Fadin"Meyasa kayi Shuru..? Kayi mgana mana ai kasan gaskiya na Fada..Kuma indai Zata Cigaba karatu acikin Gida nan Nima sai na koma makaranta..! Yadda ta Fadi mganar ne yasashi Dawowa Cikin Dakin agabanta ya Tsam yana Binta da kallo kafin ya Fara mgana Cikin bacin Rai"Rumana zata Cigaba da karatun ba iya anan Gida Nageria ba in kasar waje take son Zuwa zan kashe mata Daga naira Daya har Miliyan Dari tayi karatunta..Ammh ke Biyar dina bazan kashe akan ki koma makaranta ba Infact ma bada Izinina ba Ballatana yardata ba..Sannan mganar Matar so ko ta Chuse kin Jahilci Lamarin Soyayyah Diza yes ban yi miki karya ke na Fara so kuma ke Zuciyata taso har yau har gobe..Na yarda An aura min Rumana ba domin bana ina sonta ba ammh Tafi karfin matar Chuse a wajena Domin ita din wata kaddara ce mai Daraja da kima awajena..Tunda nake da ita Bata Taba maidamin mgana ba bata Taba fada na Fada ba,Bata tabamin Korafi ba,Bata taba Ganin Laifina ba Ita din mace ce mai Uzuri Biyayyah kyawawan Hali da sanin yakamata Tarbiya natsuwa da Yakana Shiyasa Cikin Lokaci ta Shiga Raina ta mamaye Fili mai girma acikin Zuciyata Ta samu girma mai girma acikin Zuciyata wanda Wlh Tallah zan iya Rantse Miki ke Dana so baki Samu ba..Ki Kama kanki da Harshenki akan Rumama Tafiki Daraja awajena Zuciyarta mai kyau ne a kan kowa bata Taba Nuna Kishi ko kyashi akanki ba Ammh ke ba Tun yanzu ba na Nadade dalura da Take takenki akan Rumana Ke banda ma Sakarci Matar datake kula da Danki Taci kashinsa da komai nashi bata Yarda ta samu Cigaba ita kadai ba sai dake ammh ki na Mganar Komai sai nace ita? Kada ki manta itace Matata ta Farko Uwargidata,Kuma bari na gayamiki wani abu guda Daya ko abaya Ba kin Rumana nake ba sai dai ke Zuciyata take so..Ammh Wlh Tallahi Zuciyata na Daraja Rumana tana Burgeni har wani Lokacin In yi ta addu"an Dama ace Dama ace Rumana ta Zama ke Diza Saboda yadda komai nata yayimin a Tsagin danake son mace ta kasance kuma karatu Rumana Shine Burinta Bani na Fara sa mata Burin Tayi Karatu ba ita din da Abunta na ganta ita ta sani na kara Tabbatar ma kaina Duk wanda yasa abu a ransa zai iya to Tabbas zai iya..Ki shiga Hankaliki Diza na Fadamiki..! Ya karishe Fada Cikin Zafin Zuciya kafin yaja Blanket da Filo ya Fice Fuu Lokaci Daya yana Rufo mata KofarBedroom din da karfi kamar zai Balla nan ya barta ta Baje akan gado Tana kuka da Ihu Tana Fadin"Rumana .!Rumana!kin gama Dani kin gama da komai nawa..! Haka Diza Take Fada tana Rafzan kuka Kamar ance Uwarta ta Mutu. Haka Mastur ya Fito Falo ya kwanta kan kujera yana Sauke Numfashi Bacin ransa na Raguwa Lokaci Daya yana mamakin Diza bata da Kirki ko kadan Tunda Har zatayi iya Fadin haka Rumanan Data Shige gaba wajem Tabbatuwam auransa da ita ammh yau itace take Fadin komai sai yace Rumana..?kalaman sun batamai rai kuma mganar karatu bazatayi shi ba,ba Domin bai da kudin da zai Biya mata ba sai Domin ya nuna mata Darasin haka a rayuwa sai dai ta Cigaba da abunda ta zabar mata kanta. Ranar Suka kwana A bambamta waje,Diza a Bedroom ta kwana Sai shi kuma afalo Diza kwana Tayi kuka da wani Tsanar Rumana acikin Ranta,Shi