← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 94

Sashe 92

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma Barcinsa yasha bayan Ya watsar da Sha"anin Diza Tana ciki da asuba ya Shigo yayi wanka ya saka Jallabiya ya Fita kuma Tunda ya Fita bai Dawo ba sai Wajen 10pm na Safe Ran Diza kamar Tayi Bindiga saboda Takaichi Domin Tana Da Tabbacin Shashen Rumana yaje yayi zamansa Taga shaida Domin Tare da Mansur karami yashigo,Duk da abunda ya Faru Tsakaninsu Jiya bataki tashi Tayi Breakfast, ba ammh Jibi abunda yayi mata Domin Data gabatar mai da Breakfast din a Dakile yace mata ya koshi,ga wani karin abun Haushi Mansur karami kiri kiri yaki zuwa wajenta ya makalema Mastur Daga Baya ma sai ya saka kuka yana kiran Anty Anty,Ran Diza ya Baci bata san Sadda ta Dugure mai kai ba Tana Fadin"Ba Anty ba Anto..Don Ubanka ba itace bace Uwarka nice nan na Haifeka..! Tafada Cikin bayyana Kishinta ganin bayan Mijin ma Har Danta Rumana Take shirin Kwace mata Mastur na wajen kallomta kawai yayi kala bai ce mata ganin Diza ta Fara Fita Daga Hayyacinta. Daukansa yayi ya maida ma Rumana shi kuma ya Dawo yayi wanka ya Sauya Kaya Riga da wando na kanfanin Armani batare da yace ma Diza ci kanki ba ya Zari key din Motarsa ya Fice Tana ta bakin Window din Shashenta ta gansa ya Fito Dauke da Mansur karami Rumana na Bayansa Cikin Shigan alfarma kamar sun san Tana kallonsu Suna ta Hiransu suna Dariya Cikin Begem juna agaban idonta Mastur ya Bude ma Rumana Mota ta Shiga kana ya Rufo ya koma ya Shiga bangaran Direeba ya tada Mota yayi Hon megadi ya Bude mai get suka Fice. Sai sulalewa kawai Diza Tayi anan wajen tana kuka,Kukan Data rasa na Wani Dalili ne na kwace mata miji da Rumana Tayi ko na kwace mata D"a ko na Mganganun da Mastur ya yabamata ne duk ta rasa Dalili ita dai kuka take da Dukkan Zuciyarta Ta kuma rasa mafita ko madafa. Ayayinda Ta bangaran su Mastur basusan Halin da Diza take ciki ba Domin tun safen nan suna Cikin Abu Samaru Mastur nayi ma Rumana Cuku cukun Fara Resedency dinta wanda Daddy ya kira Dr.Hambal shine ya wanci yayi musu Shige da Fice Basu Dawo ba sai yammah abinci ma a Cafteria suka Ci,Basu gama Komai ba sai zuwa gobe Za"a karisa Duk da Dr.Hambali yace ba mtsala Mastur ya Fitar da kudi Sosai kan karatun Rumana Abunda ya kara Girma acikin Idanuwanta,Anan asibitin Chika Zata Fara Karatun nata. Da suka dawo ma Hanwa suka yada Zango sai 9pm suka Dawo kana Mastur ya Raka Rumana Shashenta kafin ya iso Shashen Diza ya isketa Tayi kwalliya ammh Tayi Dama Dama da ita da Hawayen da kuka da majina Saboda Bakincikin Abunda Mastur yayi mata yau Tun dazu tagama Girki Tayi kwalliya Tana zaman jiran Sa ammh don Wulakanci sai yanzu ya Dawo gidan kuma ko kallo bata ishesa ba Ballatana wani abincinta haka ya Shige Bedroom yayi wanka ya Sauya kaya Daman yayi Sallar sa a Hanwa ya kuma ci Abincin Hajja. Shiyasa bai kara bi ta kan Diza yayi kwanciyarsa Hankalinsa kwance,bai san ya ta kare ba Domin bata kwana adakin ba da Safe ma wajen Rumana yaje ya karya ya Bige da ce mata Diza ce bataji Dadi ba ta ce zata je ta Dubata ya hana yau ma kamar Jiya Samaru suka wuni basu Dawo ba sai da komai ya kamallah nan da Sati Biyu Rumana Zata Fara karatu kan Bangaran yara wato paediatric Doctor kenan,Saboda Dr.Hambali yasa aka makala sunanta Cikin wadanda zasu Fara a Shekarar. Diza kuwa ba ita keda Mastur ba Sshiyasa da suka Dawo bata sakashi a Ido ba Cikin kwana Daya da yini Duk ta Fige ta Rame kamar ba Diza ba yar kwalliya,Rumana kuwa kwana sukayi Farantama juna rai ita da Mastur da Safe suna karyawa yace ta Shirya da ita zai Tafi porthercourt sai ta Dawo bayan Sati Biyu.,kafin ta fara karatunta Rumana Tayi mamaki ta Dago Tana kallonsa Domin ta gama Lura da akwai abunda ke Faruwa Tsakaninsa da Diza duk da batasan ko miye ba kuma bata so ta sani Tunda ba Huruminta bane taso tayi magana ammh bai Bata Damar haka ba Taga ya Dauke kansa bayan ya Hade Fuskarsa bayaso tayimai wani korafi. Rumana Tayi alkawarin zama da Diza Lafiya cikin Aminci bazata karya alkawarinta ba itace Amarya da ita ya kamata ya Tafi,Wata zuciyar tace mata ai yasan da itan ya nemeki..? Wata kuma ta kwabeta da Kada kiyi Haka Rumana ko bakomai kece Babba Wannan girman da Allah ya baki ki Rikesa. Da wannan Tunanin ta Shiga Shashen Diza da yammah Bayan Fitan Mastur da Mansur karami Koda ta Shiga Diza na Cikin Bedroom Dunkule cikin bargo Ta gama kukanta Barci ya kwasheta sai da Rumana Tayi ta sallama da Knooking kana ta jita Kafin ta taso Tazo ta Bude mata yanayin da Rumana Taga Diza sai ya bata Tsoro Cikin mamaki take Tambayan Diza ko Lafiya ganin yadda ta wani Yi iri da ita kamar ba Diza yar kwalliya ba. Diza Bata so tayi ma Rumana wani Rashin Mutumci Saboda Tana ganin Girmanta kadan Shiyasa ta kauda kai kawai batace mata komai ba ganin haka yasa Rumana ta taka zuwa ga Dizan ta Riko hannunta Tana Fadin"Don Allah Diza ki daina Daukana amtsayin Kishiyarki kiDaukeni a mtsayin yar"uwarki Kamar yadda na Dauke ki Don Allah..! Kalaman Rumana sun kashe ma Diza Jiki idanuwanta suka Ciko da kwallah ta Duba Irin Halin Rumana ko abaya Duk irin cin kashin Datayi mata bata Taba Daga ido ta kalleta ba Ta yarda da mganar Mastur Rumana ta Dabam ce kuma kyawawam Hallayarta su suka Sayo mata girma da kima wajen kowa ta Tuna Sanda Take Cikin Halin Rashin Mansur Rumana Tayi ta Dawainiya da ita Bata ko Damuwa da kanta koda yaushe Tana Tafe hanwa saboda ita uwa uba ga D'anta Da Rumana ta Daukeshi Tamkar ita ta Haifeshi ko Saboda Haka ya kamata ta Raga mata ta Daina jin Haushinta da kishinta,Mace ce wacce ta Sadaukar da komai nata saboda ita da Mastur bai kamata Rumana ta Chanchanci haka ba Sam. Ammh ba laifinta bane Laifin Zuciyarta ne Da kuma Halittarta na Mugun Kishi,Sai dai zata yi yaki Da hakan ko ta samu Zuciyarta ta samu Salama da Sukuni,nan da nan Nadama ta kama Diza ta fashe da kuka ta Fada Jikin Rumana tana Fadin"Ki yafemin Rumana don Allah..Ni bam chanchanci ki rika Kallona yadda kike kallona ba..Ni ban Chanchanta ba Zuciyata bata d...! Bata bari ta karisa ba ta Dagota ta Rufe bakinta Tana Fadin"A"a kada ki sake Fadin haka Diza..Ni wlh har acikin Raina banta Rike ki da wani abu ba..Haka nake Diza ko abokin Fada bani dashi Tundaga Rayuwar kuruciyata Har zuwa Girma na..Sai yanzu da na zama matar aure mace mai Daraja zan Chanza Daga yadda nake..? Kada ki Damu Diza na Fahinceki kowacce mace da yanayin Kishinta,Sai dai zan Baki Shawara ki yi kokarin Koyin yadda Zaki Sarrafa naki..Wlh Tallahi zaki sameni mai kiyayewa kuma mai aikin da Hadisin nan na Manzon sallalahu alaihi wasalam dayace Kaso ma Dan"uwanka Abunda kake so ma kanka..! Diza Sai ga Hawaye Sharri sun zubo Mata ta Riko Hannayen Rumana Tana Fadin"Nagode da Shawaranki kuma Insha Allahu Zaki Sameni yadda baki Zato ba..! Rumana Cikin Jin Dadi ta saka Hannu ta Share ma Diza Hawaye Tana Fadin"Yauwa ko kefa..? Ki je kiyi wanka Diza Amaryace kefa..Ki kalleki kin zauna ba kwalliya ba gyara,Ki kuma Shirya kayanki gobe Tare da Angon naki zaku wuce porthercourt..! Da mamaki Diza ke kallon Rumana kafin Tayi mgana Rumana ta Rigata da Fadin"Karki ce komai..Kedai kawai ki Shirya..! Kai Diza ta Kada Tana yi ma Rumana Godiya bata jima ba ta Koma Shashenta ita kuma Diza da karkashinta Tayi wanka Tayi kwalliya Tana kokarin yaki da Zuciyarta ta zauna Tana Dakon Jiran Dawowar Mastur sai chan Dare taji Dawowarsa Daman ta Guduri Niyar gyara Shiyasa ta saka Mayafinta ta baro Shashenta zuwa Shashen Rumana ta iske su suna Dinner Rumana taji Dadin ganinta nan ta tashi ta Tarbeta Mastur kallo Dayayayi mata bai kara ba,Kan Dinnig din Rumana ta kariso da Diza ta Ja mata kujera ta Fara Kokarin Serving dinta Mastur na ganin haka ya Ture kujera ya Mike Rumana na mgana yace ya koshi Zai wuce Daki Mansur karami ya saka Rigima sai da ya Daukesa suka Shiga Ciki Duk sai Diza taji ta Muzanta,Rumana ta gama yadda akwai Wata baraka Tsakanin Ma"auratan sai dai bazata ce komai ba Tunda Daga Dizan Har shi ba wanda ya Fadamata bazata shiga Abunda ba Huruminta bane,sai dai Tana Yi musu Fatan su Daidaita kansu. Rumana ita tayi ta jan Diza da Hira Bayan sun gama Cin Abinci suka Dawo Falo Tun Diza bata saki Jiki ba Har ta saki Jikinta da Rumana suna ta Hira Har bata san Dare yayi bama Sai wajen 10pm Rumana ta Rakata zuwa Sheshenta Tana kara Jadaddamata ta Shirya Tare zasu wuce da Mastur da to kawai ta Bita ammh ita kan Jikinta yayi Sanyi Tagama yin Nadamar Abunda ta aikata. Rumana koda ta Shiga Ciki Mastur da D'ansa sun Dade da yin Barci itama wanka tayo tayi Shafa"i da wuturi,kafin itama tazo Cikin takwanta,Ta shiga Tsakiyarsu Mastur ya Rumgumota Daga ita Har Mansur din Ya Hadesu waje Daya suka Shige Cikin Blanket Cikin Soyayyah da Muradi mai girma. Da asuba Mastur yana ta Shirin Tafiya yaga Rumana bata Shirya kayanta ba,Daman ya Fadama Hajja mansur karami zai dawo wajenta kafin su Dawo,Kuma har Mommy ya Fadama da Rumana zai Tafi wannan karon kuma sunyi Na"am da hakan Domin ko bakomai Zamanshi da matarsa yafi ya Rika Tafiya shi kadai Tunda Yana da Muhallin da zata zauna. Tana Tayashi saka Tektie dinsa ya Kalleta yana fadin"Kin Hada kayanki ne..? Kai ta Girgizamai Tana Fadin"A"a..! Cikin mamaki yace"ammh kinsan da wuri zamu wuce ko..?Rumana na Mirmishi Tace"Nasani Ta Shirya ai wacce zaku Tafi taren..! Cikin mamaki ya kallonta kafin yace"Ita wa..? Kai tsaye tace"Diza mana..itace Amarya da ita zaka Tafi..In na samu Hutu sai muje tare..! Mastur ji yayi Rumana ta gama Raina mai wayau da Hankali Saboda Haushi ko kara kallonta bai yi ba yana ji tana mai mganar Breakfast ya Dauki Jakarsa Yana
Chapter 92 · 0% Book details