Sashe 60
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rumana bataDamu ba ta Saka Mayafinta Ta Dauki Jakarta Daman kwandon Abincin ta kawo Shi nan Falon sai kawai ta Sunkuta Ta Fito,Sai da ta Tsaya ta Kulle Shashenta kana ta Karisa garesu Daidai Lokacin da Mansur ya Fito nan suka Fara gaisawa Rumana tace"Dakai zamu je Ranka ya Dade..? .Mansur Dayaji Dakakkiyar Farar Shadda Harda Babbar Riga yace"Kai Antynmu Harda ke..? Dani za"a je saboda akwai yan Tawagarmu ta party mu da zamu je Tare suna son gaida Baba.."Rumana ta gyada Kai Tana Fadin"Ba Shakka Honourable Mansur..Chairman sai kayi Tun yanzu ma na gama baka Kujeran.."Tafada Tana yar Dariya Shima Mansur din yana Tayata Diza Dake gefe Sai Hararan Mansur tske ta gefen ido Yake Shi kuwa bai ma ganta ba Rumana kuwa Yi tayi kamar bata ganta ba.
Rumana ta kalli Mansur Tana Fadin"Budemin Both na saka wannan Basket din. "kallon Abun Hannun nata yayi kafin yace"Anty Dr.Rumana wannan fa... ? Rumana ta wuce Tana Fadin"Nidai Budemin..Abun Mara Lafiya ne..'Mansur ya Murmusa Yana kara ganin girman Rumana ya shiga Motar ya Bude mata Booth wanda Diza na wajen ne da Farko jin haka yasa Ta tashi Daga wajen ta Zagaya ta Bude gaban Mota ta Shige Tana karamin Tsaki Ita kuwa Rumana bata ma san Tanayi ba Ta Bude Booth din ta saka Basket din tazo Mansur ya Bude mata Gidan Baya ta Shiga yana mata Tsiyan Matar Dcp ce Dole a girmamata.
Diza ta shaka Haka ta Hade rai kamar Tayi Kuka Sai da Rumana suka Fice Daga gidan ne suka Dauki Hanya Rumana ta kalli Diza Tana Fadin"Amarya Diza an tashi Lafiya..? Dakyar Diza ta amsa mata Shima Saboda Mansur ne Da ace su kadai ne wlh ko kallonta bazatayi ba yanzu anan Duniya ba wacce ta Tsana take jin Haushi irin Rumana..
Mansur Dake tuki ya Kalli Diza yana Fadin"Daman baku gaisa ba Firstladyta..? Ya kamata ki Rika Bata Girmanta a mtsayinta na Matar Babban Yaya,ki bita Har Shashenta ki gaisheta da kwana Ita din Antynm ce."Ya karishe Fada yana yar Dariya Diza Dataji Haka sai taji kamar ta Gunduma ma Mansur Ashar sai kuma ta Fasa kawai ta bame bakinta ta kauda kai Rumana kuwa yar Dariya Tayi batace komai ba Shina Mansur din Hankalinsa ya bar wajensu wayarsa aka Kiran ya Dauka suna mgana.
Koda suka isa Hanwa Tuni yan Tawagar Mansur sun iso mota Biyu 4matic Dayan kuma Doguwa ta Party ce irin ta Fita kamfe din nan sun iso suna ta Jiransa Sagir yana Ciki sai wasu Maza Har da magidanta wadanda suka Girmema Mansur din Diza Da Rumana Wajen Mommy suka Fara Shiga suka isketa itama ta gama Shirinta Harda Ferfesun kayan Ciki Dayawa ta saka mama Fadime tayi ma Mara Lafiya,Daddy bayanan Tun Safe ya Tafi Sokoto Direba ya tukasu Tunda yanzu Mansur zai kaisu Bayan sun gaisa Rumana ta barsu ta Fita Zuwa Gidan Hajja Duk da Mommy bata da masaniyar Rumana ta Riko wani abu ammh sai da Tayi ma Dizan Fada Taya zata je gaida Uban Mijinta bata Dafa Komai ba Sai Diza ta Tura Baki ta kalli Mommy tana Fadin"to ni Mommy me zan Dafa Don Allah..?gani nayi ba gari Daya ba kuma ai mansur yayi musu Siyayya gashi chan a Booth zamu tafin musu Dashi.."
Mommy Tana kallonta wani Takaichi na Cikata ta Sakarmata Dakuwa Tana Fadin"Kaniyarki nan..Ke bakisan Dubarun mata ba Khadija..Gidan fa Uban Mijinki Zamu.Mansur? Haka zaki je hannu sake kina Matarsa ai ko bakonai kyauta nada Dadi balle Kina sane basu da Karfi sosai Tallafinsu Mansur da Mastur sai iyayanku Nidai kam ba Halina kika Dauko ba ba kuma na Alhaji ba Chan kika Roro wannan Mugun Halin Shiyasa Bazan Fasa gaya miki ba Sai dai kiji Haushi Rumana Tafi ki wayau da Sanin Mu"amalan yau da kullum..Ki Duba ko nan Zata zo bata Taba zuwa mana Haka Hannun Rabbana ba sai ke sakara mara wayau.."Diza data kusa Fashewa da kuka Ta Mike Tana Fadin"Mommy kenan..Shiyasa naganta da Basket kenan.Itama ba Don Allah take ba Son a sani ne..'Mommy tace"Eh koma son asanin ne tayi dai Tafiki dai..Ai Daman na sani ba yadda Yarinyar Zata Taho hakanan.."Diza bata kara Jinta Mommy ba ta Fito Daga Dakin Cikin Fushi ta Sauko kasa Fuu ta Fice Daga Falon kamar ta Fashe da kuka komai sai ace Rumana ce kan gaba akanta Rumana ta kwace mata Masoyi ta kwace mata Dangin Miji ta kwace mata Iyayenta Komai Rumana Ta Tsaneta Har Abada.
Tana Fita Waje taga su Hajja da Ayya har sun Fito Allah Sarki Hatta Hajja da Kulan Abuncinta da Dafo ma mara Lafiya,Dole ta saki Fuska ta karisa suka gaisa Baba Habibu kuma yana wajen Mansur suna gaisawa da Mutanensa sai ga Mommy ta Fito Mama Fadime na Bayanta Dauke da Basket,Amotar Mansur aka saka komai Mommy suka gaisa dasu Hajja da Baba Habibu Mansur ma suka gaisa da ita da Sagir Shiga Mota sukayi Diza ko kunya ta Shige gaba Duk kuwa da Kyfta mata idon da Mommy take yi ta Nuna bata gani ba Rumana da Mommy da Ayya da Hajja suka zauna abaya..
Sune akan gaba Sauran Tawagan suka Bi bayansu,Baba Habibu na Tsaye yana Daga musu Hannu da Fatan Allah ya kiyaye Hanya.
Dayake Sun Fito da wuri Shiyasa 11am suna Tsakar Dakin Inna Zainaba Don ma basu yi Gudu Sosai ba Inna Zainaba duk ta Rude Ta rasa Ina zata saka kanta Ta Riga ta gama Sakewa Mansur kam ya mata Nisa,Tawagar yan party dinsu Mansur basu wani Dade ba Bayan sun Duba mai Jiki su ka bashi Alheri Sosai Masu 5k,Masu 10k azahar kadai sukayi suka Juya ko abinci basu Tsaya ci ba sun sha dai Fura da Lemo Su kuwa su Rumana Danwake da mai da yajin Daddawa Maryama Tayi musu sai gashi suna Ci cikin marmari Duka abinci da suka zo Dashi sun bama Inna Zainaba Baba Sule sai Maimaita Godiya yake musu Har yana kwalla Da Ayya ta Nuna mai Rumana amtsayin Matar Mastur ya kalleta Sai kawai ya Bude baki yana Fadin"Allah yayi Miki albarka yar nan..Keda Mijinki Allah ya Duba ku..Kina mai addu"a ko..? Wlh Na Tabbata Mansur kadai na Haifa ammh Habibu ya bani Ya"ya Biyu Duka Maza Mastur Mutum ne Matashi ne mai kima da Daraja da Sanin ya kamata,Koda yauahe yana Tafe hidima Dani ni da Iyalaina Kowani Sati yana Turama Maryama kudi ta Bankinta yace acire ayi amfanin Gida Dashi Baya wuni ya kwana Bai Kirani yaji yajikina ba..Aduka Sallolina Biyar ina saka sa Ina Fatan yadda sukaji kaina Shi da Dan"uwansa Mansur da Habibu da Alhaji Makocinku Allah yaji kansu suma.."Ya karishe Fada Hawaye suna Zubomai Sharr Sai Ayya ta Fara Sharan Hawaye itama Jin yana Hawaye yana Fadin"Allah ya jikan ki Maryama..Kin Tafi da Burin ganin kwanki aduniya gashi kin Haifi ko abunda kika Haifa baki gani ba Macen kirki kuma Tagari Tunda nake batataba Sabamin ba Yau gashi bakya Raye da kin ga Yadda Mansur ya koma Da kin ga Yadda Mastur Dinki Yaron da kika so shi kamar Ranki ya koma adalilinki Kaunarki ga Mastur Nima ya Shafeni yau bakya Raye Hatta da Yayanki bai Yarda Dani ba Suna kula dani da Ahalina Gabadaya Allah yayi Miki Rahma Allah ya sadaki da Mala"ikun Rahma Maryama...'
Ya karishe Fada yana kuka Sosai gabadaya Dakin suka amsa da Ameen Ameen Kowa Dake Dakin sai da yaji Tahowar kwalla,Mansur tashi yayi ya Fice kada yayi kuka gaban Matarsa Rumana ma sai da Tayi kwallah Mommy ma haka Hajja ne da Ayya kamar yanzu Akayi Rasuwar,Kewar Maryama da Rashinta ya Dawo musu Sabuwa Sai da suka Share kwallah,Inna Zainaba na gefe kanta na kasa bata da Cewa Domin tasan Ko ita ba tace ga abunda Maryama Tayi mata ba sai ma itace Tayi mata gashi yau Rayuwa wacce suka kira Juya,ta Haihu ta Rasu ta bar Abunda ta Haifa gashi yau Yana ta Dawainiya dasu da shi da Yan"uwan Maryaman gabadaya ai bata da ta cewa
Momny ce ta saka baki Tana ta bama Baba Sule baki kana yayi Shuru,sai kuma aka koma Hira Rayuwa da Shekarun Baya Matan Yayyinsa duk sunzo sun gaishesu da Mazajensu wasu da suke nan,Harda kwanukan abincinsu,Sakina ma Tazo Daga Gidan Mijinta,Zuwa 3pm sukayi Shirin Tafiya Tunda zasu Biya Ririwai,Kafin su tashi Tafiya Sai da Inna Zainaba ta Kwanke musu Kololinsu ta bada aka saka musu a mota,Mansur kuma ya Sauke musu kayan abincin Dayazo Dashi bayan ya bama Inna Zainaba 20k yace ta Rike na Cefane ya bama Baba Sule 20k yace na komawa asibiti da zasu yi wani Satin in ya samu Lokaci zai Shigo in bai samu ba zasu yi mgana ta waya Sauran Baffanin nashi ma Duk ya bisu da kudi wadanda basa nan yabama Matansu,Haka suka tafi suna Daga musu Hannu da saka Albarka Mardiya kuma tace Zata zo Insha Allahu Ashe Mansur ne yace tazo Domin sunyi mgana da Mastur ta Dawo nan Wajen Hajja ta zauna ta Shiga makarantan Boko,Tunda ga maryama na Tare da Inna Zainaba.
Ririwai sukayi Sallar La"asar gidan Inna Karime,Sun iske Tayi Dambun shinkafa basu Tsaya ci ba ta Zuba musu suka Dauki Hanya Dashi,Karfe 7:40pm na Dare suka Shigo Zaria sai da suka kai su Hajja dasu Mommy gida kana Sukawuce gida Gabadayansu agajiya suke Tun ballatana ma Rumana tun ahanya ta Fara barci bata saba Doguwar Tafiya amota ba Tafi yin Tafiyan Jirgi in zata Lagos Sama sama Tayi ma Mansur da Diza sai da Safe ta Shige Shashenta Sallar Mangriba tayi da Isha"i Ta Dibi Ruwam Zafi a Fulas ta Sha Tea tayi Shirin kwanciya ta kwanta Saboda Gajiya Washegari ma Allah ya Taimaketa ba aiki sai ta Huta Maryama ta kirata awaya tamata bangajiya har ta bata Baba Sule suka gaisa yana ta Godiya da Saka musu albarka Da suka yanke Kiran Rumana sai ta kara Tsinkewa da Lamarin Mastur kowa Kaji ya Bude baki badai kaji ya fadi Sharrinsa ba sai da alhrrinsa ta Fahimci a wajen kowa Shi mai Kirki ne awajenta ne Bashi da Kirki da kulawa ko kadan.
*****
*Bayan wata Hudu..*