← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 94

Sashe 41

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mansur da kansu yaje Maruka yakai ma su Baba sule kayan saka Ranar chan ya kwana ma sai Washegari ya Dawo Kannensa suna ta Murna,Sakina Tana Gidan mijinta Maryama ma ta koma makaranta Sauran kannensa ma Yasaka su a makaranta harda mardiya Rayuwar Gidansu ta Inganta Ya Taimaka ma Mahaifinsu ya Taimaka Yan"uwansa bashi kadai ba Hatta Mastur wani abun Alherin sai yazo Baba Sule zai ce mai Mastur ya Turo musu kaza ya Turo musu kaza,Shuru kawai yake sanin Halin Dan"uwan nashi Domin da Taimakonsa ya gyara Mu"amalansa da Yan"uwansa da Mahaifinsa shi ya Biya Ririwai yakai ma Inna karime Bushara Dataji An sakama Mastur Ranar aure Harda kuka nan Inna Karimen ke Fadamai wai ita nan Jiran Mastur din Take Mansur Dariya ta kamashi Yana Hanyan Dawowa yana Dariya Bisa Hanya Tun ahanyan ya Kira Mastur ya Labartamai Shina Abun sai da ya sakashi Nishadi Diza kuma Tun Ranar basu kara mgana ba ta Dai Turomin Sakon SORRY sai kawai yayi Mirmishi ya kyaleta yasaka aransa ko Diza bata sonshi Haka zai yi Hakuri da ita ya Aureta Domin shidai yana Sonta In bata Cikin Rayuwarsa bazai iya Rayuwa ba.
Yana komawa gida ya Labartama su Hajja Ayya nata Dariya Hajja dai bata ce komai ba Baba Habibu kuwa kai kawai ya Jinjina aransa yana Fadin kuruciya ce kawai
Diza Dataga mansur ya Dauke mata Kafa da kanta Tayi Bikonsa Domin Mastur ya Kirata yayi mata Godiya Bisa Cika alkawari da kuma alfarman Da tayi mai na auran Dan"uwansa Mansur ya Gode Har Abada bazai manta da karamincinta Da wannan Dalilin ta Fahimci Har Abada abunda take so yayi mata Nisa Gwara ta Rumgumi Mansur Shine Kadddaranta.

Rumana ta Fara Damuwa ganin Tunda aka saka Ranar auransu Mastur bai taba kiranta ba ko Sau Daya ba sai dai taji Umma ko Abba suna Fadin sun yi mgana Tun Tana Danne Abun har ya Fara Damunta ta rasa wa zata Fadamawa Taji Dadi,ammh Sai take mai Uzuri Saboda yanayin aikinsa Tayi kokarin Ta Kirashi sai kawai ta kyaleshi Tana so Ta Fahinci ya Damu da ita ko a"a abunda bata sani ba Mastur ba ta ita yake yi ba yanzu aikinsa kadai ya saka ma Gaba ba Dare ba Rana sai yakai 10pm a office kuma 7am yake Fitowa Barci Ragagge yake yi ya Lura maida kai ga aikinsa shi zai Ragemai Tunani ya Tashi Daga Miskili ya koma Uban Miskili Domin yanzu mgana ma Tafi mai Wahala Fiye da Baya Sai ya kwana Biyu bai Tuna da ita ba balle Zencen auransa Diza ce kadai bata Taba Gushewa aransa ko na Sakwan Daya ba Mastur yasha Rayawa a aransa ya siya Giya ya Farasha Indai Zata Dauke mai Tunanin Diza sai kuma ya kasa Tuna Irin Tarbiyan Baba Habibu da Hajja Garesa sai yake ta addu"a kawai ya maida ma Allah Lamarinsa.

Mus"ab kuwa yasha Takaichi da Mansur ke Fadamai Zencen Auransa da Diza da mganar Runana da Mastur domin Alhajinsu ma bai gayamai ba yaji Takaichin biye ma Rumana Da yayi bai gayama mahaifinsa ba Daga baya sai ya barma Allah komai Yayi Tunanin Dama ba Matarsa bace Suka cigaba da Shirye Shirye da Mansur Domin sun Zama Abokan juna Tun Haduwarsu a Lagos.

Mansur Zumudi har ya Fara mganar kayan Lefe Hajja yayi ma mganar sai tace basai sun Wahala ba Mommy nan Harkantan ce yar kasuwa ce su Bata kudi zata Hada musu kaya na gani na Fada Baba Habibu ma Dayaji yayi Na"am da mganar jin haka yasa Mansur ya Kira Mastur ya Tuntubeshi shi kuma yace ma Mtsala in sunyi mgana da Mommy ko nawa tace yamai mgana sai ya Turo mata Mansur kafin yayi mgana da Mommy sai da yayi mgana da Diza kan kayan Lefen Tace Tabbas Mommy tasan kan kaya Sosai,ba musu yaje da kansa yayi mata mgana Tana Murna Wai Zata Hadama ya"yanta kayan aure Tace Kowannsu ya bada miliyan Daya da Rabi ita Zata ji da Sauran itama amtsayinta na uwa Zata bada nata Gudummuwar,Mansur ya kira Mastur ya gayamai Daya Tashi Turowa sai ya Turo 4million nashi Dana Mansur,Mansur kamar ya suma saboda murna yaje Falon Hajja yana ta rawa yana kwaso Shoki wai ya zama Dan gata auransa Diza komai yimai akayi Kowa sai da yaji Labari yana ta saka ma Mastur albarka ashe bayan nan ya Kira Mommy ya Tura mata 100k yace ta Siya ma Ayya kaya da Hajja da Inna karime sai Shaddodi na Abba Dana Baba Habibu sai Daddy sai Ita da Umma yace in ya samu albashi Watansa zai ciko mata kudin Ta barshi kawai kowa yaji wannan abun Alkairin sai saka albarka yake,Shi kuma Mansur Dayaji haka sai ya bada wasu kudi a Siyoma kannensa, kaya da Mahaifinsa sai Inna Zainaba,Sai kawu Usman da Balaraba Saboda yi ma Baba Habibu kara.

Mommy ta san Size din komai na Diza na Rumana ne bata sani ba sai ta kira Umma sukayi mgana Umma tace ai yarta ce ta Kirata suyi mgana Mommy ta kira Rumana tace ta Turomata Size din Dogayen Rigunanta da bra da pant da Takalma Rumana Taji abun kamar Daga sama Tana ta mamaki bata dai yi mgana ba sai ta Tura sai Daga baya Umma ke Fadamata Lefensu ne su Mastur suka bama Umma kudi Zata Hada musu Rumana Tayi ta mamakin Mastur an kai ga Hada lefe ammh ango bai taba Kiranta ba Ranar ta Kauda kunya ta Kirashi Har sau Biyu bai Daga ba Sai Waahegari Tana Wajen aiki ya Kirata kamar bazata Dauka ba sai ta Daga bayan sun gaisa da Tambayan aiki da Mutanen gida,kamar yasan Tunaninta sai ya bata Hakuri kan yanayin aikinsa na karancin Lokaci Tana Sonsa sai ta karbi Uzurinsa kafin ya yanke kiran take Tambayansa yaushe zai zo..?
Abun sai ya bashi Dariya ma kawai Ita yanzu in akace mata zai zo sai ta yarda..? Cikin Dakiya yace"Kina so nazo ne..?
Kamar yana kallonta ta gyada kai Tana Fadin"Eh mana..Ina son na ganka..Na Dade bamu Hadu ba.."
Mastur yace"Uhmm Zaki ganni Soon..Mu da zamu zama Miji da mata..Ba zan yi miki alkawari ba nazo nayi Failing dinki ba..Kinsan Allah ba Lalle bane naje Zaria kafin Bikin ne sai Lokacin Komai dai ake ciki u can Tok on phone.."Rumana bata da tacewa sai Fatan Alheri kawai Daganan suka yanke kiran Ta Dade ta auna wasu abubuwa ganin bamai Tallafamata ta Fahinci wani abun Dole ta watsar da komai ta Cigaba da aikin gabanta.

*********

*Bayan Wata Biyu..*

Lokaci yana ta Tafiya Cikin Nasara da Tsarawan Allah Biki kuma yana ta gabatowa Kuma Shiryen Shiryrn nata Tafiya yadda ya kamata kamar Barayin Mansur shi dai yana ta Shirinsa Mastur kuma sai abunda Mansur ya kirashi ya gayamai Sukan yi waya da Rumana itama sai in ta Kiraahi Tagaji da Korafi Ta Hakura Domin Ta Fahinci Haka Halinsa yake...
Bangaram kayan lefe Mommy Ta gama Hada komai akwatuna Kowanne 7,Both Diza da Rumana Cike da kayan alfarma masu Tsada kayan kuma da Mastur yace a siya an siya komai har an bama kowa nashi yana ta saka albarka Mansur ma ya aika ma su Baba sule nasu suna ta saka albarka nasu Hajja kuma Diza yasa takai Musu Dinki inda suke kai nasu Mommy Duk iri Daya ta Dauko musu Atamfar Domin suyi anko Hakama Daddy da Abba da Baba Habibu Shaddodin iri Daya ne suma Domin suyi anko Ranar Daurin auran.

Mansur kuma bai jira Mastur ba yaSiya Shadda kala uku Da Yadi kala Daya ya Bada Dinki nashi Dana Mastur Tunda Shi ko Zuwa ma bai yi ba kullun Excuse kan aikinsa,Bangaram kaya kuwa Mommy na gama Hadawa ta kawo nan Wajen Hajja ta Zube su Baba Habibu kuma yace iyayan Mansur Zasu zo su gani kafin ashirya kai na Rumana Chan Sokoto in an Dawo sai akai na Diza Tunda ita Gida ne haka kuwa akayi Inna Zainaba da Matan yayyin Baba Sule sun zo sun kwama sunga kaya suna ta saka albarka da Zasu koma Baba Habibu yayi musu na Komawa sukace sai Lokacin Sha"anin zasu Dawo Kai kayan Rumana kuwa Inna karime sai Balaraba sai Mommy Sai Mansur Dake Namiji aka Tsara Tafiyan Ajirgi Zasu Tafi Mastur yana Daga Chan shi dai i an Kirashi mganarsa Eh kawai bayacewa komai kan Al"amarin.
Ana Bikin Saura Sati uku suka Tafi Sokoto suka Hadu da Dangin Abba dana Umma yan Wamako sun zo Taransu Dayake abun Duk Gida ne sun ga karba da karramawa nan suka kwana sai Washegari suka Daawo Zaria Ranar da suka Dawo Da Daddare su Ayya da Inna Balaraban da karime suka kwashi na Diza suka maida su Wajen Mommy Tunda Daman su suka Hada Daman Chan Sokoti sun je da 50k kudin Dinki Diza kuma Daman sun gama mgana da Mansur Washegari Tun Safe suka kwaahi kayan suka Tafi kai Dinki Shi ya Biya komai da komai .

Sai Shirya Shirya kawai ke gudana A tsaida za"a Dauran Dukkansu agarin Iyayansu ne Za"a fara Daura auran Mastur da Rumana a Wamako sai a Wuce Tureta a Daura na Diza da Mansur Daganan sai a Dauki Amarya Rumana su yada Zango Zaria gidan da Daddy ya basu a Hanwa Loswost ne Tuni Ya gama Biyan kamfanin Marhaba sun zo sun Tsarama kowacce Flat dinsu,Su mommy da Umma kawai bangaran labulai da Zannuwan gado sai kayan kitchen zasu ji dasu,Flat ne manya Guda Biyu Suna kallon Juna masu Dauke da manya Falo Guda Biyu sai 3 bedroom each yana Dauke da Tiolet,sai Kitchen,Haraban gidan kuma Kato ne wanda Zai Dauki akallah Motoci Fin Goma zasu Faka wasu basu matsu Juna ba Mommy da Hajja da Ayya da Baralaba sunje sunga Gidan suka Dawo suna saka albarka Diza ma Mansur ya kaita Ta gani Tafi Tsayawa kyan Tana ganin Shashen Mastur da Runana Tana auna Taya Zata iya wannan Sadaukarwan Zasu Zauna Gida Daya da Mastur da Rumana Kamar Rauninta zai iya Bayyana.
Chapter 41 · 0% Book details