← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 94

Sashe 34

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy na gama Waya da Mastur ya kalli Mommy yana Fadin"Hashashemu ya zama gaskiya..Mansur dai yar gida Za"ayi da yarki Khadija.."Da sauri Mommy ta Washe baki Tana Sakin guda Daddy yana Dariya yace"Shi Mastur yace bai da wacce yake so kuma baisan ina zai samu ba.."Mommy tace"Kaji wani Zence..? Kamar sa ne zai ce ina zai samu mai Sonsa..!?

Daddy ya mike yana Fadin"Ki barni dashi..In yazo ban ji wata mgana ni Zan Samo mai wacce ta Dace dashi.."Mommy Ta Bisa da kallo Tana Fadin"Wacece ta Dace dashi Alhaji..? Yana Shiga Cikin Bedroom dinsa yace"Nima bansani ba Tukunnah.."Daga haka ya Shige ya barta Tana Tunanin wacece bata bama mganar Muhimmanci ba Ta koma Murnan Abunda Daddy ya gayamata Bata Bakinciki Domin Mansur ya auri yarta Daman Ta Dade Tana Hangen Dacewarsu da juna ba Tun yau ba,Kamar tatashi taje Ta gayama Diza sai kuma ta kwabu kanta tace yaran Zamani yanzu haka kar suke kallonmu Farinciki yaki barin Ranta Taso ta Kira Hajiya Farida Ta gayamata abub Arziki sai kuma Taga Dare yayi ta bari sai gobe Tashi Tayi ta Tattara kololin abincin da Daddy ya gama ci ta Kai Kitchen dim kasa da Mama Fadime suka Hado suka ma Juna Sai da Safe Dakin Diza ta Leka Ta iske tayi barci Wayarta Ta Fadi gefe Dariya Tayi ta Shiga Dakin ta gyara mata kwanciya ta Dauke mata waya ta Dora saman Side Drower din gadon ta KasheMata Wutan Dakin ta Fito Bayan taja mata Kofa Sama ta Haura zuwa Falonta sai da ta Rage Hasken Falon kana ta Tura Kofar Bedroom ta Shiga ta maida kofa ta Rufo.

****

Bangaran Rumana kuwa Ta shiga Tashin hankali na Damuwa na Rashin ganin Amsan Sakon Mastur Zuwa gareta,bayan ta Riga ta gayamai Sirrin Zuciyarta Wanda kuma Batayi nadama ba,abun yaki barin Ranta Ta shiga Damuwa Rashin Sanin makomar Soyayyarta.

Gashi Bayan Dawowarsu Daga Lagos Mas"ud nata kiranta Bata san ina ya samu Lambarta ba,ya riga ya gayamata Sirrin Zuciyarta kuma Ya gayamata He is Ready,aure yake so in har ta bashi Dama zai gayama Mahaifunsa Ita ta Dakatar Dashi Ta gayamai akwai wanda Take so ammh bai Hakura ba kiran Safe Dabam na Dare dabam yana Beging dinta Ta soshi Text kuwa baya gajiya na kalaman kauna Gareta,Ammh bata Taba maida kai ba Bashi bane agabanta Wanda Take son wannan Kulan Daga gareshi bata son makomarta ba,abun ya Dameta yau haka Tatashi Sukusuku aikin Dare tayi Wato Call,Sai wajen 7am na Safe ta baro Cikin asibitin a Motar ta Zuwa Gida Ta gaji Ga barci acikin Idanuwanta ga Damuwa sai taji kamar ta Kirashi sai kuma ta kasa batasan me Zata ce mai ba ko Sirrin Zuciyarta Dakyar ta iya Fadamai shima Sakon Text masages.

Haka ta shiga gida Tana layi saboda gajiya da Barci,Da juma ta Fara cin karo Ta gaisheta da kwana bata iya amsa mata ba ta mika mata Karamar jakar hannunta da Lapcaot dinta Ta Haura Sama Juma ta Biyo bayanta Zuwa Dakinta Tana Shiga gado kawai ta Fada tana jin kamar kanta na Sara mata nan Saman gadon juma ta ijiye mata kayan ta Fita zuwa Kasa Kitchen ta shiga Domin Hadama karamar Hajiya Abun karyawa.

Rumana ta Dade kwance kafin Tatashi Tana Rangaji ta Fada Tiolet Tayi wanka Tazo ta Shafa Lotion dinta ta Sauya kaya zuwa Saukakkiyar Doguwar riga,Koda taFito Har Juma ta Hayo mata da Breakafst dinta Tea kadai tasha Ta Fito Daga Dakin Zuwa Falon Ummanta ta same su ita da Abba suna karyawa nan ta zauna kusa da Abbanta Tana gaishesu da kwana suka amsa mata Cikin Fara"a da soyayyah.

Umma ce ta kalleta Tana Fadin"Lafiyanki kuwa Ruma..? Naganki kamar baki da lafiya..? Rumana ta Sauke Idanuwanta Cikin gajiya Tace"Bakomai Umma..Gajiya ce Kawai sai Dan Ciwon kai dana Dawo Dashi.."Da Sauri Abba ya Dafa Kanta yana Fadin"Ayyah Sannu..Tashi kije Ummanki Ta baki Mgani kisha zuwa anjuma in bai sauka ba kije kiga Likita.."Umma ta mike Tana Fadin"Bari na Dauko mata panadol,tasha..Gajiyan Aiki ne Da Zirga Zirga.."Tafada Tana Shiga Cikin Bedroom dinta Sai gata Ta fito bata Dade ba,Ta mika ma Rumana panadol din Ta karba Lokaci Daya Umma ke Fadin"Kin karya..? Rumana ta gyada kai Tana mikewa Tace"Bakomai fa Umma..Call din ne ke Wahalardani baka samun yi  barcin kirki.."Abba yace"Watarana sai Labari Rumana..Allah ya bada Lada.."Umma na Zama Lokaci Daya Tana Dariya Tace"Ameen dai..Ammh fa Gwannati na Biyansu Alhaji.."Shima Dariyan yayi yana Fadin"Duk da haka Aikin su na Taimakon al"umma ne.."Rumana na jinsu bata ce komai ba ta Fice suka Rakata da Ido Cike da Tsausayinta da Kaunar Diyar nasu Tilo Dasu ka Mallaka.
Rumana na zuwa Daki Ta Sha panadol ta kwanta Sai barci Bata Tashi ba sai wajen 10am na Safe wanka ta sake yi Taji tana jin yunwa ta fita zuwa Kitchen Ta Hada Complex ta Dawo Daki Bataji Motsin Goggo Jummai baTafi Tunanin Tana Dakinta ta kwanta Sama ta Haura Tana Tunanin sai Zuwa anjuma Zata Shiga ta Dubata.

Kan gadonta Ta Haye da Mug din Da Cokali Tana shan Complex din a Hankali,Lokaci Daya ta Jawo wayarta Tana Latsawa Kiran Basma Tagani Lokacin kila Tana barci ne,Kiranta Tayi suka gaisa Ita Basma a Zaria Abu Take Intenship dinta Labari sukayi kadan kafin suyi sallama Kurama wayar ido Tayi Tana wani Tunani bata son ta Kirashi Bata da abun Fada sai kawai ta yanke Shawaran Turamai Sako da Sauri Ta ijiye mug din hannunta saman Side Drower din Gadonta ta Fara Rubutamai Sako.

_Salam ya Mastur How are u Doing..? Kaga sako na baka ce komai ba..? Ko baka sona ne..? Kuma ban yi maka a mtsayin irin Macen Dakake Muradin ta Zama Abokiyar Sirrinka ba nan gaba..Plz ka Fadamin mtsayina awajenka..Nidai kaji Sirrin Zuciya Am in love wit U..Bazan iya Rayuwa mai cike da Sukuni Da Jin Dadi ba in baka..Plz Help ur Sister Rumana Muhammad Wamako.._.

Tana gama Rubutamai ta Turamai Cikin karfin gwiwa ta koma ta Kwanta kawai jin komai ya Daina mata Dadi wayar na Hannunta Tana Bukatar amsar ko Cewarsa So take ta Dakatar da Mus'ab kafin ya Sanar da Mahaifinshi mgana ta Dawo kunnin Abbanta Tana da Tabbanci bazai mata auran Dole ba ammh kuma bazata iya mai gaddama akan komai ya Umarceta ba.."

Suna Tsaka da Meeting yaji Shigowar Sakon Rumana bai Duba sai da suka Tashi Daga Taron ya kuma Office dinsa ya Zauna kana ya Duba Sakon nata kalamanta sun kara kashemai Jiki kamar wani mara Lafiya,Gabadaya yau yazo dai Office ne ammh bayajin zai iya yin wani aiki kasala Duk ya Rufeshi da Nauyin Zuciya Shi yama manta da Sakon ta Domin Halin Dayake Ciki yafi Tunanin Rumana sai da yaga Sakonta ya Tuna da ita da Abunda ke Tafe da ita.

Kansa ya Dafe yana Tunanin Rumana Zata Kara Sakashi Cikin Wani Halin Daya ke Fatan fitansa nan kusa sai dai kalamanta sun kashemai jiki Sosai Yasan Zafin so da Dafinsa Tunda yana cikinsa Har yanzu bai kai ga Fita ba in yace Yana Sonta Domin ya Farantamata ya Cutarda ita..Zuciyarsa bata da wani Wajen da Zata sakata Har Abada Bazai ce Rumana ba ta Cika macen da kowani Namiji zai iya mallakanta ba No Rumana mace ce Kin kowa kim wanda ya Rasata sai dai ba ita Zuciyarsa taso ba Bai taba kallonta da wani Siga ta Soyayyah ba Kada ya barta Jira  ya kasa maida mata da amsa sai da yaga wunin Ranar Kiranshi ta Dingayi Sai da ya koma Gida Bayan yayi wanka yayi sallah kana ya Dauko Wayarsa ya Rubuta mata sako.

*Wslm..Rumana ya aiki..?Ko Daya Taya zan ce bana sonki.? Alhalin kin mallakin Duk Abunda wani Lafiyayyan Namiji yake nema wajen mace..! Kawai dai bana so ki shiga Damuwa ne Saboda ni ko ki zauna kina Bata Lokacin ki akaina..Ni ba yanzu Zanyi aure ba Rumana..Kiyi Facing din Reality dinki Ina Miki Fatan alheri Arayuwarki..Mastur Habib Doguwa..*

Yana gama Tura mata ya Kashe wayarsa ya koma ya kwanta yana Jin kamar bai kyauta mata ammh kuma Hakan shine Daidai.Inhar ya amsa mata yayi mata karya kuma yaci Amanarta yagayamata yana sonta ahalin bai taba sonta ba auranta ayanzu Tamkar wani Nauyi ne Za"a Doramai akansa Wanda kuma Faruwar hakan kamar wani babban al'amari ne na ganin irin Halin Dayake Ciki na Kokarin Binne Diza Daga Cikin Ransa.

Rumana kuwa Lokacin Data ga Sakon Mastur Kamar ta Suma Saboda bakinciki Ta Takaichi Tayi kuka awannan Daram har ta bama uku Lada Kenan ya Mastur baya sonta..? duk irin Tarin kaunar Da take mai..? Sai wata Zuciyar tace mata a"a ba haka yace ba yace ne kada ya barki kina Jira Ba yanzu zai yi aure ba Tuna haka yasa taji Sanyi aranta Tayi alkawarin Zata iya Jiransa ko nan da Shekara Goma ne in dai zai aureta Bazata Damu ba Koda gari ya waye Ta Shiga Dakin Umma gaishe su ita Abba sai da sukayi mganar Kumburin idonta sai tayi karyan Da Safan ne Wani abu ya Fada mata Abba yace in ta isa Wajen aiki ta bada a Dubata Inda wata matsalan tace to,allah ya taimaketa aikin Safe gareta 2pm zata Dawo Gida sai abun yazo mata da sauki ammh ko achan asibitin Sai da abokan aikin nata suka Fahimci ba Lafiya ba saninta mai kazar kazar da Zafin nama ammh yau ta zama wata so Silent da ita.

******
Chapter 34 · 0% Book details