← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 94

Sashe 52

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Tunda suka Dauki Hanya ba wanda yayi Mgana Tsakanin Mastur ko Diza Mansur ne ma Ke ta Surutunsa Da Mastur wanda yayi kamar bai Jisa ba,Yana Ta fama da Zuciyarsa Domin ganin Diza kamar Fami ne ga Tabon Daya Riga ya Binne acikin ransa haka Itama Diza sai taji Gabadaya Jikinta ya Mutu Ta Madubin da Mansur yasaita ya Dinga kallonta take kallon Fuskar Mastur Daya Hade rai kamar bai Taba Dariya ba,Kallonsa Take Cikin So da kauna da wani Muradi mai Girma ayayinda Gefe Daya kuma Mansur ke aika mata da kallon kauna Tuni Wata Zuciyar ta kwabeta Data Kallo Gefen Rumana Taga Hankalinta ma yana Kan Hanya ne Tana Bin Ko"ina da kallo Saurin Ta"awizi Tayi acikin Ranta Tana Neman Gafaran Allah Hakika Bata son Mansur ammh akwai Shakuwa da Fahimtar Juna atsakaninsu Sosai In Har tace Ta taba ganin Fushin Mansur tayimai karya Mutum ne mai Dadin Mu"amala da Dadin Zama bataji mamaki ba In Taga Dimbin Magoya Bayansa a Bangaran Siyasan sa Haka Jininsa yake shi na Kowa ne karya ne kayi Mu"amala Dashi na Wuni Daya bai Shiga Ranka ba yana da Sadaukarwa kan Abunda yake so ko akanta ma Mansur yakai makura Shiyasa Bata ji Tana Nadamar Auransa ba Ko Bakomai ta auri Mai Sonta Wanda Zai Ta Hidimta mata Har Karshen Rayuwarsa Mastur ya Riga yayi mata Nisa Nisa kuwa na Har Abada.
Ajiyar Zuciya ta Sauke Daidai Lokacin da Mansur Dake Tuki ya kusa kwashe wani mai Mashin Gabadayansu suka Furta Subhanallah.

Mastur ne ya kalli Mansur da Sauri yana Fadin"Kagani ko..? Kana chan wajen Surutunka na Fama zaka Jama kanka Damu Gabadaya.."Mansur na Dariya yace"Haba ai Normal ne..Shi ya Shigomin fa Yaya.."Mastur ya kada kai yana Fadin"Bana son jin Wata mgana Keep Quit and Drive Well.."Yafada Cikin Bada Umarni da Sauri Mansur ya Saki Sitiyari da Hannu Daya yana Fadin"Yes Sir...yallabai DCP.." ya fada yana yar Dariya Keyarsa Mastur yaDaka yana Fadin"Am i ur Mate..? Ka rainani ko..? Saboda munyi aure Rana Daya ko..? Zan kama ka ne..!
Yafada yana Rausayar Dakai Juyowa Mansur yayi yana kallon su Rumana Dake baya Cikin Muryan sangarta yace"Antynmu kina gani Mijinki ya Dakeni ko..? Kema Diza kin yi shuru yana Dukan miki Miji ko..?
Rumana Dai Mirmishi kadai tayi yayinda Diza ta dago ta sakarmai Harara Dariya yayi Domin Sanin Halinta Sosai Shi bai Dauka wani abu ba Ita kuwa Haushi ne da Takaichi ya isheta wai Antynmu to Shi da wa..? Badai da ita ba Allah ya kyauta Rumana ta zama Antynta.

Gidan su suka Fara yada Zango sun shigo Falon,Mansur ne kan gaba sai Mastur Dake Binsa a baya Sai Rumana sai Diza Dake Baya Tana Tafiya kamar ba zata tayi ba.

Dukkansu suna zaune afalon na Hajja,Baba Habibu na Zaune akan Cafet din Kuloli ne agabansa yana Cin Tuwon Semo Miyar Dan kubewa sai Hajja Dake zaune gefensa Ayya kuma Tana gefe Itama zaune a kasa Ta Mike kafarta Tana Shafa man Zafi Cikin Farinciki Suke Hiransu Sama sama Sukaji Sallaman su Mansur din.

Hajja ta Mike tana ta yi musu maraba Daman Mansur ya gayamata zasu zo ammh Tunda Taga Dare yayi sai ta Cire ran zuwansu ta Dauka sun Fasa ne

Mansur da Mastur Bayan kowannensu ya Cire Takalman kafarsa suka Nufi Baba Habibu Cikin Fara"a da Farinciki kamar yadda ya Dakata da Cin Abincin nashi ya Dago yana kallonsu Falon akwai Haske Tunda akwai Wutan lantarki.

Gefe da gefensa suka zauna suka sanyasa a Tsakiya kenan Mastur ne ya Fara gaisheshi kafin Mansur dukkansu ya amsa musu Cikin Sakin Fuska,Rumana kuwa Kasa Ta Zauna kanta a kasa Tana gaida Baba Habibu ya amsa mata Cikin Fara"a da Sakin Fuska Ayayinda Diza Dake gefenta itama ta gaishesa ya amsa Cikin Fara"a Kafin Su juya suna gaida Hajja Ayya ce Ke ta Musu Maraba Lale Rumana ta gaishe da Ayya Cikin Kunya da kawaici ta amss Tana yaba Tarbiyan Rumanan..!

Mastur ne ya Leka kulan gaban Baba Habibu Tunda yaga Tuwo sai yaji Ransa ya Biya Cikin Sanyinsa yace"Baba zan ci Tuwo.."Baba Habibu yace"wanko Hannunka kazo muci Babban Mutum.."Da jin Haka Shima Mansur ya Shagwabe Fuska yana Fadin"Nima fa Zan ci Baba.."Baba Habibu Na Dariya yace"Dukkanku ku wanko Hannayen ku kuzo muci..."

Ayya Dake gefe Tayi karaf tace"Dole kace zaka ci..Tunda Kishiyanka yace zai ci..'Tafada Tana Hararansa Mansur ya kalleta ya balla mata Harara yana Fadin"Eh din ina Ruwan ki.."Rumana sai Mirmishi take,Yayin da Hankalin Diza na kan waya Hajja kuma ta Fita Zuwa Kitchen Tsam Mastur ya Tashi ya Bita Chan Kitchen din ya isketa Tana Kokarin Kunna gas Cikin mamaki yace"Hajja me zaki yi..? Tace"Girki zan Dora ma Matan ku..Nasan kila basa cin Tuwo Gwara ma Diza Takan ci bansan Rumana ba..'Mastur yayi Mirmishi yana Fadin"Hajja kenan..Kada ki Damu.."Yafada yana Diban Ruwa a karamin Kofi Cikin wani Roba yawanke Hannunsa Hajja ta kallesa Tana Fadin"Haka Nan zasu zauna Babban Mutum..? Yana Shirun Ficewa ya Dawo kawai batare Da yayi mgana ba ya ja Hannunta suka Fito Falon duk sai su Mansur suka Bisu da kallon Sha"awa yadda ya Fito yana Rike da Hannayenta bai Direta ko"ina ba sai kan kujera yana Fadin"Ki zauna ki Huta Hajja..!
Ayya na gefe tace"Ai bata son ta Huta Megidana wani Lokacin in tayi ma Hajara Fada Halan me tace zatayi..?
Mastur na kokarin zama Gefen Baba Habibu yace"Wani girkin zata Sake yi.."Mansur yace"Girki kuma..? Bayan wannan Hajja..?

Hajja Da bataji Dadi ba Ta Raunana Murya Tana Fadin"Matan nan naku naje sama ma wani abu..Sun kawo mana Ziyara a barsu bako Ruwa.."Ayya Tace"Eh kema kin ce wani abu Hajara Akawo musu koda Ruwa ne in Hadiza yar gida ce ai Rumana kan bakuwa ce.!
Rumana Dake gefe Tayi Saurin girgiza kai Tana Fadin"A"a Ayya ni ba bakuwa bace..Nima yar gidace kamar Diza..Alhamdulillah wlh a koshe nake ban san ko Diza ba.."Diza Dake Latsan wayarta Daman Duk Haushin iyayin Rumana ya gama Isarta ko Dagowa Batayi ba Tace"Nima Am Ok.."Ayya Ta tabe baki Tana Fadin"Koma Amkake ne Ina ruwan wani da Turancinki.."Gabadaya Falon suka saka Dariya Banda Mastur Daya Natsu kawai yana cin Tuwonsa Hankalinsa kwance Hira ce ta Tsinke tsakanin Ayya da Diza Sama sama Rumana kuma na gefe sai dai ta Murmusa,Har su ka gama cin Tuwon Suka wanke Hannuwansu a wata Roba Mansur ya kwashe komai ya maida Kitchen kana ya Dawo nan Baba Habibu ya Tarasu yayi musu Nasihan Zaman Lafiya da yadda Zasu gyara zamantakewarsu Ayya ma Tayi nata Hajja dai Kunya addu"a kawai tayi musu Jikin Rumana yayi Sanyi Ballatana da Ayya tayi ta jan Hankalinsu su zauna Lafiya da juna ita da Diza alokacin ta kuduri Niyar Insha Allahu Zata samu Diza ta Tambayeta kotayi mata wani abu ne..? Domin su sami Fahimtar juna..!

Mikewa Mastur ya Farayi ganin pass 10 ya kalli Mansur bayan ya Duba agogon Fatan Dake daure a Tsitsiyan Hannunsa Ya kalli Mansur yana Fadin"Muje ko..? dare nayi..! Mansur ya mike yana Mika Lokaci Daya yana Fadin"Baba gobe fa Abuja zani Taron mu na partyn mu kila sai nayi kwana Biyu zan Dawo.."Nan Baba Habibu da Hajja Harda Ayya sukayi mai Fatan alheri Ammh Mastur na gefr bai ce komai ba Baba Habibu ne ya kalleshi yana Fadin"Babban Mutum kai yaushe ne zaka koma..?Mastur na Tsaye ya karkace kai yana Fadin"Munyi mgana jiya Baba..Gobe zan koma Insha Allahu..!

Baba Habibu yace"Anyi haka na Shafa"a ne..Allah ya kiyaye Hanya.."Dukkansu suka amsa da Ameen Ayya ce tace"Toh ita Rumanan fa..? Yashe zata koma wajen aikinta Tunda naji Alhaji na Fadin zata dawo nan da aiki.."
Chapter 52 · 0% Book details