← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 94

Sashe 6

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habibu Dayaje ya samo Mota Da Gudu ya Shigo Gidan kamar zai Kifa sai dai yana Sawo kansa Dakin Mala"ikun Daukan rai suka Karisa Zare Ran Maryama Allahu akbar Kullu Nafsin Zaki"katul maut kowani Rai sai ya Dandani zafin mutuwa,Tun daga Bakin Kofar ya Tsaya Cak ganin Inna Hasiya na Hawaye Sule na kuka Baba Jibo na Sharan kwallah Hajara da Ayya na kuka Mastur ma haka sai yaji Kafafunsa sun Daina Daukansa Maryama ya kura ma Ido ganin ta Kwance Jikin Sule idanuwanta sun kafe sama bata Numfashi Tuni yaji wani Dum..! Dam..! Bai san ya akayi ba sai dai yaji Duhu ya mamayesa Lokacin Dayake neman karisawa ga gawar Maryama Yaji Salatin su Inna Hasiya Daganan bai kara sanin Inda kansa yake ba sai bayan Awa Daya da ya Farfado ya gansa kan Jikin Baba a tsakar Gida Ga Gida ya Cika da mata sai Koke koke akeyi sai komai ya Dawo mai Sabo Cikin Mutuwar Jiki da kunar Zuciya ya Mike Zaune yanabin Kowa da kallo kamar yadda suke masa kallon Tsausayi Idanuwansa ya Sauke kan Hajara Dake sanye da Hijabi Tayi kuka Har tabama uku Lada Mastur na Jikinta Shima Duk Hawaye sun Bushemai Gabansa ya kara wani Rugu Rugu bai Samu Zarafin mgana ba wani makocinsu ya shigo Dauke da Likafini da Turare da ganye magarya ya mikama Baba Jibo Batare da yayi mgana ba shi kuma ya Mike ya isa ga Kofar Dakin Maryama ya Kira Ayyah wacce ta Fito Tana goge kwallah ya Mikamata ya juyo Sai matan Dake waje suka Fara Fadin"Allah ya Jikan Maryama..! Allah yasa aljannah ce makota..Tayi Shahada ta Haihu Ko abunda ta Haifa bata gani ba Allah yayi mata Cikawa.."
.mganar haka ta Rika mai Amsa kuwa acikin kunnuwansa Yanzu Shikensn kanwarsa Maryama ta rasu..? Innalillahi wa'inna illaihirraju"un..Allah gareka muke kuma gareka zamu koma..Allah ya jikanki Maryama Allah ya sadaki da mala"ikun Rahma.
Yake yake ta Fada acikin ransa Mikewa yayi ya Fice matan suka Bisa da kallon Tsausayi.

Waje ya Fita yaga Mutane Dayawa a kofar gidan Duk sun yi Jigum Jigum Ga Sule agefe Shi da yayyinsa Yana ta Sharban kuka Suna bashi Hakura Habibu na Fitowa kowa ya Bisa da kallo ganin babu Hawaye ko Daya a idanuwansa Baba Jibo ya Nufa Dake Tsaye Cikin Sanyin Murya da wani Juriya yace"Baba ina gawan Maryama..?

Baba Jibo yace"Tana ciki iyayenka na shiryata.."Kai Habibu ya Kada kafin yace"Allah ya jikanta..Ina Abunda ta Haifa..? Baba jibo ya Dafa shi yana Fadin"Ameen Habibu kayi Hakuri kaji .? Abunda Ta Haifa Ayya tace Namiji ne ya na nan da Ransa.."Shi dai Habibu Gefe kawai ya koma ya Tsugunna yana Kiran sunan Allah acikin Ransa ya ma Nemi Hawaye ko Kuka ya rasa yana nan Tsugunne sai ga mata da yawa daga gidan su Sule Harda goggonsa da Matarsa Zainabu sukayi musu gaisuwa suka Shiga Gidan ba Dadewa Aka leko aka Kira Baba Jibo yana Shiga ba Dadewa yazo ya Kira Habibu da Sule yace suzo suyi ma gawa Sallama An gama gyarata.

Shidai Habibu Baba Jibo ke Jansa Har Zuwa gaban gawan maryama da aka Hadata Cikin Likkafani an sakata Cikin makara Shidai Habibu Durkusawa kawai yayi yana kallon Fuskar maryama da Sule ya saka Hannu ya yaye Zanin da"a Ka rufe ta da shi,Wani irin yake ji acikin Jikinsa kamar bashi da Lafiya yana jin kamar karya ne..? Maryama bata mutu ba Zata tashi Inna Hasiya Kasa Zama Tayi ta Fice Tana Sharan kwallah Sule ne ke ta ma Maryama addu"a yana Sharan kwallah Habibu kuma ko motsi ya kasa yi ganin Haka yasa Baba Jibo ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Kayi Hakuri Habibu..Kayi mata addu"a Yanzu Maryama ba Shirunka Take Bukata Ba addu"an ka take Bukata.."Baba Jibo na mgana ya Runtse Cikin Kunar rai dana Zuciya ya Kura ma Fuskar Maryama Ido yana Fadin"Allah ya yi miki Rahma Maryama..Halinki na gari ya Biki..Allah ya karbi Shahadanki.."Daganan kawai ya Mike ya Fice Daga Dakin yana jin kamar Bashi ba kamar karyane Maryama nada Ranta Wata Duniya ce Ta Dabam yashigo Ko Daukan gawan ma Kasawa yayi Baba jibo da Sauran Mutane suka Shiga suka Fito da gawan yana jin kukan Mata Daga Cikin Gida Baba Jibo Shi ya ke rike da Hannunsa harzuwa cikin makabarta Daman Tuni an haka kabarin.

Habibu yana ganin Abun kamar a mafarki wai yau maryama ta bar gidan Duniya,Yana ji yana gani suka Sakata a kabarinta shi da Baba Jibo da Sule suka kuma maida kasa suka tula Tunda ya Durkusa gaban kabarin yana Mata addu"a yaji Hawaye sun Cikamai ido,ammh sun kasa Zubowa Saboda Juriya yana ta dai yi mata addu"a har Mutane suka watse bai sani ba Daga shi sai Baba Jibo Sule ma yan"uwansa sun jasa yana kuka.
Kafadansa Baba Jibo ya Tabo ya Mikamar Dashi yana Fadin"Tashi Muje Habibu...Maryama tatafi ta barmu..Sai dai muyi mata Fatan Allah ya karbi Bakuncinta.."Bai iya cema Baba Jibo komai ba ya wuce bayan ya kara waiwaya ya kalli Kabarin Wani Katako ya gani nan gefe kila na masu hakan kabari ne,ya Dauko Katakon Da Sauri ya Kafashi gaban Kabarin Maryama yana kara kallon Kabarin yana ji kamar Maryama bata mutu ba Tana Ciki Tana Kiran sunansa ganin haka yasa Baba Jibo ya Riko Hannunsa suka bar makabarta ya san yayi Rashin Ya ammh Habibu ne yayi Rashin Kanwarsa Masu Soyuwa garesa.

Har suka Dawo Gida nan waje suka yada Zango inda aka Shinfida Manyan Tabarmu ana karban gaisuwan Shidai Gashi nan ne yana zaune yayi Zuru Kamar wani gaula in ance ya Hakuri Habibu sai ya Daga kai yace Hakuri namu ne Duka.."Allah ya jikan Maryama Allah ya raya Abunda ta bari..Sai ya samu kansa da Saurin amsawa da Ameen yana jin wani Nauyi Daga saman Kirjinsa Baba Jibo na Lura Dashi bayason Rashin Fitar Hawayen nan Habibu yafi so yayi kuka ya Fitar da Abunda ke Ransa kada wata Cutar Zuciyar ta kamashi..

Acikin Gida kuwa Mata sai Koke koke suke Barin ma Hajara Tayi kuka Kamar Idanuwanta Zasu Daina gani Haka ma Mastur Duk da yana yaro ya Fahimci Tabbas Goggonsa Bata agidan nan yaga su Baba sun Fita da ita Inna Hasiya kuwa bata kuka sai dai Lokaci bayan Lokaci Tana Sharan kwallah Ayya ita ta wanke Jaririn nan tas aka Sakamai kaya kamar ya san maraicin Daya sameshi Tun Zuwansa Duniya bai yi kuka ba yana Hannun Hajara ta kamkameshi Tare da Maatur Tana kuka Dangin Sule suna Daga gefe Goggo Da Zainabu kamar ma Murna suke da Rasuwar Maryama da Bakincikin Abunda ta Haifa kafin Ta rasu suna dai Gefe suna kallon Kowa Daya bayan Daya bama wanda yabi takansu Zafin Mutuwar Maryama mai Radadi ce ga ahalinsu...

Haka akayi ta karban gaisuwan har Ranar uku..Ranar da Jaririn da Maryama ta bari ya kwana yana kuka Daman Daga Ruwa Sai Ruwa ake basa in ya fara kuka ganin haka yasa Habibu Daya zama wani Shuru Shuru ya Dauki Hajara da Jaririn Suka Tafi General Hospital na garin Doguwa aka Dubashi Bayan ya Shigar da bayanin Mahaifiyar shi Ta Rasu Lokscin Data Haifeshi likitan nata Fadan meyasa ba"a bashi madara akayi ta Bashi Ruwa yunwa ce ta kamashi kuma in son samu ne a samu wacce Zata Shayar Dashi Saboda ba lalle ne Madara ta Rikesa har ya Rayu ba Shi Nono Tamkar wani Sinadarin Jariri ne yana karaminsa da haka suka baro asibitin bayan Habibu ya kashe Sauran kudadensa Duka an Duba yaron Komai lafiya an Rubuta musu madaran da zasu Dinga bashi,Daganan gida ya maida su Hajara ya wuce kasuwa yaje ya siyo madaran ya kawo nan da nan Hajara ta Hada da Ruwan Zafi ta fara bashi sai gashi yasha da yawa Daganan sai barci Tsausayinsa da kaunarsa ya kamata Allah Sarki Yazo Duniya Lokacin da zai ji Dumin mahaifiyarsa mai Rabawa Tazo ta Rabasu.

Ranar da akayi bakwai da Rasuwar Maryama ranar Habibu yayi ma jariri Hakika kuma ya sanya mai Suna MANSUR.! Batare daya Jira Sule wanda sai dai yaji abun Daga sama Bai Damu ba Domin yasan Habibun Haushinsa Yake ji Tun bayan Daya gayamai Maryama nada Hawan Jini Tuni Ran Habibu ya baci yana ganin kamar Harda Sakacin Sulen ya Rasa Tilon kanwarsa Maryama.

Aranar kowa ya watse Gida ya Rage Daga Inna Hasiya sai Hajara da Baba Jibo da Habibu da Mastur sai Ayya Dake nan Tana Taimakama Hajara kula da Mansur Daman su goggo Tun Ranar uku suka koma Sule din ne ya zauna Har akayi bakwai Habibu bai samu Sararin kuka ba sai Ranar da aka watse chan kuryan Dakin Hajara ya shiga ya kwanta akan gado ya Fara kuka kuka mai Cike da Tsausayi da wani kewar na Rashin Maryama ba wanda ya Hanashi Domin kukan ne kadai zai saka ya samu Saukin Komai acikin Ransa.
Ya Dauki Mansur yana kallo ba inda ya Baro Maryama sai da ya kwaso Duhun Fuskar Babansa Tunda Maryama Fara ce kamar yadda Habibu yake Fari Tunda kakarsu wacce ta Haifi Inna Hasiya Mutuniyar Maiduguri ne irin Fararan Kanurin din nan ga kyau ga gashi Ita Inna Hasiya ta Dauko suma sai suka Dauko Farinta ta Duk da Shima Baba Jibon Yana Da Haskensa.

Habibu yaji Duk duniya Mansur ne kadai ya Rage mai wanda Zai kallah ya Tuna da Maryama Wacce Kullum yake kuka da Rashinta,Sai ya Dage Damtse Duk Gidan ba wanda yakai Shi kula da Mansur wanda ko Sule bai sami Damar mgana kan Mansur din ba ganin yadda Habibun ya Cika komai kuma Uwa Uba kwarjini garesa In ya Hade ran nan bamai iya ja Dashi.,Madaransa kuwa Duk Sati yake Hanyan Zuwa Siyowa Acikin Ransa kuma yana Wani Tunani Dole ya Nema ma Mansur wacce Zata Shayar Dashi ta zame mai Uwa.
Chapter 6 · 0% Book details