← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 94

Sashe 33

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jirgin karfe 4pm suka Shiga Zuwa Sokoto suka yada Zango a Gidan Abba Dake Sokoto,Sun so su wuce aranar Abba ya Hana sai da suka kara kwana Anan Sokoton,mommy dai Gidansu Taje ta kwana Diza kuma ta bita Hajja da Aiya ne da Mansur da Daddy suka kwana anan Gidansu Rumana,Washegari kuma Sai da suka Fara Biyawa ta Gidansu Mommy aka gaiggaisa kana Suka wuce Filin Jirgi Daganan suka Shiga Jirgin Kaduna,Rumana Da ita akaje Rakiya sai dai ta Fahimci Diza ta Dauke mata ba kamar Haduwarsu a Lagos ba sai bata kawo komai ba ta Danganta Hakan da kila gajiyace,Sun Rabu Cikin aminci Umma da Abba nata Godiya Mansur ya karbi Lambar Rumana yace Dayaji Ciwin kai zai kirata ya Dauketa Personal Doc dinsa sai Dariya ake a kaduna suka sauka Motor Haya kamar yadda sukayi a zuwansu suka Hau Zuwa Zaria Wajen mangariba suna Gida Hankalin Abba da Umma ya kwanta da suka yi waya sukace sun sauka Lafiya kowa Gidansa ya Nufa Domin sauke gajiya sai dai Baba Habibu ya Dawo ya iske sun Dawo Daman bai da Mtsalan komai Megadi gidan Daddy Mama Fadime ke bama abun karinsa na safe da Abinci Dare in ya Dawo Daman Mommy Ta bar mata Sallahu
Sai da Safe Baba Habibu ya Shiga yayi ma su Daddy barka da Dawowa Daman Ya kira Abba awaya ya Tayashi Murna Tun Ranar.

Kafin Barowar Daddy Sokoto sunyi mgana Sosai da Abba kan Rumana ya gayamai yana son Tayi aure,Damuwarsa Daya bata da wani Tsayayye,Daddy ya nusar dashi da kuma Shawaran kada ya matsa mata sai Ta Fito da Miji ya Cigaba mata da addu"'a Allah zai Fito mata da miji nagari kada ya Damu anan ne yake Tambanyanshi Diza fa Daddy yake gayamai ita ai suna Hashashen sun Daidaita da Mansur nan ya gayamai duk yadda ake ciki Abba yace Tabbas ko bai Furta ba akwai Soyayyar a Tsakaninsu,Daddy yace Dukkanmu Haka muke Tunanin Iyayansu Mata ma sun Dade suna Zargin haka sai dai kasan yaran Zamani gwara abari su Furta sai ayi komai Cikin Farinciki,Sun Rabu kan cewa Duk yadda ake ciki zai Kirashi ya gayamai Domin shima ya gayamai Baya son Diza ta Fita wannan Shekaran bai aurar da ita ba.

Sati daya da Dawowarsu Daga Lagos Bikin kanwar Mansur yazo Tafiya ta kama Dole Mommy Bata je ba ammh Da Diza aka Tafi da Hajja da  Balaraba da Aiya wacce Tace sai taje Ranar Daurin Aure kuma Mansur da Daddy da Baba Habibu da Kawu Usman suka taho aka Daura aure Dasu Aranar suka Juyo Daman Mansur yana da Taro Washegari bai kwana ba Dayake ya zo garin kafin Bikin har ya bada Duka Kudin Kayan Dakin Sakinan A Maruka suka kwana Daya Suka koma Ririwai suka kwana Daya,Duk da Diza tasha zuwa Saboda Tana Rako Mansur in zai Taho Diza Taga Busharan da aka so a likama Abun sonta Duk da Taga yanayinta Sai da taji Kishinta itafa bata kaunar Wata Mace ta Rabi abunda take kauna Sam,Sai washegari Daddy ya Turo da Direba ya Taho ya Daukesu suka koma Zaria Mastur kuwa Daman yace bazai samu ba,bai gaya musu bane bashi Da Lafiya Ciwon ya kara kwantar Dashi wannan karon dai bata kaishi asibiti ba sai agida Likita yazo ya Dubashi gwajin Farko ya Tabbatar mai ya kamu da Haawanjini shi bai ma yi mamaki ba Domin yasan ko Ciwon Zuciya akace yana Dashi bazai musa ba akwanakin yana ji kamar bazai iya Wannan Sadaukarwan ba yana ji kamar zai gaza sai dai kuma karfin Halinsa da Juriyansa sun gaza Ya nuna Rauninsa.

Dalilin haka yasa ya Fara Rubuta Labarinsa da Soyayyarsa da Diza Tun Ranar Daya Fara sonta acikin wani karamin Diary dinsa Dayake Rubuta Muhimman abubuwansa,In yana Rubutawa yana jin Sauki acikin Ransa,Shiyasa yake Rubutawa ammh yana mai Boye mai kyau Domin baya Fatan wannan mganar ta Fito har wani Daga Cikin Ahali yasan da ita.

_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*

*Janafty....*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*Page1️⃣6️⃣*

"Shuru Daddy yana ta jiran kiran Mastur kan mganar da sukayi zuwan da yayi  mganar auransu Shi da Mansur ammh shiru bai jisa ba yayi mai uzuri saboda baida Lafiya kwanakin baya ammh ai yanzu ya samu sauki.

Mommy ne ta Shigo Falon Tana Dauke da kofin Coffea har ta isa gabansa bai sani ba,Sai da taja Center Table din gabansa ta Dora Kofin Tangaran din Tana Fadin"Alhaji lafiya kuwa..?
Ajiyar rai ya saki yana Fadin"Bani Coffea din.."Daukowa Tayi ta mikamai ya karba ya fara sha Gefensa ta Zauna Tana kallonsa Dago kansa yayi yana Fadin"Ina khadija..?

Mommy tace"Tana Dakinta.."Kai ya gyada yana Fadin"Mastur Shuru bai nemeni ba..Kuma bai zo ba.."Mommy tace"Topha..wani abu ne ya Faru..? Daddy ya ijiye kofin Gabansa saman Center Table din yana Fadin"Kan mganar auransu ne Asiya..Tun Zuwan da yayi mukayi mgana Dashi kan su Fito da Matan Aure Duk da Mansur yace akwai wacce yake so Tuntuni shifa..? Munyi mgana da Mallam Habibu shi kanshi ya kosa yaga kowannensu ya mallaki iyalinsa na kansa"Mommy tace"Hakane kam..Ai iyali Shine mutum..Toh Shi Mansur waya ce yana so..?

Daddy ya Dauke kai yana Fadin"Bai Fada ba..bansani ba..Yadai ce zai Fadama yayansa.."Mommy Na yar Dariya tace"Ai ni nagaya Tuntuni...Mansur Har gida Za"ayi da Diza.."Daddy ya Kada kai yana Fadin"Tunanin ku kenan..! In kuma ba ita ya Zaba bafa.."Mommy tace"Ai itama zai Zaba..In sun Boye Kaunar Dake Tsakaninsu mu ai basu isa su Boye mana ba.."

Daddy bai kara mgana ba illah Wayarsa Dake gefensa Daya Dauko yana Laluban Layin Mastur Sai da tagama Ringing bai Daga ba sai bai kara kira ba ya ijiye wayar ya Cigaba da Shan Coffea dinsa yana Sauraran Hiran da Mommy kemai kan Hujjansu na Soyayyace mai Tsanani Tsskanin Diza da Mansur bai ce mata komai ba Shima anashi Tunanin Hashashensa kenan Har Baba Habibu sai da ya Fadi haka Allah yasa dai Tunaninsu ya zama Daidai da Tunanin Mansur.

Kamar Minti Goma Tsskani da Kiran Mastur sai gashi ya Biyo Bayan kiran Daddy ya ijiye abunda ke Hannunsa ya Daga Kiran da Sallama Daga chan bangaran Mastur Daya Fito Daga Wanka Ruwa na Diga ajikinsa bai Tsane ba ya Zura Jallabiya mai Ruwan Toka,Sallar Isha"i yake son yayi Data kubcemai sai Shafa'i da wuturi yake da Niyyar yi sai yaga kamar wayarsa na Haske Dayake ya sakata a Silent ne,yana Dubawa sai gaya kiran Daddy,bai Daga ba sai ya Tada Sallar sai da yayi sallar Isha"i yana Zaune kan Darduma yabi bayan Kiran Daddy gabansa na Faduwa.

Bayan sun gaisa da Tambayan Mutanen gida,Daddy ya Tambayeshi jikinsa da kuma aiki yace komai lafiya Daddy ya gyara Zama yana Fadin"Mastur ya najika Shuru ne..? Mastur yaji Faduwar gaba Cikin Sanyin Rai yace"Shurun mene Daddy..? Daddy yace"Kan mganar da mukayi kwanaki mana mganar Auran ku kaida Mansur..Kun kai mun zali kuma zaman hakan bai dace ba.."

Mastur yaji wani irin yam acikin jikinsa cikin wani irin Yanayi da kuma Dauriya Da Sadaukarwa  yace"Daddy ai Mansur ya gayamin Diza yake so.."Daddy ya kalli Mommy yana Mirmishi yace"Alhamdulillah..Dama Hashashenmu kenan Allah yasa albarka..Kai kuma fa..? Kana da wacce kake so ne..?

Mastur Dayaji wani irin Shock acikin Jikinsa kenan kowa yasan suna son juna Shine bai sani ba..! Allah ya gode maka da Yasani Tun kafin ya Furta yana sonta Da bai iya yafe ma kansa ba in har ya Fara Takara da Abunda kaninsa ke so,Cikin Karfin Hali ya Bude baki yace"Babu Daddy..Ni bansaka aure nan kusa ba..Amin hakuri zuwa gaba.."ya karishe Fada yana Jingina kansa da Bango Jinsa kamar zai Fadi yana Daga Zaune,zuciyarsa Tana wani Zafi kamar Zata kama da wuta.

Daddy yace"ba mganar ayi maka hakuri Mastur..Mansur fa kaninkane..Kai ya kamata ka farayi kafin shi..Tunda abun ya zama haka ya zama Dole kaima ka Fito da matar aure a Hadaku Dukkanku mu aurar daku Rana Daya.."Mastur yama kasa mgana sai maida Numfashi kawai yake Har sai da Daddy yace"Mastur Lafiyanka kuwa..?

Cikin Dafe kansa yace"Bakomai..Daddy adai kara min Hakuri ban da Wacce nake so..Ban kuma san a ina zan samu ba.."Daddy yayi Dariya yana Fadin"Baka dai Nema ba...In da ka nema zaka samu mana..Yanzu dai ka Kokarta ka Shigo wannan Satin sai muyi mgana Gabadaya.."Mastur Daman yana Cikin wani Hali Da Sauri yace"A"a Daddy basai nazo ba.."Daddy ya katseshi da Fadin"Sai fa kazo...mganar kuma wacce kake so kafin kazo ka Duba ina son inji Labari mai Dadi in kuma babu Ni ina da wacce Zan Baka ka aura wacce nan gaba Zaka Dawo ka Godemin.."

Mastur yaji kamar ya kurma Ihu saboda mganar Daddy ammh kuma bazai iya mai gaddama ba,Kansa kawai ya Sunkuyar kamar yana gabansa yana jin yadda yake saramai Shi dai Toh kawai yace bai ma san Sadda Daddy ya Datse kiran ba Kamar ya kwanta anan kasa yayi ta kuka da Birgima haka yake ji Saboda ya samu Saukin Nauyin Dake Cikin Zuciyarsa ammh kuma yakasa kukan Zucci da Yawan Tunanin Dayake yi suna karamai Rashin Lafiya da Rashin Natsuwar Zuciya wanda baya Fatan haka ya Shafi Lafiyansa da karfin Gwiwansa.
Chapter 33 · 0% Book details