Sashe 40
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ko Sati ba"a Rufe ba Alhaji Muhammad ya kira Daddy suka Tattauna kan yadda abubuwan Zasu Tafi Daidai ya riga yayi mgana da Yan"uwansa Dake wamako,Saboda kara yasa yace su zasu Tattaro su zo nan Zaria sai ayi mganar komai gabadaya Daddy yaji Dadi Sosai nan suka Tsaida Lokaci Ranar Lahadi mai Zuwa Alhaji muhammad din zai zo shida kaninsa domin ayi komai agamashi.
Daddy na jin haka ya samu Baba Habibu suka Tattauna Baba Habibu ya kasa bakin Godiya bayan an basu Rumana kuma ma ace bazasu je ba su Dagachan zasu zo Lalle kara da karamcin Mutanen nan ya wuce Duka Yadda Suke kwatance haka ya shiga Gida yana gayama su Hajja Ranar Duka Hiran kan Kirki da Dattakon Daddy da Abba Dukkansu suna Halin kwarai suka wuni yi.
Diza Da taji labari abakin Mansur Ranar kwana Tayi kuka Gani taki kamar zata Raunana Bazata iya cika wannan alkawarin ba gefe daya kuma Tsanar Rumana ya samu wajen Zama acikin Ranta,Gefe Daya kuma Ta Fara Jin Haushin Mansur Duk wani rawan kafa Dayake mata kallonsa kawai take yi ta Daina Sakar mai Fuska Haka kurum Take kallonsa amtsayin Wanda yayi mata katanga da abum sonta ammh Shi baya Damuwa bai ma Wani Fahimci Wani Hali Take Ciki ba yana nane da ita indai yana Gida bai je wani waje ba yanzu Har wajen aikinta yake Binta Tayi ta Shan kamshi yana Biye mata Saboda Tsananin Son Daya ke mata.
Bangaran Rumana kuwa bazata Dora komai ba Domin Ko Sau Daya Mastur bai kirata ba itama Bata kirashi ba ta Dai Turamai Sakon Murna da Godiya Daya karbeta amtsayin mata Domin Daddy bai nuna Hadin Nashi bane ya Nuna Mastur din yana Ra"ayin Rumana sai Tayi Tunanin Tabbas Tunaninta ya Zama Gaskiya kan Mastur yana Sonta auran ne bai so yinsa yanzu ba sai kuma Allah ya kawo Lokaci Bata Damu Da Rashin Kulawarsa ba ita dai abu Daya ta sani She Love him So bata Bukatar komai Daga gareshi ya gama mata komai Tunda Zai aureta.
Shi kuwa Mastur Tsausayama kansa yake yana Tsausayama Rumana Zata Shiga Sahun masu Sadaukarwan so Domin zata auri Zuciyar da batada Gurbin Wata Soyayyah sai Gurbin Kunci Damuwa da Fidda Rai Yaga Sakonta bai da tace mata kawai yasa ya kyaleta Zuwa Lokacin Dayaji Zencen zuwan su Abba sai yagama Sarewa gabadaya kan al"amarin ya Zauna yana ma kansa Fada da Cewa Rumana itace Gaskiyansa ayanzu..Diza kuma karyace Tayi mai Nisa Har Abada Tunda Zata Zama mallakin Mansur,ya Zama Dole ya Cireta aransa ya yakiceta Har Abada sai dai bashi ya Dora ma kansa ba kwana yake kuka yana Sallah yana addu"an Allah ya Ciremai Soyayyar Diza acikin Ransa ammh kuma abun kamar kara gaba yake ba wani Sauki yana neman yafi karfinsa Duk da Haka yana Faman yaki da Zuciyarsa,bayan ya Dawo sai da ya koma asibiti aka kara gwadashi aka Tabbatar da jininsa ya kara sama Likita sai Fada yake mai kan ya Rage yawan Damuwa Da Tunani Toh shi kam baisan Ta Ina Zai Raba kansa Da Tunani da Damuwa ba abunda suka Daura aure Dashi ai kuma sai abunda Allah yayi.
*****
Kamar yadda Abba ya Fada Ranar Lahadi Jirgin Safe suka Biyo Zuwa Kaduna Daddy yaje ya Taho Dasu Shida Mansur nan Falon kasa agidan Daddy aka Sauke su,Mommy ita ta Taimaka ma Mama Fadime akayi Abincin Tarban baki Diza Bata gida Tana wajen aiki Hajja ma tayi Tuwon Shimkafa Miyar agushi ta aiko Dashi RANAR Baba Habibu bai Fita aiki ba Sai yayi ma Kawu Usman kara ya Kirashi Domin ayi komai agabansa.
Alhaji Muhammad Shi da kaninsa Alhaji Hamza suka zo..Sai Baba Habibu sai kawu Usman,sai da suka ci suka sha kana suka Fara Tattauna abunda ya Tarasu Abba Dayaji Daddy yace shizai Biya Sadaki da kuma Muhallin da zasu zauna Shima sai ya Hade rai yace Duk Daddy ya kame komai saboda haka yaji shi ya Dauki Nauyin Kayan Daki Both da Diza da na Rumana,sai kuma Motocin Hawa Sabbin Yayi Guda Biyu Kowane nashi Dana Matarsa ai sai Baba Habibu ya kasa Mgana Kawu Usman ne keta Godiya Cikin Mutumci Daddy shi ya bada Sadaki Kowanne 200k mutum Daya sai kuma Baba Habibu ya Fito da da Goro da Dabino sai kwalayen Minti da Cimgam sai Katan katan din Lemuka na saka Rana sun Tsaida Ranar nan da Wata uku masu zuwa sai Daddy yayi mgana kan Aikin Rumana Abba yace bakomai zai san yadda Zai yi ta Dawo nan Cikin asibitin ABU ta karisa,sai ta Dora da Bautar kasarta Kafin atashi Taron sai da Baba Habibu ya Roka kan Kada su kara Daukan Nauyin wata Dawaniya Su bar Mansur da Mastur su hada kayan Lefe da kansu kada Dawainiyar Tayi yawa Suga kamar an basu matan akyauta ne Domin yaji Abba na Zencen kayan Lefe,Basu ja da alfarman Baba Habibu ba suka Karbeta Hannun Bibbiyu su Abba basu Juya ba sai bayan Sallar Azahar kana Mansur ya Tafi kaisu kaduna Ina Zasu Hau Jirgi su koma Sokoto.
Duka kayan Uku aka Raba Abba ya Juya da Daya Daddy suka Dauki Daya Baba Habibu Daya achan gidan ne Hajja ta Raba uku suka Dauki Kashi Daya Kawu Usman Daya,Daya kuma na Mutanan maruka ne Dangin Mansur Sadaki kuma Daddy ya Rike na Diza Shi kuma Abba Ya Bama Alhaji Hamza ya Rike a Hannunsa Lokacin da Baba Habibu ke maimaita musu Shima abun Alheri Abba sai da Hajja Ta Saki Guda da Mansur ya Dawo yaji Bakinsa yaki Rufuwa Diza na wajen aiki ya Bita Chan yana gyamata an saka musu Ranar aure nan da 3 month..Ta kasa Boye Halin Datake Ciki agabansa kawai sai ta sakamai kuka sai kuma ajikinsa yayi sanyi ya kalleta yana Fadin"Har yanzu baki sona ko..?
Yadda yayi mganarsa Taji Jikinta yayi sanyi,Da Sauri ta Girgizamai kai Mirmishi kawai yayi yana Fadin"Ko baki Fada ba nasan baki sona..Kina pretending ne saboda iyayenmu da kuma Darajan ya Mastur..Koma yaya ne Diza ki samamin Waje kadan acikin Zuciyarki Domin Ina Sonki..Son da bazan iya Rayuwa baki ba..!
Yana gama Fada mata haka ya Fita Daga office din ya barta Daman aciki ya ssmeta su Hauwa suna Daga Falon suna aiki Yana Fita ta kifa kanta Tsakanin Kafafunta Tana Rafzan kuka haka kurun Take jin wani Rauni Daga kasan Ranta kamar Bazata iya Daukan abubuwan kamar yadda Wasu ke son su Faru ba Ranar dai bata iya Tsayawa Ta kai Tsawon Lokaci ba ta jawo motar ta Zuwa Gida Mommy da ta Fahimci bata cikn Mood mai Dadi bata Bi ta kanta ba Tana Cikin Farinciki ko Su Kayan saka Ranar ta Diban ma Danginta na Sokoto akwai kaninta da zai zo zai Tafi ma iyayanta Dashi suma su Shaida duk ta Fada musu ta waya.
Ta bangaran Umma ma haka yake bakinta yaki Rufuwa da Abba suka Dawo da kayan saka Rana da Sadaki Da Rnar aure nan da wata uku sai saka albarka take da addu"an Zaman Lafiya Rumana kuwa Tamkar Mafarki Haka take ganin abun takasa gasgasta nan da wata uku Zata Zama matar Mastur abun kamar almaara Alhaji Hamza sai Washegari ya wuce Wamako Shida Abba suka Tafi ya Tafin musu da kayan Saka Ranar Duk da sun sani ammh hakan ya zama Shaida garesu.
Mastur Baba Habibu ya kirashi ya gayamai Abun alherin da Abba yayi musu Shida Mansur sai kawai ya saki komai Domin bai da ta cewa Dagashi Har Mansur auran gata Su Daddy zasu yi musu,Wannan Dalilin yasa ya kauda kunya ya Kira Abba yamai Godiya Abba yaji Dadi sai saka albarka yake suka Dade suna mgana kan Aikinsa kafin suyi Sallama Mastur na son Abba da Darajashi,Mutum ne mai ilimi da Saukin kai Ba Ruwansa Tun Lokacin yana Jami"a in Abba ya Dawo Gida da Daddare haka zai kirsa Falo suyi ta Hira Duk da Rashin son Saki Jiki na Mastur sai da ya saki Jiki da Abba Domin mutun ne da ba Ruwansa ya iya mu"amala da mutane ba a iya D"a ya Daukesa ba yana Daukansa kamar wani kaninsa ko Abokinsa,bayan sun gama waya da Abba ya Kira Umma suka gaisa sai mai Tsiya take yana Mirmishi Ba isa yace zai ki Rumana ba Domin gaba Da baya ta Fito Daga Tsatson Tarbiya Umma da Abba Har Abada bazai manta karamcinsu ba Har ya gama Degree dinsa a Sokoto bai Taba Neman wani abu ya rasa ba Umma ta Daukeshi kamar kaninta ta kula DashiTamkar yana gaban Hajja Shiyasa yake jin wani Tsausayi Daga kasan Ransu Watarana ya Zasu ji bayan Auran in yarsu ta Gayamusu baya sonta..! ? Ya Tabbata Hakan bazaimusu Dadi ba ammh kuma Bashi da Mafita Bashi ya Sa Zuciyarsa ta zama ba Tashi ba wannan kuma kudirin Allah ne.