← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 94

Sashe 76

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mastur Dayasan Haka zata Faru Dashi da bai Je wannan Taron ba Domin ya Shiga Dakin Tattaunawar bai ma kai ga Zama ba Jiri da Duhu suka Mamayeshi ya Zube kasa bai san inda kansa yake ba Cikin Gaggawa suka Daukeshi Zuwa Wani Babban asibitin kudi na garin Porthercourt abunka da masu Mikami Cikin Lokaci aka karbeshu aka Shiga Dashi Domin bashi Taimakon Gaggawa.
Dakyar Likitoci suka iya Samo Numfsshin Mastur shi din ma sai da suka sanya mai Oxygen Abun Taimakom Jawo Numfashi kana suka samu kansa,Dakin Hutu aka kaisa Daki na Mussmman,Domin ya Huta Duk da har zuwa Lokacin Bai Farfado ba.
Likita ne yace yana Bukatar ganin wani Ahalin Yallabai din Saboda mganace mai Muhimmanci zai Sanar dasu game da Ciwon Ogan nasu Tunda su Sargent Inuwa ne suka Daukosa Zuwa asibitin.
Jin haka yasa Sargent Inuwa yayi amfani da Daya wayar Mastur Dake Hannunsa tun Bayan Faruwan lamari ya kira Layin Daddy ya sanar Dashi Halin da ake Ciki alokacin Daddy baya Gari yana Abuja Harkan Kasuwanci takaisa Hankali Tashe ya kamo Hanya Bai ma gama Abunda ya kaisa ba Tun a Hanya ya Kira Baba Habibu ya sanar mai da Halin da ake Ciki Zukata sun Raunana jin wannan Labarin Musamman ma Da Daddy ya Dawo da Baba Habibu mganar takai kunnin mata,sai Suka fi Rudewa da Tashin Hankali Musamman Rumana Da tayi ta kuka Ganin Haka yasa Daddy ya yanke Shawaran Washegari Zasu Bi Jirgi zuwa Porthercourt din Shi da Baba Habibu Rumana na jinhaka tace zata je Daddy bai hanata ba Ko bakomai Mijinta ne Tabbasa yana Bukatarta.
Washegari kuwa haka akayi kaduna Direban Daddy ya kai su suka Hau Jirgi zuwa Porthercourt,karfe wajen 3pm na Rana suka sauka agarin Daganan Tashar Mota sukayi har zuwa asibitin Tunda Daddy ya kira Sargent Inuwa ya Turomai adireshin Asibitin.
Asibitin Babba ne wanda ake ji Dashi agarin suna zuwa Suna Fadin sunan Mastur aka fara musu masauki Office din Babban Likitan Daya ke Duba Mastur din Suna Zuwa Daddy yamai Bayanin sune iyayan Mastur yanzu suka Sauka agarin.
Likitan ya kalli Rumana yana Tambayan itafa..? Daddy yace Matar Mastur ne,kai ya kada kafin ya Dauko File din Mastur din yadan Duba kadan kana ya Dago ya Fara yi ma su Daddy Abunda ke Damun Mastur.
Sun Razana sun kuma Tsorata da Jin Mastur ya kamu da Ciwon Zuciya wanda Har ta Fara kumbura kadan Saboda yawan Tunani da kuma Damuwar Daya ke Ciki Kana yana da Hawan jini wanda shi ya Haddasamai ganin Jiri da Faduwar da yayi Allah ne ma ya Taimakeshi Bai yi Shanyewar Barin Jiki ba anyi Saurin kawosa asibiti sun bashi Taimakon gaggwa ya gaya musu Har yanzu bai Farfado ba,Domin Abun Zukan Numfsshi ke Taimakamai Domin sanda aka kawosa Numfashi yayi Nisa sai da Dakyar suka Samosa.
Tashin Hankali wanda ba"a saka musu Rana Duk Dauriyan Baba Habibu sai da yayi ma Mastur kwallah da suka Shiga inda yake yana kwance Sambal kan gado Hancinsa da Oxygen Ta nan yake Fitar da Nunfashi Duk ya Rame ya Lalace kamar ba Mastur ba, Dukkansu sun Danganta Ciwom Mastur da Rashin Dan"uwansa Mansur basu San Daman Mutuwar ta Iske Raunin Rashin Diza ba Daman rashinta ta gina Katon Ramin Sai Raunin Rashin Mansur yazo ya kara yi ma Ramin Zurfi.
Rumana ma Sai kuka ganin Halin da Mastur yake,har sargent Inuwa yazo ya Daukesu zuwa Gidan Mastur na cikin Headquatersu bai Farka ba Domin asibitin ba"a kwana suna da Masu kula da Majinyata.
Rumana yau ce Rana ta Farko Datazo wajen aikin Mijinta Daddy da Habibu sun Taba Zuwa Sau Daya Marigayi Mansur ne yasha Zuwa sosai har kwanaki ma yanayi wajen yayan nashi.
Rumana ainihin Bedroom Din Mastur ta sauka Ciki su Daddy kuma suka Sauka na kusa Dashi Sai Bayan sun Rama Salolinsu ne Sargent Inuwa ya kawo musu Takeway din Abinci basu wani ci da yawa ba,sai dai sun kira Chan Zaria suka kwantar musu da Hankali Sanin suna chan Cikin Damuwa Rumana kuwa Abun mamaki Har Diza sai da ta kira ta Tana Tambayanta ya Jikin Mastur..? Tace da sauki yana asibiti sai gobe zasu koma,Umma ma ta kirata da Abba Ashe Daddy ya kira Abba ya gayamai Sun ce in Jikin yayi Tsanani zasu Taho Rumana tace suyi Zamansu da Sauki.
Haka suka kwana Cikin Zullumi Tun Safe suka Shirya Sargent Inuwa ya maidasu asibitin Alhamdulillah sun iske Mastur ya Farka Har an Ciremai kakakin Numfashi kamar Daga Sama yaga su Daddy Domin Cikin Dare ya Farka Ba wanda yayi mai wani Bayani.
Abakin Daddy yaji Labarin Kiran da Sargent Inuwa yayi mai na Likita nason ganin wani nashi Tunda yaji haka yasha Jinin Jikinsa sai dai ya barsa Rumana kuwa sai kafa kafa Take dashi Yana Binta da kallo ko bai Fada ba yaji Dadin zuwanta ko bakomai Zata Debemai kewa na wani Lokaci.

Ranar nan suka wuni Cikin asibitin sai dare suka koma Gidan Mastur,Washegari ganin Jikin nashi da Sauki Daddy yace Zasu koma Shida Baba Habibu Mastur da kansa ya Roka kan su bar masa Rumana ta kwana Biyu Daddy yace Daman ba da ita Zasu Wuce ba kafin su Tafi sai da suka Tasaahi da Nasihu da Shawarwari Sai alokacin yake jin Sabon Ciwon Daya kamu Dashi na Ciwon Zuciya ya Illahi,sun Hankalarta dashi Mutuwa Dole ce Saboda haka yayi Hakuri yayi musu alkawarin Insha Allahu zai kula da kansa Kafin su wuce sai da suka kira chan Zaria duka Matan sukayi mgana Dashi suka mai Sannu da Jiki sai Lokacin Hankula suka kwanta Abba ma da Umma suna kira ko yauahe Domin jin Jikinsa Haka Mutanen Maruka ma sun kira jinsa Shuru Rumana ta amsa wayar ta Fada musu Halin da ake Ciki,Dayake Sargent Inuwa ya bata Duka Wayoyinsa,Suma Hankalinsu Duk ya Tashi Barin ma Baba Sule,Sai da sukayi mgana da Mastur din ya Tabbatar musu Dayaji Sauki kana Suka Kwantar da Hankali Aranar su Daddy suka Juya suka bar Rumana wajen Mastur Zatayi Sati Daya in ya karajin Sauki An Sallameshi Sai ta Dawo.
Duk da ba"a barin majinyaci ya kwana sai Rumana takai Dare Sargent Inuwa ke maidata Gida ita da kanta Tayi ma Mastur mgana Tana so tarika yimai Girki da kanta ba sai an siya ba,ta Duba Kitchen din ba Cefene jin haka yasa yayi ma Sargent Inuwa mgana Shi yayi mata Cefanan komai da komai,Arana ta Hudu Tayi ma Mastur Ferfesun Kayan Ciki da Dankalin Turawa Sai Lomon kankana wanda kuma yaji Dadin Lemon Har yana Ce mata Gobe ma irinsa Zatayi masa Ferfesun kuma yaci Sosai Kadan ya Rage,Rumana tayi Wahala da Mastur ita ke Taimakamai yayi wanka Ya gyara Jikinsa Abincinsa Shansa da Taimaka mai yayi alwala ya gabatar da Sallolinsa, da komai ita ke kula Dashi Sai alokacin Ma"aikatan Da suke aiki Tare dashi suka Taba ganin Matarsa nan take Wuni asibitin Tare dashi sai Dare Kana Sargent Inuwa ke maidata gida Mastur yana ta Tambayanta ko Zata iya kwana agida ita kadai..? Tace Zatayi ai akwai Mutane a Kusa da ita apartment din dayake kusa da Na Mastur akwai Mutane.
Gani yake kamar bazata iya ba,Shiyaaa Data koma Gida Zai kirata suyi waya Tayi ta Jansa da Hira Dayake Rumana Allah yayi mata baiwar Iya sarrafa kalamai,Shiyasa Suyi ta mgana da Mastur bai gaji ba sai tace yaje ya kwanta kana zasu Rabu.
Da safe kuma kafin ta Fito ssi tayi mai Abinci,mai rai da lafiya da Lemukan da zasu rika Taimakamai wajen Dawomai da Jikinsa da Kuzarinsa kuma yana jin Dadin haka Zaman Rumana Tare Dashi Tamkar wani garkuwa ne gareshi koda yaushe suna waya da Chan Zaria suna jin Lafiyarsu hankula sun kwanta Jin Mastur din yaji Sauki sai Abunda ba"a rasa ba.
Satin Mastur Daya asibiti kana Likita ya yarda ya Sallameshi Inda ta Mastur ne Ranar Dayake da Kwana Biyar yaso a Sallameshi Likitan yaki,Kafin su Tafi ssi da ya gayama Rumana ta kula da Mastur adaina Barinsa Cikin Damuwa ko Tunani Duk wani Abunda Zai batamai rai agujesa A kuma rika yin Duk Abunda zai sakashi Farinciki ya Daina Zama shi kadai Balkatana yayi Tunani ya Zama koda yaushe wani na kusa Dashi Domin gujema Damuwa,Daga karshe ya Rubuta mgunguna Wanda asibitin ta basu kafin su Tafi Duka Bill din Asibitin Headquater dinsu keda Alhakin Biyan komai ko nace Nigerian police din Gabadaya.
Sargent Inuwa ya kwashe su Zuwa Gida,shi da Rumana Wanda Taso tatafi aranar ammh ganin ba"a sallamesa ba sai Ranar yasa ta Fasa zata kwana Kwana Uku Saboda Asibiti Daman Aisha Bala ke mata Ranar Data ke da Duty,kuma yanzu Ranakun aikinsu sun Daina Fadowa Rana Daya kamar baya.
Rumana tabi Shawaran Likita Sosai kuma Tana Kokari kan Mastur Ranar Tare suka kwana Rumgume da juna Washegari Rumana Tatashi da gyaran Duka Dakunan Har tana ma Mastur Tsiya gidansa dai baya ganin Shara yana Zaune afalo Sanye da Jallabiya baka Saman Cafet ya gama Shan tea kenan da Dankali Rumana ta Bashi mgangunansa sai ta Mike ta Fara Sharan Sharan Tace Zata fara da Dakinsa in ta gama Sai ya koma Chan tazo ta gyara Falo da Sauran Dakunan zuwa Kicthen.
Mirmishi kadai yake yi acikin Ransa kuwa yana Fadin Tabbas Mganar Hausawa ne gida sai Mace in bata Ciki kuma ba Gida bane Kango ne Zuwan Rumana Gidan ya Sauya kamshi na Tashi na Dakuna dana Girki,abaya kuwa Shi bai ma san wani Turara Daki ba sai dai na kaya dana Jiki Girki kuwa baiyi Sai dai ya Siya in yayi wuta ne ya Dafa Ruwan Tea ammh Zuwanta Har Kitchen din yasan da Mace tazogidan.
Chapter 76 · 0% Book details