Sashe 25
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin Sanyi jiki da wani Raunin Zuciya ya Cigaba da Takawa Zuwa Shashen nasu,Gabadaya Zuciyarsa ta Shiga wani Sake sake na Daban kodai kodai Soyayyah suke yi ne..? Tunanin haka sai da Yaji Gabansa ya yanke ya Fadi Da Sauri ya karyata mganar bayan ya Girgiza kansa Acikin Zuciyarsa yana Fadin Da ace suna Soyayyah Tabbas da Mansur ya Fadamai baya Taba Boye masa komai,Tabbas da akwai Wani abu a Tsakaninsu Dashi ne zai Fara jin Labari Yin wannan Tunanin yasa yaji Hankalinsa ya kwanta har ma ya Karisa Shiga Shashen nasu Dayake Shuru Kamar ba Kowa.
Kamar zai wuce Bedroom Dinsa sai kuma ya Fasa ya Karkata Zuwa Dakin Mansur din ya Tura sai yaji a bude sai ya Tura ya Shiga gogan na kwance Baje Baje akan gado yana Barci Dagashi Sai Gajeren wando Dakin kaca kacs Daga gani ya Dade bai ga gyara ba Chan kaya Chan waya chan System Chan Takardu Takarce dai Gasunan.
Kai ya Dafe Cikin mamakin yaushe Kanin nashi Zai Sauya ne..?wata zuciyar tace mai kila sai Ranar da yayi aure ya zama magidanci.."Tuna Haka da yayi yasa ya Murmusa kamar zai Juya ya Fita sai kuma ya Fasa ya Fara Taku Zuwa Gaban makeken Gadon da Mansur Yake kai yana Sharar Barcinsa,Ya Dade Tsaye yana kallonsa kafin ya Duka yayi amfani da Hannunsa Guda Daya ya Murdemai kunninsa da karfi wanda yana Cikin Barci yaji kamar an Rike masa Kunnuwa sai yayi Tunanin mafarki ne,Sai ya kara Juyawa zai kara Bajewa Mastur ya kara Damke Kunnuwansa da karfi Wanda ba Shiri yasa Mansur ya Bude Idanuwansa da suka kankance Saboda Barci ganin wanda ke gabansa yasa ya Zabura ya Mike Zaune yana Mitsike ido Cikin Muryan Barci yace"Yaya Mastur na u..?
Bai ce mai komai ba Illah gyara Tsayuwa kawai da yayi yana dan Hararansa ganin haka yasa ya Sauko da Sauri Daga kan gadon ya Daka Tsalle ya Rumgume Yayan nashi yana ihun Murna da Faman Tambayansa yaushe ya Dawo bai sani ba Yana jinsa yayi masa Shuru bai tankamai ba bai Damu ba ya Dago yana Fadin"Yaya me nayi kake Fushi Dani..?
Yafada a Shagwabe kamar zai yi kuka Sai Lokacin Mastur ya kallesa yace"AU baka ma sani ba ko..?
Shuru Mansur yayi kafin yace"Allah Yaya duk iya Tunanina na kasa Tunawa..'Kunnensa Daya ya Murde yana Fadin"Ka manta da wayar da mukayi Dakai ta karshe..? Me nace maka..?ka Rainani ko Mansur yanzu ka Daina Jin mganata baka saka Komai agaba ba sai wannan Shanshancin Siyasan ko Daya maida kai wani kazami ko kanka Baka iya gyarawa,ji kanka Ka Tara suma ba aski ba gyara Kalli Dakinka kamar na Mahaukata bazaka iya gyarawa ba..? Whta Wrong With u ka Fara Hauka ne..?
Yafada Cikin Husky Vioce dinsa ammh Cikin Fada Saboda Bacin Ran abunda Mansur din ya aikata Mansur Zafi ya Isheshi Domin da Zafi ya Rikemai kunnin kuma yaki Saki,kara ya Saki yayi kasa da kansa yana Fadin"Wayyo yaya..Wlh kunnina Zafi ka Sakeni Plz...'Kara Matse kunnin yayi Da Karfi Har sai Da Mansur yaji kamar yayi kwallah Mastur yace"Yanzu ka Tuna Laifinka ko baka Tuna ba..?
Da Sauri yace"Na Tuna..Na Tuna..Wlh na Tuna yi hakuri Yaya bazan kara ba.."Sai Lokacin ya Sakeshi Lokaci Daya ya juya yana Barin Dakin yace"Ok..Kafin mu Fara Ainihin Fadan namu kafim ka Fito u Bettrr Clean dis Room ka gyara komai In bahaka ba Ranka sai yafi haka baci.."Da Sauri Mansur yace"Yes Sir...!Fita yayi yana Kyafci bai yi mgana ba yana Fita Mansur ya koma yana Rike kunnunsa Lokaci Daya yana Fadin"Wlh Ya Mastur yasan Lagon mugunta..Allah ma ya Taimakeni ya Daina kolo akai..Ai da naci Ubana yau.."Yafada yana yar Dariya Lokaci Daya Yana Tuna mganarsu ta karshen kan Gidansu ne Da auran kanwarsa Sakina Dayace yaje Chan Maruka ya gaida Baba Sule ya kuma Yi musu abunda ya kamata ammh Sam ya Manta Kansa ya Dafe kawai bai da ta Cewa Karamin Tsaki yaja jin ana ta Kiran Wayoyinsa Kamar Zai yi kuka ya Mike ya Fara Tattara Kayan daya watsar a kasa ko Ta kan wayoyin Dake Zube kan gado suna neman agaji bai bi ya Fara gyaran Dakin Sanin Da yayi in yayi wasaa Mastur ya Dawo bai gyara Dakin ba Yasan Sauran..
Diza kuwa Batasan Mastur ya Dawo ba 11am nayi ta HauraSama Tayi ma Mommy Sallama ta Hau Motarta ta Fice taso ta Shiga su gaisa da Hajja da Aiya Mansur kuma tasan bai Tashi ba yana Barcin gajiya Sai kawai ta wuce Tunda ana Jiranta Hauwa sai waya take mata tace in ta Dawo sai ta Shiga Ta isa wajen keman ba Dadewa ta Fara aikinta Sagir Abokin Mansur ya Kirata Tare sukayi Makaranta anan ABU,Shi bai samu aiki bane har yanzu sai Yake bin Mansur din yana Taimakamai Kamar dai P.A dinsa Shine ya Kirata yana Fadin yayi ta Kiran Wayar Mansur bai Daga ba Tace bata Gida Ammh bari ta Kirashi Taji itama Dai Kamar Sagir din ne Domin bai Daga kiranta ba sai ta Kira Sagir din Tace Kada ya Damu kila bai Tashi bane ya Bari zuwa anjuma ya Sameshi agida yace mata Shikenan ya gode da Haka suka yanke kiran..
Mastur kuwa yana Shiga Bedroom Dinsa yagansa Tsaf Dashi,Duk da ba haka ya barsa ba Daga gani an kara gyarashi kuma ba kowa bane ya gyara sai Hajja Mirmishi kawai ya Saki yana Jin Kaunar Mahaifiyar Tashi acikin Ransa Kayan Hannunsa ya Zube kan Katuwar Katifar Dake Shimfide adakin Wacce Taji Shinfidun alfarman Mastur Bai Cika son Gado ba Shiysa sai makeken Wardropr dinsa Dake Shake da kayansa Bai Tsaya wani Bata Lokaci ba yaTura Kofar Tiolet Din Dake Dakin ya Shiga wanka Yayi ya Fito Daure da Babban Towel Gaban Madubin Dake Dakin ya isa yaShafa mai kansa SayeSaye da gashi kadan Kadan Domin Mastur ya Tsani Tara Gashi Duk Sati yake Zuwa aski,In yaga Mansur ya Tara Gashi Ya Dinga mai Fada kenan Tun ba yau ba ammh bayajin mgana sam Har yau ya girma ammh bai San ya Girma ya Daina aikin Yarinta ba Shi yana mamakin yadds Har ya Fito Siyasa Partyn Dayake Ciki Ta karbeshi Sai dai kuma Bai da ja Mansur Mutun ne mai Dadin Zama Barkwanci da Son Mutane ya Tabbata Duk inda ya zauna Ko na awa Biyu ne sai sun ji suna kaunarasa Sau Tari In gayansa ya Shige Cikin su Hajja yana ta Hira sai ya Rika Bashi Sha"awa Domin shi bazai iya ba Mgana da Hayaniya kamar Lalura suka zamemai.
Jallibiya ya Zura Kawai ya Samu waje ya kwanta Domin ya gaji Tafiye ce fa ba Kadan ba Daga Porthercourt Zuwa Zaria Bai saba ba Domin Sau Daya suka Taba Tafiyan Mota kuma alokacin bashi ya Tuko Motar ba Sargent Inuwa ne,Ko takan Wayoyinsa bai bi ba daman suna Kashe ne ya Kwanta Yana Lumshe ido Saboda gajiya bai Dade ba barci ya kwashe Sai dai Mansur ya Shigo ya gansa yana Barci sai ya Fita ya Rufomai Kofa Ya Fice Daga Shashen Bayan yayi wanka ya Saka kananun kaya Na kamfanin Armani Shashen iyayen nasu ya Shiga suka gaisa da Hajja da Aiya suka Fara Diraman nasu ta Fama Hajja Tace Ina Mastur yace mata yana Ciki yana Barci ya Dade anan Shashen su Hajja kafin ya koma Barayinsu ya Dauko Wayoyinsa Kira ya Samu ba adadi Kiran Diza Shi yafi Muhimmanci ita ya Kira Take gayamai Kiranta da Sagir yayi.
Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Kyalesa..Nifa yau ba Inda Zani..ina Fita Zan kara Laifi Wajen Ya Mastur..!Da Sauri Diza tace"Bangane ba..? Kunyi waya ne..? Da sauri yace"Ai Diran makiya yayimin Firstlday ta...Tun Safe ya Shigo..Kinga yadda ina barci ya Murdemin kunni Kamar zanyi kuka..Yana Dakinsa yana Barci yanzu Kafin ya Tashi Barci na karbi Hukuncina.."Farinciki Daya Cika Zuciyar Diza Yaushe Rabon Da Taga Abun Sonta Wannan Labarin yayi mata Dadi.
Cikin Farinciki tace"Ka gano Laifinka kenan My Honourable..?yana shafa kansa yace"Eh..Kanmganar zuwa Maruka ne.."Kai ta gyada Tana Fadin"Uhm..Ai na sani.Mansur Allah ya Shiryeka.."Yana Dariya ya amsa mata sun dan Taba Hira Yacr yaushe Zata Dawo Tace Sai ta gama Sallaman Mutane Zuwa La"asar Zata Dawo kana suka Katse Kiran Diza Taji kamar an sakata a ajannah Tana aiki Tana Mirmishi ita kadai Har Hauwa sai Da ta kalleta Tana fadin"Madam kamar an biya miki Kujeran makka..?
Diza tayi dariya Tana Fadin"Kai hauwa saka ido ko..? Ai wannan Farincikin nawa yafi Biyamin Kujeran maakka."Tana Dariya Tace"Allah Madam..?
Bata kara mgana ba ganin basu kadai bane Ashagon akwai masu Jiran kwalliya da wadanda akeyimawa ammh Ranar Duk wanda yaga Diza Sai ya Fahimci Fara"anta ya Karu Sauri Sauri Take tana son Ta gama Komai Ta koma Gida Ta Sakashi acikin Idanuwanta.
Mastur bai Tashi ba sai Bayan Azahar Ya tashi da bacin ran Barci yasa bai samu sallah ba agurguje ya Fada Tiolet yayi alwala ya Fito ya Shimfida Darduma yayi sallah yana Zaune yana Addu"a Mansur ya Shigo Dakin sai ya gansa ya Tashi Cikin Fara"ansa ya isa Kusa Dashi ya zauna yana Fadin"Ashe ka tashi..?daman yanzu nake Shirin Zuwa na Tasheka Har munyi sallah
Baice komai ba sai da yagama addu"an kana ya waigo yana kallinsa Fuska ya Hade yana Fadin"Kasan Girman Matsayin Mahaifi Kuwa Mansur..?
Ganin irin kallon Dayake mai Da kuma yanayim Muryansa yasa ya gane ba wasa kai ya Dukar yana Fadin"Nasani yaya..Kayi Hakuri abubuwa ne..!
"Har akwai wani abin da zai hanaka zuwa ganin mahaifinka bai da lafiya..? Mansur ka bani kunya Bantaba Zaton Haka ka koma Da bana nan ba..Ka baci Sam yanzu baka da Tsausayi.."Mansur kamar zai yi kuka yana son mgana ya Hanashi Mikewa Mastur yayi yana Nimke Darduman Dake Hannunsa yace",Ko ka Dawo Cikin Hayyacika ko kuma na Dakatar da wannan Takaran naka na Dauke ka na maidaka makaranta ka Cigaba da Masters Dinka..Tunda naga Siyarsace ke Sakaka kana Raina mganata Data Baba kuma kana Banzatar da Mahaifinka da yan"uwanka.."