Sashe 14
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin Ikon Allah wani bawan Allah yayi musu Hanya suka Fara Sana"ar Motocin Daga kwatano,Kafin su Rufe Shekara Daya sun samu karuwa Sosai Lokacin Dukkan sun kamallah Karatasu,Alhaji Muhammed ya Riga Alhaji Sunusi Aure in da akayi mai Auran Zumunci da yar"uwarsa Farida,Anan Sokoto ya siya Gida suka zauna sai bayan Auransu da Shekara Uku kana Alhaji Sunusi yayi Aure da Asiya ita yar asalin Garin Sokoto ne kuma Tayi Karatunta anan Usman Dan Fodiyo University.
Bayan sun yi aure suka Hada kan Matansu Waje Daya suna Zaune Lafiya gefe Daya kuma Suna Cigaba da Kasuwancinsu Duk da Shuru basu samu Haihuwa ba Ammh basu Damu ba Suna Cigaba da addu"ansu Cikin Lokaci kadan Allah ya sama Abun albarka shekara Goma da suka shude har kowa ya mallaki katon Gida da Motar hawa sunje sun sauke Farali su da matansu kuma Har sun kai wasu Daga Cikin Danginsu,kana sun Bude wani karamin ma"aikata Da suka saka ma suna WAMAKO AND SONS MOTORS LIMITED..!,Cikin Lokaci Daya sukayi suna suka kuma Shahara Ajahar Sokoto har zuwa Lokacin kuma Allah bai basu Haihuwa ba.
Farida ita ta fara Haihuwar yarta mace wacce taci sunan Mahaifiyar Alhaji Muhammed Wato RUMANA,sai bayan Haihuwan Rumana da Shekaru Uku kana Hajiya Asiya ta Haifi Diza wacce kamar bazatayi rai ba wajen Haihuwarta ba dakyar aka samu kanta,Tun kuma Daga ita bata kara Haihuwa ba haka itama Farida sai ya kasance sun Rumgumi Abunda Allah ya basu Sun gode ma Allah.
Komawar Alhaji Sunusi kaduna kasuwancinsu ne ya Bunkasa Har Kaduna da Sauran Jahohi sun Hada Hannun Jari da wani Kamfani Dake Shigo da Motoci Daga kasashen Waje Dalilin Dayasa ya Dawo Kaduna da zama kenan Hajiya Asiya taji kewa Sosai Domin Sun Saba da Hajiya Farida Tamkar wasu yan"uwa ga Diza da ta saba da Rumana ammh basu da yarda Zasuyi yanayin kasuwancin ne Shekararsu Duka Duka Biyu ne a Kaduna suka Dawo Zaria da Zama Saboda Bude wannan Rishen da sukayi anan,sun Riga sun Raba abun Kamfaninsu na chan Sokoto Takardun da sunan ciki na Alhaji Muhammad Wamako ne na nan Zaria kuma sai ya zama na Alhaji Sunusi Tureta ne sun Raba abun saboda Halin Rayuwa sai dai,Sauran Hannayen Jarinsu Dake wasu kamfanonin Dake makwafta dasu.
Dawowarsu nan Zaria yan"uwan Hajiya Asiya suna zuwa Sosai Lokaci bayan Lokaci hakama Hajiya Farida Tazo ssu Biyu Ita da Alhaji Muhammed Domin Lokacin da suka Tare basu samu zuwa ba Rumana na makaranta ammh bayan sun samu Hutu sun zo sun kwana Biyu yaje yaga wajen sosai yaji Dadin ganin yadda abubuwa suka Tafi Daidai kamar yadda suka Tsara.
*****
Mansur da Diza suna Cigaba da Zuwa Zaria Acadmy,Ayayinda Mastur ke zaman Jiran samakonsa kwatsam Sai gashi ta Fito kuma Daman ya Cike makarantar kwana ne Harda Hassan Gwarzo,kuma Alhamdulillah yasamu da Farko Hajja taso taki yarda yaje makarantar kwana ammh sai Mastur din ya nuna yana so kuma yana Bukata Sai Mallam Habibu ya maramai baya Hajiya Asiya ne Data Shigo Taji Aiya na Fada Taje ta gayama Alhaji Sunusi Shi kuma ya samu Mallam Habibi yace ya kawomai Takardun Makaran nashi,haka kuwa akayi ya Dauko ya bashi ba"a Rufe wata Daya ba Komai ya kamallah Mastur ya samu Gurbin karatu a makaranta Hassan gwarzo Duka abubuwan da suka Biyo baya Alhaji Sunusi yayi komai Harda Provison dinsa da komai da komai yace baya Bukatar Mallam Habibu yace komai Mastur kamar D'a yake garesa bashi da bakin Godiya sai dai yacigaba da mai addu'an Allah yasa ya gama Lafiya.
Ranar da Mastur zai tafi makaranta Mansur haka yake kuka kamar ransa zai Fita haka Diza ma ganin Mansur na kuka sai itama ta kama Ranar itace Rana ta Farko Daya Taba Rike Hannuwan Diza yana bata Hakuri ya Hadasu ita da Mansur din yayi musu Fadan su maida Hankali a karatu Don Allah banda wasa sukayi mai alkawarin Insha Allahu Zasu yi karatu kamar yadda yake so,Hajja ita kanta sai da Tayi Hawaye Hakama Aiya Ga Tsufa Sai kuka Tana Fadin ina zai Tafi ya barta Shi kansa Domin yana Namijin Duniya ne bai yi kuka Haka suka Shiga Mota dashi da Alhaji Sunusi da Mallam Habibu Audu Direba zai kaisu su Hajja na waje suna Daga musu Hannu.
Tabbas Sabo wani abu ne..Ranar Mansur da Diza wuni sukayi wasu sukusuku dasu Kamar basu da lakka Barin na Mansur Dayafi Kowa Shakuwa Dashi Haka Aiya da Hajja su kansu Sunji Dabam yau koda Mastur baya Yawan mgana Ai Sabo wani abu sai dai sun Ji Dadi da su Mallam Habibu suka Dawo suna sanar dasu makaranta ce mai kyau inda Mastur din ya zaba kuma Insha Allahu zai samu karatun Dayake Fata kuma in anyi Hutu zai Dinga Zuwa ganin gida da Haka suka samu suka Saki Ransu Kowa yacigaba da Harkokinsa...
Tafiyar Mastur Kano Shi ya kara Saka Karatun Diza da Mansur kara Lalacewa makarantan Kadai suke zuwa da sun Dawo ba mganar su dauko Littafansu su Duba sai wasa,islamiya kuwa sai sun ga dama suke zuwa Daman Mastur ke matsa musu ko mallam Habibu shi kuma yana kasuwa Mastur kuma baya nan Hajja Ko tayi musu mgana Sau Daya bata karawa Ballatana Aiya,Hajiya Asiya kuwa Tana da i don"t Care kuma bata som mtsama yara In tayi musu mgana Sau Daya suka Nuna basason zuwa kyalesu Take yi Alhaji Sunusi kuma Baya zama yana Kamfani inda yake da Office dinsa sai Dare yake Dawowa ba wanda ya Fahimci karatunsu ya Fara Rauni Ballatana ya kwaba musu.
Dawowar Hutun Mastur na Farko ya Fahimci Sai a Hankali Karatun Bokon suna Zuwa Dole na addinin kuwa Duk sun watsar wanda suka sani a baya sun manta Dashi yayi Musu Fada Sosai suka nuna sun ji Zasu gyara a hutun da yayi sun Dage saboda yana mtsa musu ammh Da Zarar ya koma Shikenan sai ungulu ta koma Gidanta na Tsamiya kuma Laifin Duk na Mansur ne Shine Babba Im ya ce Diza tayi abu bata Tsallake mganarsa toh shima ba son karatun yake ba sai Su wuni agidan su Diza suna kallo ko suna Buga Game Hajiya Asiya bata da wata Damuwa balle Har ta kwaba musu.
Zuwa Lokacin Zumunci mai karfi ne ya Shiga Tsakanin Gidajen Biyu,Alhaji Sunusi ya Dauki Mallam Habibu kamar Dan"uwasa kaninsa baya Zartar da komai sai da Shawaransa wani Zakka ne im zai Fitar shi zai samu kan mganar Alhaji Sunusi Duk wata kamar yadda zai Siya kayan abinci agidansa haka zai aika Dashi Gidan Mallam Habibu komai na Rayuwar nan babu abunda suka Nema suka rasa Tun Mallan Habibu na Jin Nauyin Alhaji Sunusi har ya Daina Dalilin Haka yasa Shima in ya samu alherin yake ma Mutane irin su Usman Tunda ko bakomai bazai manta da karamincin Usman garesa ba.
Doguwa kuwa sau Daya suka Taba zuwa sanda karime ta Haihu Yayar Hajja sun je Dukkansu sun kwana Biyu sun Dawo Lokacin Mastur na makaranta da Mansur suka Tafi Da Diza wacce tace sai taje suka Tafi da Ita a zuwan da sukayi ne Sule mahaifin Mansur yazo ya Roki Mallam Habibu kan zai Tafi da Mansur chan maruka yan"uwan su gansa Shima ya gansa Mallam Habibu bai yi Gaddama ba ya amince sai dai Diza tace itama da ita za"a je sai yace ya Tafi dasu Dukkansu Lokacin da Goggo da Zainabu suka ga Mansur sunyi mamakin ganin girmansa da yanayinsa Lalle ya samu Chanjin Rayuwa Ballatana Sauran yan"uwan nashi Duk ya Fita Dabam Dasu Goggo Kasa Boye Bakincikinta Tayi balle da suka ga Diza Sulen yace musu da ita suka zo Daga Zaria yar makotansu ne sun ganta yar gayu Kuma Daga ganinta Sun ga Jinin Kudi da Jin Dadi,Da sule yaso su kwana ne ammh Diza ta saka,kuka Dole acikin Daran ya Dawo Dasu Doguwa Gari na waye suka koma Saboda makaranta kuma Daman Audu Direba ne ya Taho Dasu kuma yazo ya koma Dasu.
Jin Dadin Rayuwa Sai dai su mallam Habibu su bama wasu labari,Suna Cikin Rufin asirin Allah,Mansur kuma ya zama Dan gata Domin komai Tare da Diza ake musu Mastur kuma Duk wata Alhaji Sunusi na Turamai Kudi ta Hannun Wani malami amakaranta lokacin da suka kaisa ya karbi Lambarsa Shi yake Turama kudin yayi mai Siyayyah Shima baya Cikin Wata Wahalan Rayuwa in sukayi Hutu ya Dawo yayi kiba ya kara Haske sai da Ramar Makaranta da kuma Chanjin Rayuwa Hajiya Asiya da Hajja sun zama kamar kawaye ko nace yan"uwa basa iya Boye ma Juna Komai Hajiya Farida Tasha Zuwa sukan Shigo Tare da hajiya Asiya su gaisa da Hajja Har ma suyi ta Hira Sau Daya dai suka Taba zuwa da Rumana itama kamar mastur Take bata da Hayaniya Ballatana yawan mgana sai dai ta zauna Tayi Shuru Tana kallon Diza da Mansur suna abunsu.
Tun Mastur na Dawowa Hutu yana Matsama Su Mansur da Karatu har yagaji ya saka musu Ido ganin sun yi Nisa basa Jin Kiran sai kawai ya Fita batunsu ammh bai Fasa yi musu Fada ba sai su nuna kamar sun ji da sun Fara kwana Biyu sai su Bari,Bawai basa Karatun bane suna yi ammh basa maida Hankali Har gwara ma na Bokon Dole sukeyi ammh na Addini kuwa Har suna manta na Baya Diza kuwa Daman Karatu ba Damunta yayi ba Tafi son waasa Data Fara wayau kuwa Game da kuma Kallo Sai Shima Mansur yake Biye mata ba wanda zai iya ma wani Fada acikinsu.
******
Tafe Tafe Rayuwa haka tacigaba da Gangaragarawa Cikin Kudiran Ubangiji Gashi Har Mastur ya zana Jarabawar Fita aji 6 ya dawo gida yana Jiran Sakamako Lokacin yana da Shekara 19 aduniya ne,ayayin da Mansur ke da Shekara 15 aduniya yana SS1 ita kuma Diza Tana da Shekara 11 aduniya Tana kuma JSS1 ne,Dukkansu sun Girma sun Fara mallakan Hankalin kansu.