← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 94

Sashe 73

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Da wurin misalin 2:30pm na Rana Jirgi ya sauke Mastur a kaduna Daganan bai ma yi Tunanin kiran wani Sargent dinsu Daganan Reshensu na kaduna ba ya Fita ya samu mai Mota yace zaria zai kaishi Shi kadai Tasha,nan da nan kuwa ya samu ammh basu Fita Daga kaduna ba sai da sukayi Sallah Domin Direban ne yace zai yi sallah kafin su mika jin haka yasa Shima yayi Sallar azahar ya Hada da La"asar sanin da yayi kafin su isa Zaria La"asar ta gabato Saboda Zullumin Dayake Ciki baya ta Cikinsa ma.
Arude yake shiyasa bai ma Tuna daya kunna wayarsa balle ya Nemi wani Daga gida ba,Kuma Saboda Baya Cikin Natsuwarsa adaidai wajen Barrak na Jaji Hatsarin ya Faru kuma sunce Lokacin ko Kauda Motar Mansur din Datayi Dameji ba"ayi ba da Motar Bua din da sukayi karo sai dai Motoci sun Rika Zagayesu suna wucewa Allah ya gani yaga Motar ammh Sam Hankalinsa bai basa ya Tantance Motar ba Duk da ta Lalace ta Gabanta da Bayanta.

Sai 4:10pm Mai Motar Daya Dauka ya Shigo Layinsu na Hanwa Irin Tarin Motocin Da Mansur ya gani ne Tundaga Farkon Layin nasu abun ya kara Bashi Tsoro Allahu Akbar Mansur akwai Jama"a Shi din mai Masoya ne zuwa Lokacin Tuni Mutane sun cika anguwan Tasu Tunda Daga Taron da Za"a gudanar achan kaduna Taro ne na Charmo mi da kuma Yan Majalisun Jaha,wanda gwanna ne ya Shirya Taron da kansa To daga chan suka samu Labarin rasuwar Mansur Taron bai Samu ba Suka Tarkato zuwa nan Zaria Domin samun Jana"iza Gwamna bai zo ba ammh ya aiko Wakilinsa,Shiyasa wajen ya kara Cika da Motoci sai Taron matasa Wanda Daman Kowa ya sani Mansur na Jama"a ne.

Mastur ganin Cinkoson Ababan Hawa Data Mutane yasa ya Umarci Direban Daya sauke sa Daga Chan gefe,koda ya Fito Daga Motar kamar kafafunsa baza su iya Daukansa ba Haka yake ji Walet dinsa ya Ciro ya Mika ma Mai motar nan kudi wadanda bai san wayan adadinsu ba Hankalinsa yayi gaba Direban nata mgana ganim kudi wajen 10k ammh bai ma san yaanayi ba jefa kafarsa kawai yake yi Hannunsa Dauke da Walet dinsa da bai ma da karfin maida ita inda ta Fito ko wayoyinsa Dake jikinsa ji yake sun mai Nauyi Tuni Rauni ya gama Bayyanamai ya Fara Tunanin kodai Baba Habibu ne ya Rasu..?ko Hajja ce..?ko dai Aiya ce..? Sam Hasashensa da Tunaninsa bai taba kawo masa Dan"uwansa bane Ko acikin zuciyarsa bai Shirya Rabuwar tasu yanzu ba.
Ya fara Dumfaro Kofar gidan nasu da kafarsa Abunda ya Bashi mamaki ganin Mutane haka yana ganinsu ammh bazai iya ma gane suwaye ba Kuma sai Nunashi akeyi Cikin Tsauaayawa,bai nemi Tsayawa ba Burinsa yaji ya jingina da Abunda Zai Taresa Faduwa yadda yake jin Kafafunsa na rawa.

Bai kara jin wani Dum a tsakar kansa ba sai da ya kariso Kofar Gidan nasu yaga an Wangale get ga Mutane nan aciki da waje Cikin wani yanayi wasu kuma suna alwala Idanuwansa sun Hangi masa Baba Sule Dake kuka Hawayensa Bibbiyu bai gama Farfadowa ba kawai yaga Wani Kamar Baba Habibu da wani Wanda bai sani ba sun kamo makara Zasu Shiga gidansu Dashi Daidai Lokacin da Daddy ya Fito idanuwansa Jajir alamun yasha kuka yana Fadin"mu Hanzarta..Lokacin Janaza din Har cika..!

Kamar Daga sama sukaji Muryansu saman kansu Cikin wani irin Amo da Firgici yace"Dad...Ddy..Waye...ya rasu..?yana Rarrabe mganar kamar mai In"ina sai Alokacin ma aka Lura Dashi Gabadaya sai aka Zubamai Ido Baba sakin makaran yayi da Sauri Sagir Dake gefe ya karbeshi Suka Nufi Cikin Gida da ita Hankulan Mutane duk ya Dawo kan Mastur,Baba Habibu Da Daddy suka kalli Juna kafin su karisa ga Mastur din Dake Tsaye kikam kamar an Dasashi.
Dafa kafadarsa Daddy yayi yana Fadin"Alhamdulillah..Ashe ka samu Labari..?
Mastur Tsuri yayi ma Daddy da ido,,in ya kalleshi sai ya juya ya kalli Baba Habibu kamar bai Fahimcesu ba,Sai dai ya samu kansa da bakinsa da Fadin"Ba..ba.meya faru ne..? Bangane wannan Taron ba..? Naga makara ne an shiga da ita cikin gida waye ya rasu..!? Hajja ce ko Aiya.?
Kallon kallon aka Shiga yi Tsskanin Baba Habibu da Daddy,an rasa wanda zai Fara yima mastur mgana acikinsu Su azatonsu ya samu labarin Rasuwar ganin Mutuwar ta Zaga ko"ina Tunda dai basu same sa ta waya ba,
Bakinsu yayi nauyi matuka Kowa bashi da wannan Jarumtar ganin haka yasa Mastur ya karisa ga Baba Sule Dake tsaye kusa da yan"uwanshi yana ta Sharan kwallah,gabansa ya Tsaya Cikin wani yanayi yace"Baba sule wai koken koken me kuke yi.? Nace a Fadamin meyake Faruwa ne..? Waye ya rasu..?ko so akeyi sai Zullumi da Tashin Hankali ya saka Zuciyata bugawa ne..?

Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Hargagin irin mutum baya cikin Hayyacinsa Da Sauri Baba Sule ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Sai Hakuri Mansur Kai akayi ma Rashi bamu ba..Allah yayi ma Dan"uwanka Rasuwa..!
Alokacin Kwakwalwar Mastur ta Dole ne bai ma Fahimci wani abu ba,Kalmar Dan"uwan ne ma ya Bace mai sam acikin Kwalkwalwarsa,Ya kasa ma kama wani Dan"uwan nashi ake Nufi Saboda Tsabar Firgici ko Sunan Mansur bai kamo ba Cikin Rawan baki ya Furta"Wa...ni Dan"uwan nawa..?
Yafada gabadaya Idanuwansa suna Waje ganin haka yasa Baba Habibu yayi Saurin Rikosa Daddy ma ya Riko Gefen kafadarsa ganin Mutanesuna kallonsu basu Tsayar dashi ba sai da suka Shiga Haraban gidan kana Baba Habibu ya Dago yana kallon Cikin Idanuwansa yace"Mastur Kayi hakuri...Allah yayi ma Mansur Rasuwa Sakamakon Hadarin Mota..Sai dai muyi Fatan Allah ya jikansa da Rahma Allah ya sadashi da mala"ikun Rahma"
Daddy yana ta amsawa da Ameen Lokaci Daya yana Bubbuga kafadan Mastur din alamun Lallashi.

Mastur Dayaji kalaman Baba Habibu Tamkar saukan aradu acikin kansa Cikin wani irun yanayi yaji Zuciyarsa Tayi nauyi,Kafafunsa sun yi Wani rin Sanyi kamar wanda Harshashi ya Shigesa,Gangar Jikinsa kuma kamar ba Nashi ba Miyan bakinsa sun kafe,Idanuwansa suna Fari Fari saboda irin yanayin Daya shiga kamar wanda yake Cikin Coma kunnuwansa suna ijiyemai amsa kuwwa na Cewa Mansur yarasu Sakamakon Hadarin Mota.
Ganin yanayin Dayake Ciki ne yasa Baba Habibu riko Hannunsa yana Fadin"Mu je..Adauko Gawan Dan"uwanka Da Hannunka Mutane sun Hallara Jana"izan damam karfe 4:00 ne.."Shidai Mastur kamar baya jin ma mgana Saboda Kunnuwansa kamar sun Nane sama sama yake jin mgana Shidai Kamar wani Rakumi da akala,Sai tsintan kansa yayi Cikin Tsakiyar Falon Hajja yaga Mata Zazzaune suna kuka suna Kallonsa suna kara Karfin kukansu yadda Yake alokacin Baya ma Bambamce Fari da baki Kamar irin wanda ya Mutu kafin akai shi Kabari yana ji ammh bazai iya mgana ba Ballatana Tantance matan Dake Falon
Bai kara Jin kamar Yana Cikin wata irin Rayuwa ba sai da Baba Habibu ya sadasa da Uwar Dakin Hajja bai sakesa ba ssi Daya dangantasa da gaban Gawan Mansur da aka Riga aka Hadashi Cikin likafi kuma Har am Sanyashi Cikim makara an Rufeshi da Zanin Hajja,ga Jini Duk ya wanke likafin Saboda Fashewar kansa Jinin Har alokacin bai Tsaya ba.
Chapter 73 · 0% Book details