← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 94

Sashe 1

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*HAKKIN MALLAKA⚒️🚫Wannan Labarin Gabadayansa Mallakata ne juyasa ko Sarrafashi ta sigan maidashi Audio ko kuma Sakashi a Youtube Channels ko kuma Daukansa Zuwa wani kafar sada Zumunta batare da Izinina ko Sanina ba❌Littafin Da Duka Labarin mallaki na ne...!🙅*

*Bismillahir Rahmanir Rahim in the name of Allah The most Beneficient the most Mercefull praise be to Allah load of The words*

*Page1️⃣*

*KANO STATE..*
_*Doguwa Local goverment.*_
_AREA:Ririwai_
*SHIMFIDA..*

"A karamar Hukumar Doguwa Dake Jahar Kanon Dabo a Wata anguwa mai Dauke da Gidaje masu karamin karfi na Hango Wani Karamin Gida na Ginin kasa da Misalin karfe 3:30pm na Talatainin Dare da Hasken Fitila Daga Tsakar Gidan da alamu wani Abu na Faruwa agidan Har takai masu Gidan basu saka Hakarkarinsu a kasa ba Domin kwanciya ba,kila saboda wani yanayi ko Rashin Sukunin Danayi Hashashen Mazauna Gidan mai Dauke da Shashe Guda Biyu Da ke matsaikacin Gidan.

Wani Matashi ne Domin akallah zai kai Kimamin Shekara Talatin da Biyar a Duniya ayanayinsa Dogo ne Mai Cikar Ingarman Jiki Da kwanji Kallo Daya zakamai ka Fahimci ba Rago bane Domin akwai Tsantsan Jarumta irin ta Manoman kauye Tare Dashi Fari ne sai dai Wahala Irin ta Mazauna kauye yasa Kalarsa ta koma Duhuwa,wanda ya Sauya ya bada wani kala Dabam.

Safa da Marwa yake yi Kofar wani Daki Wanda yaji Filista da Shafan Farin Fenti Hannayensa Suna Goye a bayansa ne yadda yake Safa da marwan bakinsa na Motsi Alamun baya Cikin Natsuwa akwai Tashin Hankali Karara a Fuskarsa Da Hasken Jan Lantarkin Dake Bakin Kofar Dakin ya gama Gauraye Karamin Tsakar Gidan ya haskashi gabadaya.

Wata Yar Dattijuwa ce ta Yaye Labulen Dakin Ta Fito Lokaci Daya Tana gyara Haban Zaninta a kallah Ashekara bazata gaza 58 ba Sai dai kallo Daya zakayi mata kasan Tana da alaqan Jini mai karfin Tsakaninta da Matashin Dake Safa Da marwa abakin Kofar.

Yana ganin ta Fito Da Hanzari ya Isa Gareta yana Fadin"Innanmu..Innanmu..Ya ake Ciki..?

Ya Fada Cikin karaya da wani Fargaba wanda kallo Daya zakayi mai Kaga alamun Hakan ya Bayyana a saman Fuskarsa.

Inna Hasiya ta Sauke Numfashi Lokaci Daya Tana kallon Fuskar Dan"ta Habibu Daya Gauraye da Fargaba da Tsausayin Halin da mai Dakinsa Take Ciki Cikin son kwantar mai da Hankali Ta Rike Hannayensa Duka Biyu Tana Fadin"Har yanzu Bata Sauka ba Habibu..Ammh Tana kan gwiwa Insha Allahu yanzu Zata sauka Kadaina Damuwa Kaji ko..?

Cikin Karaya ya Girgiza kai yana Fadin"Innanmu Ko Zan Fita na samo Mota ne mu kaita nan General Hospital mugani..? Kai ta Girgizamai kafin ta samu Zarafin Mgana sukaji Numfashi mai karfi da Salati lokaci Daya Muryan Hajara ya Gauraye Gidan Inna Hasiya ta Saki Hannu Habibu Ta Fada Dakin Shima kamar ya Bita Haka yaji ammh Ba Dama sai ya koma ya Jingina Jikin Ginin Dakin yana Maimaita kalmar.

"Hasbunallahi wani"imal Wakeel.."

Haka ya Dinga maimaitawa a sarari Saboda Fargabansa da Tashin Hankalin Dayake ciki ya Ragu Cikin Ikon Allah kuwa sai yaji ya Fara samun Natsuwa Ya Hada Hannnuwansa duka biyun Ya Daga sama Yana Fadin"Ya Allah..Kai ne Ubangijin Sammai da kassai..Kai ne Ubangiji Duka Hallitun Duniya baka Haifa ba kuma Ba"a Haifeka ba ya Allah kafi kowa sanin Halin da Duka Bayinka suke ciki Kashewa da Rayawa Duka suna Hannuwanka ne,yau in ka Dauke Hajara Zan yi Takwalli Zuwa Gareka na kuma yi Godiya mai yawa ammh In ka Sauketa Lafiya Ita da Abunda ke Cikinta Zan kasance Cikin Farinciki kuma Zan Cigaba da Godema Ni"imarka Har na koma ga Gareka ya Allah.."

Ya Karishe Fada wasu Zafafan Hawaye suna Zubo masa Daidai Lokacin da wani Farin Dattijo mai Farin gashi ya Bude Wata Kofa Daga Gabas din Dakunan Guda Biyu Dake Barayin ya Fito Yana gyara Carbin Hannunsa Lokaci Daya Da Kwanon sha Cike Da Ruwa a Hannunsa yana Fadin"Ya ka nam Habibu..Maza zo ka mikama Hasiya Ruwan addu"an ta bata tasha Insha Allahu yanzu Zata sauka..!

Tsohon ya Fada Lokaci Daya yana Kallon Habibu,Da Sauri Habibun ya taho zuwa gareshi yasa ka Hannu Biyu ya karbi Kwanon Shan Ganin yadda Hannuwansa ke Rawa yasa Baba Jibo ya kurama Habibin Ido Lokaci Daya yana Fadin"Anya Habibu..? Habibu na ne Jarumin maza kuwa..? Yayan Maryama kuma Uba Gareta..?yau kaine naga Rudewa da Damuwa akan Fuskarka mai Cike da Zati da Hakuri..?

Habibi Daya Karbi Ruwan addu"an Yana Fadin"Na kasa Zama Jarumi ne Baba..Bana son wani Abu ya samu Hajara ko Abunda ke Cikinta.."Yafada kamar Zai saki kuka Baba Jibo Ya Dafa kan Habibi Lokaci Daya Yana Fadin"Kada ka Damu...Insha Allahu Hajara Zata Haihu Lafiya da yardan Allah.."Da Sauri yace"Allah yasa Baba.."Yafada yana Juyawa Baba Jibo ya Bisa da kallon Tsausayi Lokaci Daya ya kada kai ya juya ya koma Ciki Lokaci Daya yana gyara Zaman Rawanin Dake kansa.

Da Hanzari Habibu ya isa Kofar Dakin yana Fadin"Innanmu ga Ruwan Addu"a Baba yace ki Bata Tasha.."Daga Cikin Dakin ta amsa mai Sai gata ta Leko Ta karba Kallonta yayi yadda Duk Ta Hada Zufa yana Fadin"Innanmu ko Zan Fita na Buga Gidan Mallam Haruna ko Zai Bamu Mairo Tazo ta kama Miki..?

Kai ta Girgizamai Tana Fadin"Bari dai mu gani Habibu..Muna Fatan Komai ya zama Daidai.."Cikin Son Aro Jarumta ya gyada kai yace"Allah yasa Innanmu.."Daga Haka ta koma Ciki Shi kuma sai ya koma Gefe ya Durkusa kawai yana karantar Duka Addu"a Da Tazo Bakinsa Ko Minti Sha Biyar ba"ayi ba yaji Kukan Jariri ya Karade Gidan Gabadaya Lokaci Daya da Gudan da Inna Hasiya ta Saki.

Cikin Farinciki Habibu ya Mike bakinsa kamar zai yage Saboda Murna Hannu ya Daga sama Lokaci Daya yana Fadin"Alhamdulillah bi Ni"imatis salihat.."Bai gama Rufe baki ba Baba Jibo Shima Dake Ciki yana ta Jan Carbi yaji kukan Jikansa akaron Farko a Duniya ya Fito Jikinsa na Rawa yana Fadin"Habibu Hajara ta Sauka ko..? Kai masha Allah.."

Habibu Da Murna ta Hanashi Mgana ya isa ga Baba Jibo ya Rumgumesa yana Fadin"Ta sauka Baba..Naji kukan Abunda aka Haifa naji gudan Innanmu Baba.."Baba Jibo ya Murmusa Lokaci Daya yana Dafa Bayan Habibu yana Fadin"Sai ka Godema Allah da Ni"imar da yayi maka Habibu.."Dagosa yayi Bakinsa Har kunni Basu samu Zarafin mgana ba Inna Hasiya ta Fito da Sauri Bakinta kamar Zai yage.

Kafin ma ta isa Garesu Habibu ya Fara karisowa Garesu Tana Fadin"Masha Allah..Hajara ta Sauka na samu Sabon Megida..Ya nan mai kama da Habibuna kamar yayi kaki.."Habibu sai kawai yaji ya Rumgume Inna Hasiya yana Fadin"Allah na gode maka.."Su kansu Farincikinsu suke bakinsu yaki Rufuwa nasan wasu zasu yi mamakin ina alkunyar nan..? Habibu Da iyayansa Tamkar Abokan juna ne Duk Duniya bayan su da kanwarsa Maryama yana jin bashi da kowa sai su sune Abokan Shawaransa da Sirrinsa Gabadaya.

Inna Hasiya ta kalli Habibu Tana Fadin"Bari na saka Ruwan wankan da zan gyara su..Na yanke Cibiya kuma an yi Sa"a Mabiya Ta Biyo baya itama.."Baba Jibo yace"Alhamdulillah..Allah kara Lafiya Allah ya Raya Abunda aka Samu.."Dukkansu suka amsa da Ameen da Sauri Habibu yace"A"a Innanmu Ki koma Ciki wajenta..Bari na Dora Ruwan Zafin.."Inna Hasiya tace"Shikenan..Ka Dora Babbar Tukunyar nan ne.."Cikin Hanzari ya wuce karamin Madafin da aka ginashi da kasa yana Fadin"Toh Innanmu.."

Cikin Dakin ta koma Wajen Hajara Ta Cigaba da Goge Wajen daya Baci da Jini Mabiyan da Cibiyan Kuma ta Nannade su Cikin Wata bakar Leda,Yaron kuma Ta Namnadeshi Cikin wani Zani Ta Dorashi Gefen Hajara Dake kwance Tana Maida Numfashin Wahala.

Cikin kulawa Inna Hasiya ke Fadin"Sannu da Kokari Hajara..'Hajara ta Kauda kai ta kasa Hada ido da Inna Hasiyan Saboda kunya sanin Halinta yasa Innar Bata Damu ba ta Fice da Zanmuwan da suka Baci da Zani Tana Fadin"Kai sabon Megidana nawa Daga gani zai Taba Rigima.."

Tafada jin kukan Dayake yi Tayi Yana Inya..! Inya..Inya..! Koda ta Fita Har Habibu ya Hada Wuta da Itace ya Saka katuwar Gwarwa ya Cikata da Ruwa ya Dora,Daga ganin yadda yake aikin Zaka san ya Saba Da irin wadanan ayyukan Inna Hasiya na Fitowa da kayan Habibu yaki barinta Ta Wankesu Shi ya karba nan da nan Ya Dibi Ruwa Cikin Katon Bombin da shi ya Cikashi da yammah bayan ya Dawo Daga gona kamar yasa yau din Zata kasance Ranace ta Musamman awajensa.

Tsab ya wanke Zannuwan nan masu jini ya Shanya Lokacin Har Ruwan ya Tafasa Inna Hasiya Ta Diba tayi ma Yaron wanka ta Sanya mai kayam sanyi masu kyau wanda Maryama ta Siyo ta kawoma Hajara Cikin kayan Datake Tarawa ne na Haihuwanta Wanda har yau Allah bai Bata ba.

Shi kuma Baba Jibo Shi ya Karbi Cibiyar da Mabiyan Ya Haka Rami ya Binne su Duka acikin Gidan ta chan Baya ya maida kasa ya Dandade,Inna Hasiya na Gama gyara yaron ta Fito ma dasu Habibu Dashi wannan karon Sai Habibu yayi kara ya bar ma Baba Jibo ya Fara karban yaron Dake kama da Habibu sak Lokacin yana Jariri.

Inna Hasiya Daki ta koma Ta Kamo Hasiya zuwa Makewayin Dake Chan gefe Katange da Langa Langa Domin yimata wanka Habibu ya Bisu da kallo Kamar ya kamota ya Rumgumeta ya Jadaddamata Godiyarsa Baba Jibo Bakinsa yaki Rufuwa Fadi yake"Hajara Sannu Kinji ko..? Allah yayi Miki albarka.."

Bata samu Damar mgana ba,sai ma kanta Data Dinga Rufewa Domin Hajara mace ce mai kunya Da kawaici Sai da Suka Shige Makewayin kana Habibu ya Sauke Numfashi yana Leken yaron a Hannun Baba Jibo Shikuma Lura da hakan da yayi sai ya karisa addu"an Neman Tsarin Dayake ma yaron ya Mikama Habibu yana Fadin"Karbesa..Kayi masa addu"a ka kuma sakamai albarka Daga bakin ka mai albarka Habibu.."Hannunsa da Jikinsa na rawa ya karbeshi Lokaci Daya yana kuramai Ido Shima yaron kamar ya sani ya Bude Idanuwansa Tar yana kallon Habibu wanda Hawaye suka Cikama Kwarmin Ido.
Chapter 1 · 0% Book details