Sashe 79
Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rumana ta kira Diza a waya Tayi mata Barka tace Ta na nan Dawowa ita da Umma Zasu zo Daga nan sokoto Ashe kanwar Mommy Taje chan tana kula da Dizan Anty Hadiza,Mastur bai kira Rumana ba sai Da aka kwana aka wuni kana ya Kirata yana Tambayanta yaushe Zata Dawo tace Umma take jira Daganan bai ce mata komai ba sai itane ma Tayi barkan Haihuwan Dizan.
Sai ana Jibi suna suka Dira zaria Ita da Umma da kayan Sunan Umma Niki Niki ita da Abba,Rumana Taga abun mamaki Babu Abunda Mastur bai siya ba na Suna Kama Daga Raguna Guda Biyu sai Sa Guda Daya kayan abinci Komai da komai ya Tanada,Ya kuma bama Dizan 200k yace ta Rike a Hannunta in tana Bukatar wani Abu Ita da kanta Dizan take Fadamata Ranar da suka zo ita da Umma,Bata Damu ba kuma Bata Nuna Bakincikinta ba Domin Shine komai yanzu.
Nan yazo ya sameta suka gaisa da Umma Kana ya Dauketa suka Tafi Gida sai adaran ne yake Shawartatan me ya kamata ya Siyama Hajja da Aiya da Mommy da Mutanen maruka Rumana tace Lokaci ya kure sai dai In zasu je Kasuwa su suyi Atamfofi Su kai Dinki a sakarmai kudi Za"a samu kafin Safe Shine fa da Safe ya Bata kudi ta Nemi Rakiyan Mardiyan Sukaje ta Siyo Atamfofi na adadin Mutanen Ta kai Dinki ta kuma bada kudin Dinki Wajen Telan Diza ne wanda ta Hadata da ita,Kuma Daman ya bata 50k yace itama Tayi ma kanta Siyayyah sai ta Siyan ma kanta less Daya da Atamfa guda Daya sai ta Siyan ma Mardiya less Daya ta kara musu da Material ita da Diza sukayi anko.
Ana gobe sunan su Inna Zainaba suka iso Harda inna karime da Maryama Daga kano,Sakina ce kadai tazo Mariya nada Tsohon Ciki,Sai matan yayyin Baba Sule su Biyu da suka zo sai Balaraban kawu Usman da makota da akayi ta Hidima dasu
Bangaran ruwa da Lemuka Mota aka Sauke agidajen Biyu Su Snaks kuwa Daga Catering din Diza akayi Merry ita da Sauran Ma"aikata suka zo Dashi Lalli kuma Wata ce Hauwa ta kawo Tayi ma Diza Harda kitso itama Rumana Tayi gyaran kai itama an Zirara mata Kunshi Aranar Da daddare Telan ya kawo Kayan Rumana ta Damka ma kowa nashi tace in ji Mastur ,Inna Zainab dasu maryama da Sakina sai Inna karime Balaraba,Umma Mommy Anty Hadiza da Ayya Tsohuwa mai Ran karfe sai na Mardiya sai nasu da tayi musu anko Ita da Diza,Diza ta karba Tana ta Godiya.
Basu yi wani aiki ba Tunda abincin ma aikatau suka kai,Shiyaasa washegari Tun Safe Bayan Mahauci yazo ya yanka Raguna Kowa ta Tsala wankanta,Sai Da Safen Mastur yazo yayi ma Jarrin Huduba da Mansur wanda Daman ba inda ya bar Babansa,Kowa sai Fadi yake Mansur ya Tafi ga wani Mansur din yazo.
Hauwa tazo Tayi ma Diza kwalliya Sama sama itama Rumana anyi mata,Diza ta Shiga ta Fita Cikin Tsadaddun kayan da Mastur ya Dinkamata ita da Little Mansur sai da yammah ta Saka Material din da Rumana ta Dinkamusu,sai suka saka atare,Sosai jama"a suka zo musu Wannan Taron,Anci ansha Sosai Kuma anyi kuka da Tuna Mutuwar Mansur Musammsn Diza,Taron Diza agidan tayi shi Taron sauran Mutane kuma Gidan Hajja nan aka gyara Naman Sa da na Ragunan ma su Inna Zainaba suna aikinsu.
Mastur kuma yana Gida,Daddy kuma yana wajen aiki hakama Baba Habibu yana kasuwa duk sai Dare suka Dawo.
Anyi suna Lafiya an watse Lafiya Baki Duk sun koma Gidajensu Lafiya Rumana kuwa sai bayan suna da kwana Biyu Mastur yazo ya Dauketa suka koma Gida Shima a washegarin ya koma ammh Sai da ya Biya Ta gida Yaga Diza da Little Mansur Dayaji Duk Duniya ba wanda yake so da kauna irin yaron nan gabadaya soyayyar Mansur ya Dawo kansa ne Kowa gefe ya koma ya bar masa Domin Dan nashi ne
Umma ma Ta koma Sokoto Anty Hadiza ce kadau bata koma ita keyi ma Diza wankan Jego Ta kuma Kula da little Mansur.
Sai bayan suna da Sati Daya Baba Sule yazo yaga Jikansa ya Daukeshi ya sakamai albarka Yayi kuka sosai kwana Daya yayi ya koma Bayan ya koma Abba ma yazo yaga Little Mansur bai kwana baya koma,Haka Abokan Siyasan marigayi ke ta zuwa barka suna bama Diza abun Arziki Duk Sagir ya gaya musu Haihuwan Dizan aikuwa suna ta Zuwa kuma kowa yazo da abun Arzikinsa Har Chairman din da aka Dora yazo yaga Little Mansur ya bama Diza100k,kyauta Diza fa ta samu kudi bata san adadinsu ba In Ta tasa Little Mansur tana kallo Bata sanin sadda take Fashewa da kuka sai kuma ta kamashi Ta Rumgume tana kuks sai Anty Hadiza tayi ta Fada kana take yin Shuru.
Rumana ta Fara Service dinta anan asibirin Abu dake Zaria,sai dai Itama Lokaci Bayan Lokaci Tana Zuwa Duba Diza da Little Mansur Daya gama Shiga Ran kowa Hatta Baba Habibu Takawa yake ya Shiga Saboda ya gansa ya Daukesa yana ji kamar Mansur ne ya Dawo.
*Shakira.."*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....36*
*Ki biya ki karanta cikin Salama da Aminci 09069067488*
"Anty Hadiza da Mommy suka Hada Hannu wajen Cigaba da kula da Diza da Little mansur wanda Mastur yace baza"a sskaya sunansa ba da Mansur dinsa za"a rika kiransa.
Cikin kwanciyar Hankali Diza take Jegonta Tayi Bulbul Tayi kiba ta Fara maida kibanta,Su hajja ma ba"a barsu abaya ba kowa yana iya bakin kokarinsa wajen kula da Diza da Mansur karami
Babu abunda Diza ta nema ta rasa na Rayuwa ba Daddy ko Mommy ba,Mastur shi ya Dauke duka Dawainiyar Diza da Mansur karami,madaransa kayan waasansa,kayansa pampers komai nashi Mastur ne,Hatta da ita Dizan Nauyinta Duka ya maidashi kansa arana sau ya kirata yafi a Kirga yana Tambaysn Mansur karami Ta sskamai kukansa yaji ko kuma Numfashinsa Kowa yasan Kaunar Dake Tsakanin Mastur da Mansur ne ya Dawo dashi kan Mansur karami.
Baya wata Daya bai ijiye duk abunda yake yi yazo gida ganin Mansur karami ba,kuma baya zuwa Hannu Rabbana da Sha tara na arziki na Mansur karami,in yazo har ya Tafi Mansur wajensa yake wuni ssi in yayi kuka ne ya bada akaima Diza ta bashi Nono kowa dauka yake saboda Mansur Mastur ke Zarya Tsakanin Zaria da Porthercourt,Sai Rumana wacce gabadaya ta la"kanta Abun a Saboda Diza yake zuwa Duk da Hakan take a zuciyar Mastur din ammh kuma Yaana zuwa ne Saboda Mansur karami,da kuma amfani da wannan Damar wajen Samar da Shakuwa a Tsakaninsa da Diza wanda bai wanzuba a tsskaninsu ba abaya kuma Ba Laifi Shakuwa ta Fara Shiga Tsakaninsu ance mai Da wawa kuma mai baka Kulawa yana Samun Wata Daraja akan ne ta Faru da Diza Gabadaya Mastur ya zame mata wani al"amari wanda batasan yaushe ya Farfado ba Soyayyarsa Data Binne Shekarun Baya itace ta Fara Bayyana kanta Batare data sani ba,Yawan kiranta Dayake akoda yaushe da Kula da ita da yake yasa Zuciyarta taFara kwadaita mata Cikar Burinta nan kusa da kuma Tunanin Kila hakan ne yasa Allah ya karbi Ran Mansur Saboda ta auri Mastur sai dai duk da haka Rana bata Taba Fitowa ba ta Fadi bata Tuna da Mansur tamai addu"a ba Shidin wani Jigo ne nata Wanda bazata taba mantawa Dashi ba Har gaban Abada.
Anty Hadiza bata koma Sokoto ba sai da Diza Tayi arba"in kana ta koma Bayan Daddy da Mommy sun cikata da abun arziki harda Mastur ma,Bayan Tatafine ba Dadewa Mommy ta Raka Diza sukaje Sokoto Har Tureta sai da sukaje ta kai Mansur karami Har gidansu Rumana sai da sukaje ta kaima Umma da Abba mansur Karami Wajen kwanansu Goma kana suka Dawo bayan sun Dawo Suka Shirya ita da Mardiya suka je Maruka wanda Duka Dawaniyar Tafiyar Mastur ne ma yayi shi Direban Daddy ya kaisu.
Agidansu Mansur tayi Sati Daya Cur Tare dasu kuma sun ji Dadi kwarai an Zagaya Dangi da ita ana Nuna cewa matar marigayi Mansur ce Kamar su Lasheta ita da mansur karami Har gidan Sakina Taje da mariya,Maryama kuma ita tazo Dataji Labarin zuwanta Daganan Ririwai suka Sauka gidan Inna karime suka kwana kans suka juyo zuwa Gida Zuwa Lokacin Diza tayi kiba tayi Bulbul da ita ta kara Haske Daga gani Hankalinta ya Fara kwanciya.
Bayan Dawowarta ta natsu agida ta cigaba da kula da Mansur karami Wanda take jinsa aranta bama ita kadai ba Kowa da Rana wajen Hajja yake wuni har ya saba Baya yawan kuka akwai Hakuri kamar Babansa,Mardiya in Tana gida Tayi ta Reno in Tana makaranta Hajja ta Goya Tana Jijjiga,Diza ita dashi Sai dare Tunda In Baba Habibu ya Dawo Shima ya Dauka yana mai wasa Hakama Daddy daya Dawo Diza Zata Hawo mai da Mansur karami Sama sai Dare ya Tsala Mommy zata Dawo mata dashi yayi Barci Ita Renon Mansur karami Baya hannunta yana Hannayen su Mommy ne Tsskaninta Dashi Kawai bashi Nono ne ko wanka da Shiryashi Aikin Mommy ce ko Mama Fadime wani lokacin kuma Hajja.
Su Daddy sunyi zama wajen Rabon gadon Dukiyar Mansur Mastur ya bada shawaran saida Motocin Mastur Duka da Sauran kadarori Sai dai yace abar Gidaje Saboda Mansur karami in ya Girma an samu kudi Miliyoyi Masu yawa,An raba gadon Yawancin Dukiyan Rabi da kwatanta na Mansur karami ne sai Baba Sule Dayasamu gado sai Diza ita Ta samu Gida da kudi Sai Baba Sule shima Daya mallaki gidan Mansur na Gra.
Duka Dukiyan Mansur Karami Mastur aka Damkamawa bai karba ba,ya Umarci Diza da taje ta Bude accout da sunan mansur Karami ta ijiyemai kudinsa ita keda alhaki a mtsayinta na uwa Garesa haka kuwa akayi taje ta Budemai banki ta adana mai Dukiyarsa Ta Hada duka da Kudaden da ta samu Lokacin Haihuwarsa Da Rasuwarsa wadanda abokansa yan Siyasa sukayi ta bata,Bata da wani Abunda Zatayi Dasu komai na Rayuwa Mastur ya Dauke mata Uwa uba ga Catering dinta ba Laifi ta samu kudin da Bata san iyakarsu ba.