← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 94

Sashe 53

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mastur ya dago suka Hada ido da Rumana sai kawai ya Dauke kai ya kama Hanyar barin Falon Lokaci Daya yana Fito da wayarsa Daga aljihun gaban Rigansa ganin haka yasa Rumana ta sadda kai Tana Fadin"Gobe nima zan koma Ayya In Allah ya kaimu.."Baba Habibu yace"Allah ya kaimu Allah ya bada Sa"a..'Dukkansu suka amsa da Ameen Ameen Baba Habibu ne ya kalli Diza yana Fadin"Hadiza ke yaushe zaki koma naki aikin..?kafin tayi mgana Fit Mansur yace"Zata koma Baba..Sai na Dawo Insha Allahu..."Baba Habibu ya amsa da Cewa"Allah ya kaimu Allah ya Bada Sa"a..!
Suka amsa da Ameen Ameen Mansur ya kalli Diza yana Fadin"ku tashi muje ko..? Yafada yana gyara zaman Hulan kansa Hajja tace"Zaku shiga wajen su Hajiya kenan..? Mansur yace"Eh Hajja.."Ayya Dake gefe tace"Ku hanzarta Dare nayi..Gashi ance Gidan naku Chan Daji Yake.."Hajja na Dariya tace"Ai chan zamu kai musu ke Hutu Ayyah.."Ayya ta tabe baki Tana Fadin"Sai dai mutuwa Zata Rabamu da Zama daku Hajara.."Fadin Hakan datayi sai Jikin kowa yayi sanyi Baba Habibu ne ya katse Shurun da Fadin"Da yardan Allah Ayya..Allah yasa mu cika da kyau da Imani.."Dukkansu suka amsa da Ameen Daidai Lokacin da Mastur ya leko Cikin Falon Cikin Dakiyar Muryansa yana Fadin"Wai me kuke jira ne..? Dare nayi kuma kusan akwai Tafiya agaban mu gobe kunje kun Zauna.."Ya karishe Fada yana Hararan Mansur Shi kuma sai ya Fara Dariya yana Fadin"Naga kana kallona Ranka ya Dade ba ruwana..Gasu nan Tun da zu nake ta Fama Dasu sun ki su tashi Kamar masu Tsohon Ciki ko Hajja..? Baba ma Shaida ne..? Ya karishe Fada yana wani Daga Hannu Dariya ta Kama su Hajja Shi kanshi Mastur din sai da ya Murmusa Jin Haka yasa Rumana ta yunkura ta Mike Babbar Ledan Dake Gabanta ta Dauka ta karisa gaban Ayya ta Ijiye Batare da tayi mgana ba Ayya ta Kalli Ledan Tana kallon Rumana Tana Fadin"Yar'nan wannan Ledan fa..?Rumana kanta na kasa Tace"Naku ne keda Hajja Ayya..!Ayya ta washe baki Tana Jawo Ledan Lokaci Daya Tana Fadin"Masha Allah..Kai Hajara Kinga Surukarki Harda Wata Dawainiya..La Harda Turaman Zannuwa Habibu kalli Abun arziki Megidana Na yarda Zan yi zaman kishi da Rumana Daga gani zata ji Dani.."Ta karishe Fada tana yar Dariya bayan Tagama Fidda abubuwan Dake Cikin Ledan Duka.
Ba Mastur kadai ba Hatta Mansur yaji Rumana ta Burgesu Ba wanda Cikinsu yayi Tunanin zuwa da wani abu ammh Gashi ita tayi wannan Tunanin Diza kuwa Bakinciki da Kishin Rumana ya kusa kasheta ganin yadda Ayya ke kwararo mata addu"a da saka albarka Hajja kuwa Fadi take"Rumana Harda Wata Dawaniya..? Ummanki Fa ta aiko mana da Zannuwa da kayan Fulawanan da yawa Harda Dambun Naman Nan fa.."Rumana kanta na Duke Take Fadin"Wanchan Daga Umma ne Hajja..Wannan kuma naku ne Daga yarku Rumana.."Baba Habibu Dayaji Yarinyar ta Burgeshi Saboda Ladabinta da Hankalinta ya kada kai yana Fadin"Shikenan kuwa..Allah yayi Miki albarka Dukkanku Allah yayi muku albarka.."Suka amsa da Ameen kafin ta Mike Dauke da Karamar Ledan Zata kaima Mommy Itama Dizan mikewa tayi Hajja na Tsaye Tana ta Godiya Mansur dai yabi bayan Mastur sun fita Diza saboda Haushi ta Fara Ficewa kana Rumana tabi Bayanta a waje suka ga su Mastur kana suka Rankaya zuwa Gidansu Diza.

Mama Fadime suka gani a Falon kasa Tana ganinsu ta washe baki Tana Musu Maraba,Daya Daga Cikin kujerun Falon suka yada Zango Mansur da Mastur,Ita kuwa Diza Mgana tayi ma Mama Fadime ta Hado Ruwa da Lemo ta kawo ma su Mansur Kana ta Kalli Mansur Fuskarta ba Fara"a Tana Fadin"Bari na Haura sama..Na gayama Mommy da Daddy Zuwan mu.."
Mansur yace"Ok..Ku tafi Tare da Anty Rumana mana.."Diza ta kallesa kamar tace wani abu sai kuma ta Fasa kawai taja Jikinta ta wuce Rumana Dake tsaye taja ta Tsaya Mastur Dake Zaune hankalinsa nakan wayarsa ya Dago suka Hada ido da Rumana wani kallo yayi mata wanda yasa Itama Jam jiki tabi bayan Diza zuwa Sama.

Diza na tura kofar Falon Mommy da Sallama Ta iske Daddy zaune yana Shan iske yana Sanye da Jallabiya Mommy na gefensa Suna Shan Fruit suna Hira Sama sama Lokaci Daya suna Kallon Babban Telebijin din Dake Falon sukaji Sallaman Diza Mommy ta Mike bakinta kamar Ya yage Tana Fadin"Wa nake gani kamar Diza..? Diza da Farimcikin ganin iyayanta ya kamata ta Cire Takalminta ta Nufi Mommy da Sauri suka Rumgume juna Daddy na gefe yana Dariyan Farimciki yana Fadin"Khadija..Wato Uwarki kadai kika gani ko..? Jin haka yasa ta saki Mommy ta karisa Garesa ta zauna gefensa ta Yada kanta saman kafadansa Tana Fadin"Nayi kewarka Daddy..Mommy nidai Ki Dawo Wajena mu zauna..'Ta fada Cikin Shagwaba Mommy da Daddy suka Hada ido suka Saki Dariya Sai Diza ta Fara kukan Shagwaba Daddy ya Fara Lallashinta yana Shafa kanta dukkansu Farinciki ya Cikasu sun ma manta da Tambayarta Ita da wa suka zo..? Rumana Dake Tsaye bakin Kofar Falon Tana kallon abunda ke wakana Bata karisa ciki ba saboda kada ta Shiga Lokacin su.
Mommy ce ta Dago kanta sai kawai Taga Rumana da Sauri ta Mike Tana Rike baki Lokaci Daya Tana Fadin"Kai innalillahi..Diza ashe tare kuke da Ruma kuma baki mgana ba Tun Shigowarki..? Sai lokacin Diza da Daddy suka kai Dubansu wajen Rumana Daddy ne ya washe baki yana Fadin"A"a Diyata..Rumana Maraba kariso mana Daga Ciki..!
Jin haka yasa Rumana ta Tako Zuwa Cikin Falon tana Mirmishi Tana Cire Takalminta Mommy ta kariso ta tarota Tana mata maraba Har sai da ta Danganta da Gefen Daddy ta zaunar da ita da Sauri Rumana ta zamo tasauko kasa Tana gaida Daddy Cikin Ladabi ya amsa yana Dafa kanta Lokaci Daya yana saka Mata albaerka.
Diza Dake gefe Sai wani Cika Take Tana batsewa kamar wacce taga wani abun kinta Eh mana ai Rumana Abun kinta ne.

Mommy ce ke fadin"Sannun ku da zuwa..Yanzu kuke tafe da Daran nan..? Ina Mazajen naku..? Rumana ta Dago suka Hada ido da Diza sai kawai Taga ta balla mata Harara ta kauda kai sai kawai itama ta kauda kanta Tana Fadin"Tare dasu muke Mommy suna Falon kasa..Tun dazu muka zo mun FaraShiga wajen su Hajja ne.."Mommy ta Rike baki Tana Fadin"Ikon Allah Gaskiya Diza baki kyauta Shine tun Shigowarki baki yi mgana ba..? Diza ta Tura baki Tana Fadin"To ba yanzu na Shigo ba.."Tafada tana Hararan Rumana ta kasan Ido Mikewa Daddy yayi yana Fadin"Nidai bari na sauka wajen Ya"yana..Asiya sai kun Fito ."Yafada yana Ficewa Daga Falon.
Yana Fita Mommy tace"Bari naje na sako mayafina Mu sauka kasa ko Zakuyi zaman ku anan ne Rumana..? Kafim ma Rumana tace wani abu Diza ta Mike Ta wuce Bedroom din Mommy Suka Bita da kallo Mommy sai abun yayi mata wani iri ammh bata Nuna ba ta kalli Rumana Tana Fadin"Bari na Dauko mayafina Rumana.."Ruma ta gyada kai Lokaci Daya tana Mikama Mommy ledan Hannunta Tana Fadin"Gashi Mommy.."Mommy ta karba da mamakin Tana Fadin"Rumana Miye wannan din..? Tafada Tana Bude ledan ganin Abunda ke Ciki yasa Ta saki Mirmishi Tana Fadin"Duk wannan nawa Ruma..? Allah yayi Miki albarka Nagode kwarai.."Tafada Cikin Farinciki Rumana kanta na kasa Tace"Ameen Mommy.."Mommy Tana Murna ta Shige Ciki Tana Nuna ma Diza Datagani kwance Kan gadomta Tana latsa wayarta ko Dagowa batayi ba tace"Kin gode.."Daga haka ta Cigaba da Latsa wayarta Mommy sai taji Ranta ya baci ta kalli Diza Tana Fadin"Khadija miye haka..!?ya kin zo Tare da yar"uwanki kuma kin Shigo kin barta kin kwanta..?
Diza ta Gyara kwanciya Tana Fadin"Kai Mommy nida Dakin Mamata.."Mommy ta ijiye ledan Hannunta Saman Madubi Tana Fadin"Bana son Shashanci tashi kije wajenta..."Tafada Tana Kari sowa Gaban wardrope dinta ta Bude ta Dauko katon mayafinta ta Saka Tana kara kallon Diza tace"Oya tashi muje gabadaya.."Diza tasan Halin Mommy da Kafiya tunda tace sai ta Fito sai ta Fiton hakanan Tana Tura baki ta Sauko Daga kan gadon Tana Fadin"Shikenan Ni da Dakin uwata baza'a barni na Shakata ba.." Tafada Lolaci Daya tana Wucewa ta Fita Fuu..Mommy ta Bita da kallo Kafin ta Girgiza kai tabi Bayanta koda Mommy ta Fito Diza takai Kofa ta Fice,Mommy taji wani irin Haushin Dizan sai dai bata Nuna ba Ta kalli Rumana Tana Fadin"Mu sauka kasa Ruma.."Rumana ta mike tabi Bayan Mommy zuwa Falon kasa sun iske Mansur da Mastur da Daddy suna ta Hira ga Kayan Sha da Kwalama nan agabansu Diza bata wajen Dakinta na Baya ta Shige abunta.
Chapter 53 · 0% Book details