← Book details Sadaukarwa So Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 94

Sashe 55

Sadaukarwa So Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunanin haka yasa nan take ta Bude Fridge ta Dibi kayan Miya ta Dauko Blander ta Markada bayan ta gyara tafara Soya Nama Kafin ta Tafasa kayan Miya,sai da Tagama kana ta Hada mai Miyar Ta barta Tana Soyuwa Jin ana Kiran Sallar Asuba yasa ta baro Kitchen din bayan ta Rage gas Din Tana Fitowa Falo Mastur na Fitowa Daga Dakinsa yana Sauri Zashi Masallaci Yayi mamakin ganinta kwarai Har sai da ya Nuna Domin ya kalleta Sau Biyu kafin ya Dauke kansa Sabanin abaya sau Daya yakan kalleta ya basar Da sauri tace mai Ina kwana ya amsa mata Da Lafiya yana Wucewa Itama bata kara bi ta Kansa ba ta Shige Dakinta Wanka Tayi Lokaci Daya ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Tana Idarwa Ta koma Kitchen ta Duba Miyar taga tayi sai ta Sauketa Ta Dora Ruwan Zafi Bayan ta saka ganyen Tea da Na"a Na"a,Ta koma Daki ta Cigaba da azkar dinta sai Lokacin Taji Dawowar Mastur ya Shiga Dakinsa.
Misalin 6:00am ta koma Kitchen din Ta Juye Ruwan tea din a Wani Fulas ta Fere Dankali Ta Soya ta Fasa kwai ta Soyashi Kana ta Soya Buredi mai kwai,agurguje tayi komai Ta jera Saman Dining Miyar kuma ta samu Wata Lafiyayyar Kularta mai kyau ta Juye mai aciki ta Rufe Duka Naman Datayi Miyar Dashi ta kawo Falo Saman Dining,Daki ta koma ta Fara Shiryawa Domin 8am take so Tayi mata a Abu Chika Cikin Lokaci Ta Shirya Cikin Riga da Sikat na Wani Leshi mai kyau da yarari Mai kalan Ja ta yafa Gylenta ja da Jakarta da Takalminta,Wayarta ce tayi kara Tana Dubawa Taga Abbanta ne ta Dauka suka gaisa nan yake tambayanta ta isa Asibitin..? Tace mai A"a yanzu take Shirin Tafiya ya kara mata Bayanin in taje Ta Tambayi Dr Hambali ya riga ya gayamai komai Data isa Ta tambayeshi ana Nuna mata Shi Ta bashi Takardan Hannunta ta amsa mai da toh Basu sallama basai da Yabama Umma sukayi mgana Dukkansu sukayi mata Fatan alheri kana suka yanke Kiran Tana Kokarin Fitowa Taji Knooking din Kofarta Sai ta Rarumo Jakarta da Key din Motarta ta Fito Bayan ta saka Takalminta mai Dan Tudu kadan Tana Bude kofar Taci karo da Mastur Tsaye Cikin Shigar Riga da wamdo Duka Bakake na Kamfanin Armani Rigar mai Dogon Hannu ce,kafarsa sanye da Takalmi Sawu Ciki Bayansa Goye da wata Jaka baka,Hannunsa Daya na Aljihunsa Dayan kuma Wayoyinsa da key din Motarsa Tana Bude Kofar bai Tsaya ba ya Juya yana Fadin"Ki fito zan tafi.."haka Kawai ya fada Ya juya Zuwa Cikin Falon Da Sauri Rumana tabi Bayansa Zuwa Falon bai Zauna ba ya na Daga Tsayen ya Juyo yana Mikamata Atm din Daya Fito Dashi Daga aljihunsa Ta saka Hannu ta karba Tana kallonsa na neman karin Bayani Cikin Dakewarsa yace"Daya Daga Cikin katinan Bankina ne...akwai kudi aciki Ki rika amfani Dashi in wata Bukata tataso ko kuma dai In kima Neman wani abu.."Yafada yana kara gyara zaman jakar Dake Bayansa,Rumana ta Sadda kanta kasa Tace"basai ka bani ba..Ina da kudi a Hannuna Na Sadakina kuma akwai kudi acikin Bankina wanda Chan asibitin Uduth ke Biyana na Intenship dina sun Isheni Komai ."
Ko kallonta bai yi ba ya Fara Taku yana Fadin"Ai nasan kina da kudi kuma na bar Miki..So ni zan wuce ba lalle na Zo da wuri ba..Ki kula da kanki.."Daga Haka taga yana Shirin Barin Falon da Sauri ta Bude baki tace"Plz ka Tsaya kayi Breakfast gashi Chan na Hada.."Cak ya tsaya Yana Jinta Yaki Juyowa ba alaman zai Dawo ya Daga kafa ya Cigaba da Tafiya tace"Don Allah ka Tsaya kaci wani abu ya Mastur..Bai kamata ka Dauki Hanya baka ci komai ba.."Ta karishe Fada Cikin Sanyin murya da Shagwaba muryan Datayi amfani Dashi yasa ya kasa Tafiya kawai taga ya Juyo kan Kujera ya ijiye Jakarsa da Wayoyinsa Ya wuce saman Dining Din Rumana Cikin Farinciki itama ta Sabule Jakarta nan Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon tabi Bayansa.
Dasauri ta isa Wajen Taja mai Kujeran Dinning ya zauna akai Tafara Kokarin Daukan Filet zata Zubamai Dankalin da Sauri yace"No..Ki Hadamin Tea.."Daga haka ya Dauke kai da Sauri ta Dauki Mug ta Zubamai Ruwan Tea din Ta Tura gabansa Tare da kayan Tea kamar baya so haka yaja ya Hada Tea din Madara kawai ya saka ya fara sha sai ta Turamai Buredin Data Soya Daya kawai ya Dauka yaci Itama dai Sama Sama tasha Tea din Taci Dankalin,Tana Cikin hakane Taga ya ijiye Mug din Hannunsa ya Mike Lokaci Daya yana Ture kujeran Daya tashi ta Dago Tana kallonsa Lokaci Daya tana Fadin"Tafiyar kenan..?
Kamar bai jita ba kuma ya Jita Tissue yaja ya goge Bakinsa ya Wuce zuwa Falo ya Dauki Jakarsa,Ganin haka yasa Tatashi da Sauri Tana Fadin"Bari nazo.."Da gudu ta Rumtuma Zuwa Kitchen Har sai da ya Juyo yana Binta da kallom Mamaki Abun sai ya Bashi mamaki yayi Tsaye yana Jiranta Chan sai gata ta Fito Dauke da Wata Farar leda Mai Dauke da kananun Robobin Guda uku sai kulan Miyan Tana Zuwa Gabansa Tace"Gashi..Kayi amfani Dashi in kaje Chan.."kamar zai Tambayeta Menene sai kuma ya fasa ya Juya kawai Ita kuma Tabi bayansa Bayan ta yafa Mayafinta Har Haraban Gidan suna Fitowa Mansur da Diza ma suna Fitowa tayi mai Rakiya Dauke da Jakarsa Shima Sai wani Shagwaba take mai Rumana na gefe Tana kallon Ikon Allah Dayake Daga bakin Shashenta ta Tsaya Mastur ya Juya yakarbi kayan Hannun Rumana yana Fadin"Ki kula..Ki Rika Tuki a hankali nan ba Sokoto bace..Zaria ce.."Daga haka ya wuce ya Bude bayan Mota ya saka Kayan Hade da Jakarsa kana ya Rufe Mansur ya kariso sukayi mgana Kafin kowanne ya Juya ya Shiga Motarsa Rumana dai Hannu kawai Ta daga ma Mansur Shima ya Daga mata Diza Dai Har bakin Mota ta isa bayan ta Bude Gaba mazaunin mai Zaman banza Ta Saka mai Jakarsa sun Dade suna mgana Domin har sai da Mastur yayi Ribas yayi Hon Megadi ya Budemai get ya Fice Rumana na Dagamai Hannu Mansur na ganin haka Shima ya Tada Motar kafin a Rufr get din yabi bayansa Dukkansu Daga nan sai da sukaje gida Baba Habibu Da Hajja sukayi musu Fatan Alheri kana kowannensu ya Dauki Hanya Mansur dai sai ya Jira Tawagarsa kana suka Dauki Hanya Mastur kuma Dayasan Tafiyace agabansa Tuni ya Daura Set Belt yana Ta kwarara Gudu Bisa Tituna.

Bangaran Rumana kuwa Tayi kokarin sakarma Diza Mirmishi Duk da suna Nesa ne ammh sai Diza Tayi kamar Bata ganta ba ta Taka ta Bude Kofar Shashenta ta Shige,Tabar Rumana na Binta da kallon Mamaki Kai kawai ta Girgiza ta Koma Shashenta Bata Tsaya Bata Lokaci ba ta Dauki Jakarta da Wayarta Ta Rage duka Fitulan Dakunan kana ta FitoKofar Shashen nata ta Kulle Daman key din Biyu ne Daya na Hannun Mastur,kamar ta Shiga Tayi ma Diza Sallama sai kuma ta Fasa Ta Bude Motarta ta Shiga da Bismillah Ta saka Set Belt Bayan ta ijiye Jakarta agefenta ta kunna Motar Daman Anyi mata Full Tank ammh Duk da Haka zata Tsaya saman Hanya ta kara sakamai ko bayan ta Dawo ne,Hon tayi ma Megadi ya Bude mata get ta Fice yana mata Allah ya Kiyaye Diza na kallonta ta Window Falon Takaichi ya Isheta waya ta Daga ta Kira Mommy tace Direban Daddy ya kawo mata Motar ta 10am take so Ta Fita Zuwa Catering dinta Mommy tace Shikenan Daganan ta yanke kiranta Tana wani Bata rai Daman sun gama Sham Fama da Mansur kan bazata koma ba sai ta kara Jin Sauki ita kuma tace ai taji Sauki sai taje Dayake bayason Bacin ranta bai Ja ba yace Ta koma,Ita Bata yi Niyar komawa ba sai ta kara Hutawa ammg ganin Rumana zata koma yasa Taji itama Zata koma Saboda Kada ta Dauka itace kadai mai Zuwa aiki agidan Kada ta Rainata.
Ba jimawa kuwa sai ga Direban Daddy da Motar Diza Kudin Mota ta bashi ya koma Gida ita kuma Tayi wanka Ta Shirya Cikin Shigar Abaya Daman da Safe Tea sukasha da kwai batajin yunwa Kwan ma Mansur ya Soya tanakwance 10am din Datace ta Fito Itama ta Hau Motarta ta Fice Daga Gidan suka bar Megadi da Gadin gida Diza na zuwa Catering Dinta Ma"aikatanta nata mamaki sun Dauka sai wani Sati Bangaran Catering din ta Fara Shiga Ta Duba Komai Merry tasha Masifa Ita da sauran Ma"ikatan Data Fito sai Shashen Makeup dinta Ta iske Hauwa da Meena suna aiki mai kyau Taji Dadi Sosai Hauwa sai Murnan ganinta Take Tana Hajiya Amarya Diza na Mirmishi Officr dinta ta Shiga ta zauna ta Dauko Wayarta Ta Kira Mansur Tun Tana Cikin Catering yake ta Kiranta Bata Daga ba Basu Jima suma mgana ba yadai ce mata sun isa Abuja 12pm za"a Fara Taron nan itama tace Tana wajen aikinta Daganan sukayi sallama.
Chapter 55 · 0% Book details