← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 165

Sashe 99

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ma ta shiga sannan ya kulle kofar, bin dakin take yi da kallo, taga tray me dauke da kayan shayi da cup din shayi alamar an sha shayi, ya kunna wutan dakin ya sauke curtains sannan ya shiga bandaki, tana jin alamar wanka yake yi ta zamo kasa a hankali ta zauna ta jawo ledan abincin da ya ajiye ta bude, fried rice da yaji liver hade da spicy jollof rice a gefe ta gani, sai peppered chicken, tayi unwrapping cokalin daga tissue dake jiki, har wani rawa jikinta yake ta fara cin abincin, Nihad da bata wani cin abinci sai gata ta cinye abincin nan tasss naman kawai ta ci kadan ta bari don ita cin nama aiki ne a wajenta, kai ta yage yage kana bata baki da maiko, ta bude chilled chivita dake leda shi ma kadan ta sha sannan ta ajiye, Sai a sannan ta fara gani dai dai ta daina jin jirin da take ji, fitowa khalil yayi daga bandaki ya dinga kallonta da mamaki, can yace "Amma wa yace maki naki ne da kika dauka kika ci?" Ko kallonsa bata yi ba balle ya sa ran amsa, sai kuma ta mike ta wuce ta gabansa ta tafi jikin window tana kallon waje da motocin dake ta tafiya saman titi, waii lallai ta jinjina ma yan kauye, Allah Ubangiji ya kawo masu mafita. Tana jin ya fita daga dakin ta juyo a hankali ta dawo gefen gado ta zauna tana tunanin irin rayuwar da tayi na kwana biyu kacal, ita kanta tasan ta rame kuma ta yi baki, tashi tayi daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana sallan Magrib, banda Aliyu babu wanda ke ranta, ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ta murda taji a kulle, dawowa tayi ta fada saman gado ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa......
Chapter 99 · 0% Book details