← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 165

Sashe 142

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Contact https://wa.me/c/2349090591769Bayan Azahar Aunty Maryam ta sakko downstairs tana kallon mai aikinta dake parlor tace "Kin kai ma bakuwar can abinci kuwa?" Mai aikin ta tashi da sauri tace "Wallahi na manta Hajiya" Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta tace "Amma ai baki mance naki cikin ba" Da sauri mai aikin tayi hanyar kitchen, Aunty Maryam ta nufi guess room, bude kofar dakin tayi taga Nihad zaune saman darduma, Aunty Maryam ta shiga dakin, Nihad ta daga kai tana kallonta, Aunty Maryam tace "Kiyi hakuri ashe wancan gantalalliyar bata kawo maki abinci ba ni ina can sama ban sani ba" Nihad dai tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kika ki zama parlon kiyi kallo?" A hankali Nihad tace "Ba komai" Aunty Maryam bata kuma cewa komai ba, Sai ga Murja ta shigo da abinci dakin ta ajiye ma Nihad, Aunty Maryam na kallonta tace "Ki karo lemun" Da sauri Nihad tace "Aa ya isa Aunty" Aunty Maryam tace "Toh zuba abincin ki ci" Daga haka ta juya ta fita daga dakin, All through Khalil na compound wajen shan iska tare da Nadeeyah, kana ganinsu kasan they really missed each other, abincin ma waje aka kai masu suka ci tare, bayan Nadeeyah ta zuba masa drink din kwalin gabansa yana kallonta yace "Thank you" Tayi murmushi tace "Continue... ina jin ka" Ya ɗan buda ido yace "Me xan ce kuma,?" Tace "Ba labarin stay dinka a kano kake bani ba, ai baka gama ba" Yayi murmushi yana shafa kansa yace "Shikenan, all the household are very nyc, i think that's the most important of all" Tace "To ita wannan yarinyar da na ganku tare, yar gidan ce?" Yayi shiru, sai kuma yace "Nihal!! Of course yarinyar mai gidan ce..." Nadeeyah tace "Allah sarki, wani school take?" Yace "Ahmadu Bello" Nadeeyah tace "Ohk, but kasan har yau yan gidanku basu san inda kake ba all those while, a lot of time Farhana da Sajida suna yawan tambayata about u, irin dai suna son su san ko i know about your whereabout" Yayi murmushi bai ce komai ba, tayi sipping drink din gabanta tace "Kasan everything happens for a reason, may be don kaje ku hadu da yan gidan ku kulla zumunci shi sa Allah ya kaddara zaka je kano har kuma ka je gidansu, kaga ai baxa ka manta halaccinsu ba" Ya gyada kai yace "Haka ne" Tace "And you mean har yanzu basu san kai waye ba har bayan da ka dawo Abuja?" Ya girgiza kai yace "Basu sani ba" Tayi murmushi tace "Za su yi mamaki kuwa idan suka san kai wanene, but menene ya ja ra'ayinka har ka je gidan nasu ka zauna bayan baka ta6a saninsu ba sannan ba rasa wajen da zaka zauna a kano kayi ba, infact ko hayar nawa ne nasan xaka iya affording, u can even decide to stay in the hotel don duk da ba salary kake samu ba sannan babu wani source of income don duk Abba ya toshe hanyar but still nasan u neva ran out of cash all that period, Mami na tura maka, Aunty Maryam, Aunty Hamida even though bata kasar...." Murmushi yayi yana kallonta murya can kasa yace "And even you yourself" Ta hararesa tace "A'a ni ka cireni a lissafi don anything mine is urs" Ta tallabi chin dinta ta ci gaba tace "So how did u even know about them? And me yasa kayi deciding zaman gidan?" Yayi shiru yana kallonta kamar baxai ce komai, can kuma yace "I will tell u some other time Nadeeyah" Tace "Why?" Yace "I don't want to talk about it now" Ta langwabar da kai a hankali tace "Amma ka ta6a saninsu ne?" Ya girgiza kai yace "Nace xan baki labarin some other time" Tace "Ohk, but ya kamata ko Mami ka hada da yan gidan su gaisa a waya, su ma za su san kayi appreciating dinsu" Yace "I will do that dear" a hankali tace "But why did u keep on telling me kana USA?" Yace "Saboda nasan xa ki iya cewa xaki zo kano saboda ni, shi yasa ma ranan da muka hadu nace maki in few hours time flight dina xai tashi, don kar ki saka ran za mu hadu" Murmushi kawai Nadeeyah tayi tana kallonsa... sai kusan la'asar suka shiga cikin gida, Nadeeyah ta haura sama shi kuma ya zauna parlor, ko minti biyar bai yi zaune parlon ba Nihad ta fito rike da warmers na abinci da mai aikin Aunty Maryam ta kai mata, tun da suka hada ido sau daya bata sake kallon direction dinsa ba, sai dai kuma bata san hanyar kitchen ba don tayi zaton zata hadu da mai aikin ne a parlor, juyawa tayi ta koma inda ta fito, sai ga Mami ta sauko downstairs tare da Mum din Nadeeyah da Aunty Maryam, Mami tace "Khalil xaka ajiyesu gida daga can mu tafi gida, xata kira driver nace ba sai ta kirasa ba mu ma yanzu za mu tafi gwara mu tafi gaba daya" Khalil ya mike yace "Ohk" Mami ta nufi Aunty Maryam dake answering call tayi kasa da murya tace "Kai ni mu yi sallama da ita, ina ga ai daga nan zata wuce in ta amshi abinda xata amsa" Aunty Maryam ta nufi bangaren da Nihad take Mami na biye da ita a baya, Aunty Maryam ta bude kofar, kwance suka ganta a kasa, Aunty Maryam ta katse wayar da take tace "Me yasa xaki kwanta a kasa ga gado?" Nihad ta mike zaune bata ce komai ba, Mami tace "Naga bata da sabo ne da wuri" Mami na Murmushi tace "Ya sunanki?" Nihad bata iya ta dago kanta ba a hankali tace "Fatima amma ana kirana Nihad" Aunty Maryam ta kalli Mami, Mami tace "To maa sha Allah Nihad, yaushe xa a baki admission letter din?" Sai a sannan Nihad ta daga kai tana kallon Mami, Mami tace "Yaushe suka ce?" Cikin sanyin murya tace "Nima ban sani ba" Mami tace "Toh jiya me suka ce maki a makarantar" Ta sauke idonta kasa tace "Shi ne dai suka gaya ma ba ni ba" Mami ta kalli Aunty Maryam, Sai kuma tace "Toh, ya dai ce kafin sati za ki samu, idan na zo nan din kafin ki tafi to, idan kuma ban zo ba xan bada sako a kawo maki kin ji? Sannan ki gaida su mamanki da kyau" Nihad ta gyada mata kai kawai, Mami tace "Toh sai anjima" Cikin sanyin murya Nihad tace "Nagode" Tana fadin haka ta fara cire dankunnen dake kunnenta tace "Ga dankunnen" Mami tace "Aa, na baki ne ki dinga sa wa Nihad" Nihad ta mayar tace "Toh Nagode, Allah ya saka da Alkhairi" Mami na Murmushi tace "Ameen" Daga haka tace "Mun tafi" Ta juya ta fita dakin, Aunty Maryam ta bi bayanta ta kullo kofar dakin. Khalil kadai ke jiransu a parlon, Nadeeyah da Mum dinta kuwa sun fita compound, Mami na kallon Khalil tace "Ina suke?" Yace "They are outside" tace "Toh mu je" Ya kalli Aunty Maryam yace "Na sa wayata caji idan na ajiyesu xan dawo in dauka anjima Aunty" Mami tace "Ji wani wahalar da kai, ka dau wayar mana idan mun je gida ka sa a cajin" Aunty Maryam tayi dariya tace "Baki ga yanda na saki baki ina kallonsa ba" Ya ɗan yi murmushi yana sosa kai yace "Haka ne" Gun wayar ya nufa, Mami ta juya ta fita daga parlon, ya juya ya kalli Aunty Maryam yace "Kawai bari in bar shi Aunty, ai bamu gama hiran ba dama" Aunty Maryam tace "Toh je ka ajiyesu ka dawo, akwai abinda kake so ayi maka kafin ka dawo" Yace "Aa coffee kawai xan sha idan na dawo" Tace "Toh sai ka dawo son" Daga haka ya fita parlon da sauri zuwa parking space. Wajen karfe biyar da wani abu Nihad ta fito parlor, Aunty Maryam dake zaune parlon tana rungume da autanta Mus'ab ya dawo makaranta ta kalli Nihad tace "Kin fito" Nihad na wasa da fingers dinta tace "Eh, akwai aikin da xa ayi Aunty?" Aunty Maryam tayi murmushi tace "Aa Nihad, Murja ta ma kusa gama girkin ina ji yanzu, karaso ki zauna" Nihad ta karaso cikin parlon ta zauna a kasa, Aunty Maryam tace "Hau saman kujera mana" Nihad ta girgiza kai tace "Aa nan ya isa" Mus'ab dake kallonta yace "Ummi is she our visitor?" Aunty Maryam tace "Yes dear, sauka kasa ka gaisheta" Ya sauka daga jikin mamarsa yace "Good evening" Nihad na kallonsa tayi murmushi don mate din Fadil dinsu ne tace "How are you?" Ya koma jikin mamarsa yace "Fine" Har Bayan magrib Nihad na parlon tare da Aunty Maryam, aka bude kofa Khalil ya shigo da sallama, Aunty Maryam ta amsa masa tana kallonsa tace "Sai yanzu?" Ya karaso cikin parlon ya ajiye jakar hannunsa yace "Eh Aunty, good evening" Tace "Evening welcome, wannan jakar fa? Ko na ta ne?" Ya nufi wayarsa yace "Eh nata ne" Ya dauko wayar ya dawo ya zauna, Aunty Maryam na kallon Nihad tace "Dauka ki kai can dakin" Tashi Nihad tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta dau jakar ta wuce ciki, Aunty Maryam tana kallonsa tace "A kawo maka abincin ko coffeen dai" Yace "Na sha a gida Aunty" Tace "Ohk, Mami tace xaka yi tafiya, yaushe ne tafiyar?" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Nan dai da kwana biyu idan na gama shirye shirye" Tace "Toh Allah ya kai mu" Wayarsa yake dubawa ya ga missed calls din Farooq, ko jiya ya kirasa, Khalil yayi dialing numbersa ya kai kunne, Farooq na dagawa suka gaisa, Farooq yace "Har yanzu baka turo ba Khalil" Khalil ya shafa kansa yace "Nace kar ka damu Yallabai, da da bukatar hakan xan tura maka" Farooq yace "Ehh naji, amma kawai ka turo min" Murmushi Khalil yayi yace "Toh shkkn, Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Farooq yace "Fatan dai kuna lafiya?" Khalil yace "Alhmdlh" Farooq yace "Zariyan a wani anguwa ku ke, ina ga in shigo ko jibi weekend" Khalil yace "Ohk zan tambaya" Khalil yace "Ohk, tana kusa?" Khalil yace "Bari in bata" Mikewa yayi yana
Chapter 142 · 0% Book details