Sashe 135
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gado kiyi kwanciyar ki Baby" Shiru Nihad tayi sai kuma ta mike a hankali ta tafi ta hau saman babban bed din wanda furnitures dinsa kadai ma abun kallo ne, Mami ta dago mata duvet ta mika mata ta amsa ta rufe jikinta ɗon dakin yayi sanyi ta dalilin Ac dake kunne. Har kusan karfe dayan dare Nihad bata ga bacci ba, tuni Mami tayi bacci, da ta tuna wasu abubuwan sai taji hawaye me zafi ta gefen idonta na zuba, she wish she could rewind everything from the scratch, she wish many things didn't happen, daga karshe da taga she needs to cry out ko zata samu saukin abinda take ji a ranta, cike da karfin hali ta mike zaune tana kallon Mami cikin duhu, a hankali ta lallaba ta sauka daga kan gadon ta tafi bakin kofar, nan ma ta tsaya tana tsoron kada kofar yayi kara idan ta bude har ya farkar da Mami, can dai ta runtse ido ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude, bata ji yayi kara ko kadan ba, ta fita ta kullo mata kofar, yana kwance parlon nan ma wutan a kashe yake, a hankali tana tafiya making sure she isn't making any sound ta tafi ta bude dayan kofar ta shiga daya parlon, can wani corner ta tafi ta zauna tana shesshekan kuka cike da tausayin rayuwarta, hawaye kawai take wani na bin wani, tun da ta fito daga dakin Khalil da shi ma bai yi baccin ba ya bi ta da ido cikin duhun har ta tafi daya parlon, he can't say why he is still awake may be over excitement ne na cewar yau gashi a gida da Maminsa after some years, bayan kusan minti 7 ya mike a hankali, shi ma bai kunna wutan ba ya nufi kofar ya bude gently ya fita, ta direction da yake jin shesshekan kukanta ya nufa, kawai gani tayi wani abu da yayi mata kama da statue tsaye a kanta, er kara tayi a mugun tsorace ta mike xata gudu ya rikota, sai a sannan ta ji kamshin turarensa ta rufe fuskarta da sauri a jikinsa tana kuka a hankali, bayan few seconds yace "Saboda kiyi kuka kika fito nan?" Ita dai bata ce komai ba sai shesshekan kuka take tana Girgiza masa kai kawai, ya janyeta jikinsa yace "Zauna nan" ta tattaba bayanta taji kujera, hakan ya sa ta zauna a hankali, yana tsaye inda yake yace "Ki saurari duk abinda zan ce maki yanxu cause it's for ur benefit" ita dae tayi shiru tana jin sa gabanta na faduwa, yayi kasa da murya yace "On no condition xa ki gaya ma wani a gidan nan relationship dinmu, that should be s secret between us har zuwa sanda xa mu cika ma juna alkawarin da muka dauka a baya" Nihad dai kanta na kasa, yace "Nace ma yan gidan admission letter kika zo amsa garin nan, so duk abinda zaki ji na gaya masu gobe ya zama hakan kema a wajenki" Nihad ta share idonta ta gyada masa kai kawai, ya kunna wutan parlon yana kallonta yace "Sai da safe" Bata yarda sun hada ido ba ta mike ta nufi kofar shiga second parlon Mami ya jira har ta shiga sannan ya bi bayanta. Washegari Nihad na tashi taga ita kadai ce dakin Mami, tana kokarin gyara gadon sai ga Bilkisu ta shigo, Bilkisu na murmushi tace "Ina kwana" Nihad ta sauke idonta tace "Mun tashi lafiya" Bilkisu tace "Ai da kin bar shi ma xan shigo in gyara, aikina ne" Nihad dai bata ce mata komai ba ta shigo ta fara abinda zata yi, Nihad ta fita parlor, tana bude kofar first parlor taga Mami da khalil a zaune parlon, Ta gaida Mami da ladabi Mami ta amsa mata da fara'a, ta kalli Khalil suka hada ido, ta kasa barin wajen bata gaishesa ba saboda Mami dake zaune, bata yarda ta kallesa ba tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya, ga breakfast din ki" Mami tace "Bari a kai mata can parlon so that she will be comfortable" Yace "Aa za ta yi a nan" Nihad dai bata ce komai ba, can ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, ya nuna mata breakfast din dake saman tray, ta dauka ya nuna mata inda xata zauna, Mami dai sai bin ta da kallo take because she is so cute and meek, Mami ta kallesa tace "Amma 'yar mai gidan da kake ce min kana zama wani lokacin a gidansa ce ko?" Khalil zai yi magana aka bude kofar parlon, Mimi da Noor ne suka shigo, suka yi wani ihu a tare ganinsa, daga inda yake zaune duk suka tafi da gudu suka rungumesa so happy seeing him, sai ga wasu set din Yan matan biyu Hanan da Farhana, su ma duk suka rungumesa so so happy seeing him, he couldn't help it but smile don shi ma yayi kewansu sosai, Mami dai sai murmushi take, Mimi ta kalli Mami ta fashe da kuka tace "Mami mene ya sa zaki boye mana yayanmu ya dawo, Abba yace he's been around since yesternight" Sai kuma ta fashe da kuka, Khalil ya jawota gefensa yana kallonta yana murmushi yace "Is there any diff between now and the yesternight" Tace "Yes of course, wallahi da nasan kana nan nima a nan zan kwana jiya, i soo miss you yayanmu" Tana fadin haka ta kara rungumesa tana hawaye, Nihad dai sai bin su take da kallo kana ganinsu kasan su ne ainahin rich kids din, duk Mimi ta fi kama da shi, Noor ma fara ce Farhana da Hanan ne kadai haskensu bai kai nasu Mimi ba, Farhana sai kallon Nihad take keenly, can ta kalli Mami tace "Mami who is she?" Mami tace "Our visitor" Tambayarta ne ya ja hankalin sauran yan matan suka kallo inda Nihad ke zaune, Noor ta ɗan juya ido tace "Ohh She looks familiar" Hanan dai kallonta take babu ko kiftawa kamar me son gano wani abu, can ta ja Noor suka fita daga parlon tana zare ido tace "Kin tuna wata yarinya da video dinta ya tafi viral weeks ago?" Noor ta zaro ido bayan tayi recalling video din tace "Ohh yess!! exactly, wallahi suna kama sosai, i think baxan rasa video din a thrash bin dina ba" Tun da Khalil yaga sisters din nasa duk sun yi concentrating kan Nihad, yace "Ohk, ohk now, i need rest za mu hadu anjima a main parlor..." Mimi tace "Yayammu who is she, nima kamar na santa" Mami tayi dariya tace "A ina kika santa, banda karya Mimi" Mimi ta juya ta sake kallon Nihad da ta sunkuyar da kai gabanta na mugun faduwa don banda nude video dinta babu abinda ya fado ranta, mikewa Khalil yayi yace "Mimi za mu hadu anjima a main parlor, i said i need rest, ku fita" Sai ga Noor da Farhana sun shigo da gudu parlon, Hanan ta biyosu da sauri, Noor ta nufi Mami har tana tuntube tana mika mata wayarta tace "Mami u remember this???" Mami ta amshi wayar ganin video din da take nuna mata tace "Wai ba nace ki goge video din nan ba Noor? What is it still doing a wayarki?" Noor na zaro idanuwanta kamar za su fito tana nuna Nihad tace "Ba ita bace warcan" Mami ta kalli Nihad da sauri, sai kuma ta amshi wayar tana kallo, Kasa cewa komai Khalil yayi, Nihad da jikinta yayi sanyi kamar warce aka kwara ma ruwan sanyi ta kasa kwakkwaran motsi inda take zaune ta dinga bin su da kallo kamar warce tayi ma sarki karya, sai kuma ta sunkuyar da kanta with tears in her eyes, Mami ta kalli Khalil da sauri, sai kuma ta kara kallon Nihad, tuni Farhana ta tafi ta kirawo wasu set din yan mata biyu duk suka tsaya bakin kofa ko warce da wayarta a hannu, da ta kalli videon sai ta leko ta kalli Nihad baki bude, Mami da ita kanta jikinta yayi sanyi qlau ta kara kallon Khalil that is saying nothing, can ta hadiye wani abu tace "No, no may be resemblance ne kawai, ai akwai resemblance" Noor da Farhana suka wani gwalo ido har suna hada baki suka ce "Mami wallahi ita ce, the video is so clear fa ba wai yayi dishi dishi bane, ki duba mana ki ga, ita ce wllh" Da sauri Hanan ta tafi tana mika ma Mami waya wai don ta kara gani da kyau, Mami ta ki amsar wayar bata kuma sake cewa komai ba, Sajida tace "Ikon Allah, then who brought her to this house? Ance yar Maryam Abatcha American University ce fa" Mimi dake tsaye gefen Khalil ta kallesa a hankali tace "Yayanmu who is she?" Bai ce mata komai ba yana bin sisters din nasa da kallo ya nuna masu kofa yace "Ku fita" Farhana ta kyabe baki haka ma Hanan duk suka juya, Noor ma tayi ficewarta, Mimi ta dinga kallon Nihad dake ta hawaye, Ita ma ta fita daga parlon, Mami dai mutuwar zaune tayi a inda take. Daga karshe ta mike ta shiga dakinta ta zauna side din gado duk jikinta a sanyaye, a ina Khalil ya samo yarinyar nan har zai shigo da ita gidan nan? Bilkisu ta fito daga bandaki tana kallon Mami ganin yanayinta tace "Mami are you okay?" Mami tayi karfin halin cewa "Sure, ki tafi idan ina bukatarki zan kira ki Bilkisu" Tace "Toh Mami" Daga haka ta fita daga dakin, Har sannan Khalil na tsaye ya rasa abun yi, Nihad dai ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka, Bayan Bilkisu ta fita ya juya ya tafi dakin Maminsa, yana shigowa dakin ya kulle Mami ta mike tana kallonsa cike da tuhuma tace "Khalil wacece warcan yarinyar ka kawo mana gidan nan? Who is she? Menene alaqarku?" Yayi gathering courage yace "Mami calm down pls, yarinyar mai gidan da nace maki nakan zauna wajensa a kano ce, kuma ai na gaya maki dalilin da ya sa muka taho tare, Banda wannan babu wani dalilin Mami" Mami tace "Toh zan tura maka kudin jirgi ka siya mata ticket ta koma, ai ta gama abinda take ko?" Ya rasa