Sashe 108
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna fitowa parlor Nihad na kallon khalil cikin kuka tace "Don Allah ni ka barni in je in gaida Umma" Juyowa yayi yana kallonta yace "Akwai wata Umma bayan warce kike gaida da muka shigo daxu?" Muryarta na rawa tace "Toh kawai a parlor xan gaisheta?" Yace "Eh" Kuka kawai take tana kallonsa ta wuce sa kamar xata tashi sama ta nufi kofar fita parlon, bin bayanta yayi ya sameta jikin mota tana kuka kamar ranta xai fita, ya zaga driver seat ya bude ya shiga, bude bayan motar tayi ta shiga don ita har yanzu Drivern gidansu ne shi, Aminu ya marairaice bayan Khalil ya fito da mota waje yace "Ina ta rokon Saminu ya jira min gate in kawo maka ziyara amma ya ki..." Khalil na kallonsa yace "Wataran ma baxa kayi gadin ba gaba daya, sannan matsayinka xai dawo dai dai da na kowa a duniya" Aminu ya daga hannu biyu sama yace "Allah Ubangiji ya amsa bakinka, Allah ya dubemu yanda ya dubeka lkci daya, wannan gagarumin ci gaban da ka samu Allah ya sa mu a danshinka, wayyo wa yaga Aminu ya daina gadi, duk basur ya cinye ni sbda zama kan benchi daga safe har dare, na ma ji Alhaji yace xa a dubo sabon driver tunda kai yanxu ai ba batun tuki kuma" Murmushi kawai khalil yayi ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika masa yace "Ga wannan ka sha kankana" Aminu ya karba hannu bibbiyu yana cewa "Allah ya taimakeka oga" Wani shegen kallo Nihad ke ma daga Khalil din har Aminu tana jin kamar ta hadiye zuciya don takaici, nan ta kara jin wani sabon tsanar Khalil ya dirar mata, wato fafa yake yi sbda Abba ya aura masa ita, ji yake babu ya shi a duniya, Bayan sun bar layin tana kallonsa ta madubi tace "Kai yanzu kawai jin kanka kake saboda Abbana ya daukeni ya aura maka ko? Gani kake ka fi kowa sa'a a duniya tunda yanxu kudin da Abbana ke baka ya ninku linkin ba linkin har da su kyautar dubu daya, shkkn xaka dinga amfani da ni kana cin kudin Abbana" Khalil yayi wani murmushi bai tanka ta ba, ta murguda baki tace "Ai shi dama talaka bai iya samun waje ba, nasan yanxu alfahari kake yau gani matarka ko?" Yace "Ohk" Ta kara murguda baki bata kuma ce masa komai ba har suka isa gida, sauka tayi daga motar bayan ya bude gate tayi shigewarta ciki kamar xata tashi ciki, yayi wani murmushi kawai ya motar ya shigar da shi compound din. Bayan Nihad ta idar da magrib ta fito parlor ta samesa kwance saman dogon kujera yana waya, ganin bai lura da fitowarta ba duka a hankali ta rarrafa har bayan kujeran ta kasa kunne tana sauraron wayar da yake yi, A hankali taji yace "Nan da wata daya in sha Allah xan dawo, idan kuma na dawo baxan sake fita ba sai bayan aurenmu" Yana fadin haka babu sunan da ya fado ran Nihad sai Nadeeyah don har ta haddace sunan nata a xuciyarta, ta ɗan kyabe baki tana tsugunne bayan kujeran tana kara kasa kunne, Taji yace "Aa, akwai dalilin da ya sa na dade wannan karan Nadeeyah, ba wai da son raina bane, amma in sha Allah na kusa gama abinda nake yi, ni kaina na gaji da USA haka" Buda baki Nihad tayi hangangan jin sunan kasar da ya kira, Tunda aka haifeta bata ta6a ganin me lafta karya kamar wannan mutumin ba, wato USA?? Mutumin da ko ruwa ta kasa sha a garinsu balle ta ci abinci shine yake karyan yana USA, ya ma san full meaning din USA din kuwa?? Taji yayi dariya ya mike zaune yace "Wai da gaske??" Magana yake amma bin parlon kawai yake da idanuwansa don banda kamshin Nihad babu abinda yake ji a parlon, amma kuma bai ga alamarta ba, don haka ya koma ya kwanta a hankali yace "Ke ce farko kece karshe Nadeeyah, in sha Allah baxan hada ki da kowace mace ba, don kin min hallacin da baxan manta ba, in dai kuma ba baturiya kike son in auro mu dawo Naija tare in hada ku gida daya ku zauna ba, kinga ai nasan baxa kiyi kishiya da ita ba" bayan few seconds yayi murmushi yace "Ya na ji kin yi shiru?" Mikewa Nihad tayi tana tafe hannu tace "Ni wallahi ban ta6a ganin inda babba yake karya ba sai kai..." tuni Khalil ya katse wayar, ya mike tsaye yana kallonta, da mamaki Nihad tace "Kasan ma'anar USA kuwa? Kasan ina ne Usa? Me yasa baka tsoron yin karya a rayuwarka?" Yace "Kin karya daya daga sharadinmu don haka nima dole xan karya daya...." Yana gama fadin haka ya bar parlon ta marairaice ta bi sa da kallo har ya shige dakinsa, ta fi minti biyar tsaye parlon can dai ta bi bayansa, a hankali ta murda kofar dakinsa, tsaye ta gansa yana unbuttoning shirt dinsa, ta turo baki tace "Toh kayi hakuri" Ya juyo ya jefa mata wani kallo yace "Baxan yi" Ta marairaice tace "Don Allah mana" Bai sake kulata ba ya shige bandaki, ta ɗan kyabe baki, sai kuma ta dinga kallon wayar tasa dake gefen gado, tana tafiya a hankali kamar munafuka ta karasa gadon ta dau wayar, number Nadeeyah ta shiga tana kallon number tana ta6e baki, wai ba ma tayi blocking din number nan ba, wato unblocking yayi, tana dai ta kallon number, can ta ja tsaki kasa kasa ta kara blocking number tayi deleting ta ajiye wayar ta fita da sauri. Fitowa Nihad tayi dai dai sanda Khalil ma ya fito daga dakinsa, ta 6ata fuska tace "To ai cikin deal dinmu baka ce idan ana kwankwasa gate kai kadai ne xaka dinga xuwa budewa ba, nima xan iya fita in bude tunda ba kai kadai bane cikin gidan" Ba abinda yace mata ya nufi kofar parlor xai je bude gate din da ake ta bubbugawa kamar xa a cire, Nihad ta tafi jikin window dake parlon tana kallonsa har ya isa gate din, Yana tsaye bakin gate din yace "Waye?" A mugun fusace Umma tace "Uban me tambaya, nace uban me tambaya, halan gidan na ubanka ne idan ka ji an kwankwasa gate sai ka tambayi waye sannan ka bude?" Kawar Umma dake gefenta tace "Wai kaddai Dreban ne ke maki wannan tambayar?" Umma tace "Atoh ba matsiyaci bane? Kuma kin mance matsiyata basu iya samun waje ba?" Hajiya Turai tace "Aa ga alama" Umma tace "Ai kinsan gidan Ardo ko Nenne dake kauye ne shi yasa yake tambayar waye" Hajiya Turai ta kwashe da dariya tace "Sai dai haka kam" A mugun fusace Umma tace "Au, baxa ka bude min gate din ba??" Khalil yace "Me gyara yana hanya don tun jiya gate din ya samu matsala, mu ma bamu samu fita ba duk yau, don haka sai ku jira" Buda baki Umma da kawarta suka yi jin abinda yace, shi kam yana gama fadin haka ya juya ya bar bakin gate din ya koma ciki, Nihad na masa wani kallo tace "Waye a gate din da kaki budewa?" Yana kallonta da kyau yace "Warce kika yaudari kanki kika bai ma matsayin mahaifiyarki" Nihad ta zaro ido tace "Umma?? Shine kaki bude mata gate din?" Bata tsaya jin abinda xai ce ba a fusace ta taho xata fita daga parlon ta je ta bude ya fixgota, tana tsaye dab da shi yana kallonta da kyau yace "In har kina son mu rabu cikin salama ba tare da iyayenki sun yi fushi da ke ba ko an ga laifinki to kar ki tsallake umarnina ko daya, datse alqarki da warce kike kira da Umma yana daga cikin umarnina gare ki, bayan mun rabu xaki iya ci gaba da mu'amala da ita wannan ba matsalata bace, amma muddin muna tare babu ke babu ita" Nihad was shocked and lost of words at first, can dai tana girgiza tace "Amma kasan abinda kake cewa kuwa? Kasan warce kake cewa xaka datse alaqata da ita?? Kasan wacece Umma kuwa ko dai duk zamanka gidanmu baka san matsayinta ba? Matar Abbana ce fa? First wife din Abbana ce, She is my step mother, kuma duk duniya babu wanda ke sona baya ga ita, ban san dai ko Mumy da ta haifeni ba ba tunda ita bata ta6a nuna min son da take min a fili ba na Umma kawai na sani, Umma tun tasowata ban ta6a cewa ga abinda nake so a duniya an hanani a gidanmu ba, kome nake so shi nake samu, yanda Umma taga Abbana ke ji da ni haka ita ma tafi sa ji da ni, kuma bata ta6a hanani yin duk abinda nake so in yi ba tunda a ɓangarenta ma na taso, she is 100% in support of me always, ta daukeni kamar er da ta haifa a cikinta, dai dai da second daya bata ta6a banbanta ni da Nihal ba, don sai taki goyon bayan Nihal amma ni ta goyi bayana, ba kuma ta son bacin rai na ko na second daya, yanda na shaku da Umma ko Mahaifiyata ban shaku da ita haka ba wllh, don dama tun ina karama ta maidoni dakinta, ita ce komai na, amma shine yau xaka bude baki kace min xaka datse alakata da Umma?? Kana da hankali ma kuwa?" Kallon cikin ido kawai khalil ke mata, bai kuma ta6a jin tausayin rayuwarta ba sai a wannan lokacin, Ta fashe da kuka tace "In har a sharadin rabuwar mu har da datse alakata da Umma to kar mu rabu din, kai xaka wahala ba ni ba" Tana gama fadin haka ta kwace hannunta daga rikon da yayi mata ta shige dakinta, zaunawa khalil yayi saman kujera deep in his thought yana sake digesting duk abubuwan da Nihad ta gama fada masa..... Ana magrib Nihad taji fitar Khalil, tun da rana take kuka duk idanuwanta sun kumbura saboda ya hana Umma shigowa gidan, tana jin fitarsa ta fito bakin gate din sai taji ya sa makulli, ji tayi kamar ta kwanta wajen tayi ta birgima, ta dinga rera kuka kamar ranta xai fita a wajen. Khalil na zaune parlon Abba,