Sashe 161
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tadda Mimi na jiranta su yi Breakfast, bayan ta zauna shayi kawai ta iya sha sai irish kadan, ta na dai zaune idonta na kan tv abubuwan da Khalil ya gaya mata na ta dawo mata, tabe baki kawai tayi, aka bude kofar duk suka daga kai, Aunty Hassana ce ta shigo parlon, bata amsa gaisuwar Nihad ba tana kallon Mimi tace "Ke ina uwarki?" Mimi ta mike ta shiga dakin Mami, Aunty Hassana ta dinga hararan Nihad, a hankali Nihad ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon don haka kawai ta ji tana tsoron matar, Aunty Hassana ta bi ta da harara, tana ta tsaye har Mami ta fito, Mami na kallonta tace "Mun tashi lafiya Aunty Hassana" Aunty Hassana ta dakatar da ita tace "Ba wannan ya kawo ni ba, ina ce ai ko ba komai Hajiya Fatima yanda xa ki mutunta uwar mijinki da tana raye haka nima ya kamata ki girmamani ki mutunta ni don ni din ba banza bace, Da mijin nan naki da kike takama ya sha nono ni ya sakar ma, amma naga baki da warce kika raina sama da ni, yanzu ace wannan yarinyar da ta zo gidan nan tun jiya har ta kwana zuwa yau ya dace ace baki turata ta gaidani ta gaida Amina a gidan nan ba? Idan ita Amina bata isa ba nima din ban isa ba kenan? Kawai yarinya ta shigo gidan mutane tsabar ba a nuna mata matsayin wa enda ta samu a gidan ba sai ta wuce ka wuce bata gaida ka ba, ko daga kai baxata yi ta kalleka ba, to akan wani dalili?" Mami ta kalli Mimi tace "Mimi je ki kai ta ta gaishesu" a fusace Aunty Hassana tace "Aa bama bukata, taje ta gaida wa? kawai dai ina kara baki shawaran ki daina abinda kike, in raini kike ji a gidan nan to karki matso da shi inda nake, don ni ba abokiyar yin ki bace Fatima" tana kai wa nan ta fice daga dakin kamar iska, Mimi ta kalli Mami tace "Why is she always creating issues out of nothing? From this to that, is she normal?" Mami tace "Jeki ki kaita nace ta gaishesu ban iya wahala da safen nan Mimi, da nasan abinda ya kawota kenan ma ni cewa xanyi kice mata ina bacci" Mami na kai wa nan ta juya ta koma dakinta. Khalil na zaune parlon Abbansa, ya jira har ya gama wayar da yake na kusan minti goma, Abba na kallonsa bayan ya gama a takaice yace "May i help you?" Khalil ya gyara zama yace "My Curriculum vitae, the key to my houses and their written document, my land title, my car.... Ina bukatarsu gaba daya, and I also want my business account unfrozen" Kallonsa kawai Abba yake, can ya mike yana kallonsa da kyau yace "Till u pay ur debt of 800m, idan ba haka ba duk assets din nan da ka lissafo ina me tabbatar maka siyar da su zan yi, kuma basu kai biyan bashin ba ma, shi kuma Cv din in kona, after all i sponsored you...." Khalil ya dinga kallon mahaifin nasa, Abba yace "So Now get out before i shoot ur leg" mikewa Khalil yayi ya nufi kofa kamar xai tashi sama ya bude, sai kuma ya juyo yace "But dad, I can't pay for what I know nothing about...." Yana fadin haka ya fice daga parlon, direct bangaren Mami ya tafi, Mami na ganinsa ta mike tace "Lafiya" Yana huci yace "Mami me yasa har yanzu Abba ke danganta 800m dinsa da ni?? Ina zan kai har 800m" A hankali Mami tace "Saboda kai ya ba, a hannunka yasan kudinsa" A fusace Khalil yace "Toh ni ban san komai kan kudin nan ba, why is he not believing me?" Mami tace "Yanzu me ya kawo maganar kudin?" Yace "Naje na samesa xan amshi abubuwa na da ya amshe min" Mami tace "Amma ai na hanaka ko? What are you lacking now without them?" Khalil na girgiza kai yace "Baxan iya ci gaba da zama bana aiki ba Mami, ya sa anyi sacking dina a inda nake aiki, to ya bani Cv dina in nemi aikin a wani waje mana?" Mami tace "Idan da ka saurareni da baka je masa da maganar wani Cv ba Khalil, me kake bukata da baka samu a yanzu haka? Baka fi wani me aikin samu ba duk da haka? Every month ina tura maka 300k banda wanda kannena ke baka, so me xaka yi da Cv yanzu" a fusace Khalil yace "Ni neman auren Nadeeyar ma bana son yaje min, xan samu kawu kawai su je" yana fadin haka ya nufi kofa a fusace, Mami ta buda baki, sai kuma tace "Toh ai mun yi magana da shi jiya yace next week xai tura representative nasa su je neman auren, kar ka fara xuwa wajen kowa idan ba ɓacin ransa kake son gani ba" Tuni khalil ya fice daga parlon. Hajiya Amina ta shigo bangaren Aunty Hassana tace "Aunty Hassana kin ji abinda Oga yake ce min daxu kuwa?" Aunty Hassana tace "Me yace?" Hajiya Amina tace "Wai satin da xa a shiga xai tura a nema ma Khalil auren yarinyar nan dai, ita fatimar ta masa maganan hakan..." Aunty Hassana ta gwalo ido tace "Da gaske?" Hajiya Amina tace "Wallahi, kafin ya fita yake sanar min" Aunty Hassana tace "Ai ko bai gaya min ba kuma na shiga gaishesa daxu" Hajiya Amina tace "Toh dai shine nace bari in zo in sameki" Aunty Hassana tace "Toh bari inyi wanka zan fito yanzu" Hajiya Amina tace "Toh sai kin fito" Daga haka ta juya ta fita, Aunty Hassana ta mike da sauri ta dau wayarta ta shiga daki tayi dialing number aminiyarta, tana dagawa tace "Ke kuma haka ake Chamo daga cewa kina zuwa sai in ji shiru" Daga daya bangaren aminiyar tata ta kece da dariya tace "Ke dai bari na shiga rububi ne, ai da ma sai dai ki gan ni yau to kuma sai tafiya Kaduna ya kamani, ya gida ya su Sajida" Aunty Hassana tace "Lafiya lau, ni baki gaya min yanda ku yi da mutumin nan kan maganar da muka yi dake ranan ba har yanzu" Chamo tace "Wallahi yace daga dubu dari tara da hamsin ko biyar baxai sake ragewa ba, kuma ke ma dai kin shaida aikinsa, ba fa kowa yake ma aiki ba don shi aiki ma yawa yake masa" Aunty Hassana tace "Shikenan, don wallahi yanzu Amina ta shigo take gaya min satin da xa a shiga ma xa aje neman auren yarinyar" Chamo tayi wani dariya irin ta bosawa tace "Wuyarta ba a tura masa kudi an fara aiki ba, ke dai turo kudi kawai aminiya" Aunty Hassana tace "Toh Sadiya, yanzu kuwa zan saka maki, so nake da kansa zai birkice masu yace ya fasa bai sonta, kuma dab da xa a kai kudin" Chamo tace "An gama, sako kudi yanzu" Aunty Hassana ta katse wayar ta tura mata kudin.