Sashe 65
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ana saura kwana hudu su Aliyu xa su kawo kudi, Nihad na bacci da rana Kasancewar ranan asabar ce babu lectures wayarta ya fara vibrate, bude ido tayi don Aliyu yace xai kirata tana jawo wayar taga wata Coursemate dinta Sajida da ba wani shiri suke ba ce ke kiranta, da kamar baxata daga ba sai kuma ta daga ta kai kunne, Sajidah tace "Nihad what is this i am seeing on social media?" Nihad ta bude ido tace "Kamar me?" Sajidah tace "Hau WhatsApp" Daga haka ta katse wayar, sai ga kiran wata secondary school mate dinta Hafsah, tana ta kallon kiran sai kuma ta daga, daga daya bangaren Hafsah tace "Nihad what's happening?" Nihad ta mike xaune tace "Ban gane ba?" Hafsah tace "Ki hau WhatsApp" Nihad na kokarin shiga WhatsApp sai ga kiran wata warce suka yi islamiyya tare, kawai haka nan taji gabanta ya fadi, ta dai daga kiran, Badiyya tace "Nihad garin yaya haka don girman Allah??" Hankali tashe Nihad tace "Wai me ke faruwa?" Badiyya tace "Ki kunna data" Nan Nihad taji jikinta ya fara rawa, wani kiran ne ya shigo taki dagawa tayi rejecting ta bude data ta hau WhatsApp din da sauri, messages ta gani rututu na shigo mata, kawai ta bude wanda hannunta ya kai, Wata school mate dinta ce ta turo mata video tana tambayar "what is this Nihad??" Hannun Nihad na rawa ta bude video din, kanta ta gani with just skimpy undies a saman gado ba kuma bacci take ba, sai kuma taga ta mike tsaye turning all over jefar da wayar tayi jikinta na rawa tana zaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai kuma ta saki wani kara ta sauka daga kan gadon ta durkusa kasa, ringing kawai wayarta ke yi amma ta kasa motsawa daga inda take, bude kofar dakinta aka yi ta daga kai da sauri, Umma ta shigo tana zaro ido tace "Nihad me ke faruwa a social media yanxu Nihal ta kirani tana kuka, kuma wai ta kiraki bakya dagawa" Nihad ta kasa cewa komai, bata ta6a zama soo weak all her life ba kamar wannan moment din, ji take kamar komai na jikinta ma ya daina aiki, wayar Umma ne ya fara ring ta daga da sauri, Nihal na shessheka tace "Umma ki hau WhatsApp na tura maki" Umma tace "Tohh" Da sauri Umma ta hau WhatsApp ta shiga chat dinta da Nihal ta bude video din, salati ta saki bayan ta gama kallon video din har karshe ta jefar da wayarta kan gado tace "Nihaddd????" Dai dai da second daya wayar Nihad bai samu breathing space ba, kiran su Husnah ne, Naf, Zully, infact calls upon calls kawai amma ta kasa kwakkwaran motsi inda take a durkushe balle ta daga wani waya, sai rufe ido take tana budewa kamar dai warce ke mafarki tana son ta farka, Umma na tafe hannu ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace ni Sumayya, Nihad wa ya maki haka? Garin yaya haka Nihad?" Bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo da tashin hankali kwance fuskarta, Umma ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah mun gode maka ni Sumayya, me xa mu gani haka Nihad" muryan Mumy na rawa tace "Nihad??" Kawai sai ga hawaye na xuba idonta tana girgiza kai, Wannan ne yasa Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace" Kwalban turare da Mumy ta gani gaban mirror din dakin ta figa tayi kanta amma tuni Nihad ta shige bandaki ta sa makulli, Umma kuma ta rirrike Mumy tana kuka tace "Aa Maryam ki kai zuciyarki nesa kiyi ta furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un, nima shi nake yi" A haka ta ja mumy dake kukan bakin ciki da takaici suka fita daga dakin.
kafin dare kai ka ce mutuwa aka yi a gidan, gaba daya iyalan gidan Alhaji Abubakar sun iso gidan Abba, makusantan Mumy duk sun xo gidan, Umma ma yan uwanta da kawayenta duk suna gidan, Aminu sai bin duk wanda ya shigo yake da kallo cike da mamaki don ba ace masu kowa ya mutu a cikin gidan ba gashi khalil da yake ma gulma baya nan tun rana ya fita, kowa kuma ya shigo babu walwala yake nufar entrance din parlor, all the way from Abuja haka Farooq ya biyo flight ya dawo, Usman ma daga kaduna haka ya taho... Tun faruwan abun nan Umma ke kuka non stop, handkici hudu duk sun yi jagab a hannunta, Mumy kuwa in ka ganta sai ka tausaya mata she is so heartbroken, banda kanninta mata biyu da Yaya farooq da suka jibgi Nihad son ransu babu wanda yayi attempting ta6a ta ko ce mata komai a gidan...... Tashin hankalin Nihad bai linku ba sai da taga alamar Aliyu yayi blocking dinta ta ko ina, WhatsApp, IG, Phone call, Twitter, infact all, kawai sai take fatan Allah ya dau ranta ta huta kawai, gashi har lkcn ta rasa a ina aka mata wannan video din idonta biyu ba bacci take ba.....
*Ci gaban labari*
A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take yashe da kallo, tsakiyar parlor ne kuma a kasan Carpet, gashi babu kowa parlon, everywhere looks strange to her, da sauri ta mike xaune as if trying to recall something, dai dai nan aka bude kofar wani daki ta juya suka yi ido hudu da shi, sai da numfashinta ya dauke na few seconds da kyar ta jawo numfashin, lkci daya komai ya dawo mata ta kurma wani uban ihu jikinta na rawa tana kallonsa, sai kuma ta mike a guje tayi hanyar kitchen kamar mahaukaciya....
Nan na kawo karshen free pages, sai mu hadu a payment group.
Domin samun ci gaban littafin *Nihaad* it is only 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah