← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 165

Sashe 61

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sai ka zo kai ta makaranta ba" Khalil yace "Ok" Juyawa yayi ya tafi ya cire akwatin karshe ya kulle booth din, khalil ya ja motar yayi zoom off, Nihad ta bi sa da harara tace "Uwa motar ubansa, wllh ni ce sanadin aikinka a gidan nan mu dai je zuwa, sai kayi da ka sanin sanina a rayuwarka" Shi da mai gadin kallonta yake yana kokarin kai akwatunan cikin gidan, ko karamin bata dauka ba haka ta bar masa su dukka ta wuce ciki, Kamila dake parlor tace "Mutanen Maryam Abatcha American University" Murmushi Nihad tayi tace "Aunty ina kwana?" kamila tace "Lafiya lau, amma fa ki kira warce xata xo ta dau kayan naki xuwa hostel don karfe sha biyu xan fita nima" Nihad tace "Ehh tace min karfe sha daya xata zo" Kamila tace "Toh ya dai fi, daxu ma Mumy ta kirani wai in sa maki ido nace toh" Nihad tayi dariya tace "Aunty kamila mumy sai tayi ta treating dina kamar wata er yarinya" Kamila tace "Gaskiya kam, ga ki ke ba yarinya ba, makarantar ki ma ba ta yara ba" Dariya kawai Nihad take, Kamila tace "Atoh dai" Karfe sha daya Naf da Husnah suka iso kofar gidan Kamila na tsaye compound duk suka saka akwatunan a motar Naf, Bayan sun gama tace "Toh Allah ya tsare" Nihad tace "Ameen Aunty" su Naf suka mata sallama, tana kallonsu har suka bar compound din ta juya tayi komawarta ciki, murna a cikin Nihad ba a cewa komai, a haka ta koma rayuwarta a hostel babu me sa ta babu me hanata, duk sanda Mumy ta kirata sai ta shige bandaki ta kulle su yi waya don kar ma taji hayaniyar su Naf da Husnah, night party kuwa sai wanda suka mance ne baxa su ba, duk yanda suka so rinjayar Nihad ta dinga shan kwayoyin da suke sha bata ta6a sha ko da wasa ba, sau daya Husnah ta shammace ta ta xuba mata a lemo shi ma sai da ta kwana ta yini tana baccin wahala, hakan ya sa suka rabu da ita da batun drugs, sai kuma suka fara jan ra'ayinta zuwa kwanan hotels da suke da boyfriend dinsu, nan ma dai ta ki, ko min daren da suka yi a waje ita dai sai ta dawo hostel, duk sanda suka yi waya da Umma sai ta ja mata kunne kan cewar kar fa ta dinga bin duk wani wuri da xata iya haduwa da Abbanta ko Farooq, ita kanta Nihad is so careful about that, a haka har suka fara exams, duk cikinsu Nihad ce ke maida hankalin karatu, sauran ko bude takarda, duk sanda Mumy ta bukaci Nihad ta zo gida sai tayi karyan karatun exams yayi mata yawa, bayan an gama exams din ma don kar Mumy tace Nihad ta zo gida Umma ta sa kamila ta kirata tace xa su garin mijinta, haka nan aka kare hutu Nihad na hostel abun ta suna baza life, su ne har Kaduna da hutun, sau biyu ta je gidan Kamila shi ma ɗon Aliyu ya shigo kasar ne xa su hadu sai taje gidan kamila shi ma ta ce masa mijinta ne yayi tafiya take taya ta zama......
Chapter 61 · 0% Book details